Thursday, 18 January 2018

Gidan Mati 6

*GIDAN MATI*

© BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR

KASHI NA SHIDA

Inna ta hau tafa hannuwa tana salati iyakar k'arfinta, kan ka ce me magulmatan makwaftansu sun hau lek'e cike da al'ajabi.
   "Yau na ga abinda ya fi karfina ni Uwar biyu! Kai! Kai! Wallahi ba za ta sa6u ba, Mati!"
  Ta juya ga Mati wanda zufa ke ta karyomasa, gabadaya ya susuce, daman ita Abule ya san k'arya ce ta shukamasa musamman da ya ji tana maidawa Delu irin tuggun da ta shirya na iska, ita kuwa Nene bai ta6a kawowa k'arya ta ke ba, a zatonsa idan Abule ta ɓata rawarta da tsalle to yana da mafaka a wajen Nene. Sai dai ashe dukkansu taron na ayya ne.
  "Eh dole ka rasa bakin magana mana! To wallahi ba za ta sa6u ba! Ko ka k'ara aure ko kuma ka saki kowace shegiya ta koma akurkin ubanta. Za6i ya rage naka, yanzu na ke son amsata."
Inna ta k'arashe tana gyara zaman siket dinta na buje. Nene da Abule suka shiga tashin hankali, kada fa su yi biyu babu.
  "Kai nake sauraro ka tsayamin k'erere kamar liman ya manta Fatiha."
  Mati ya saci kallon Matansa, to da ya rasa tafkekiyar gonar Inna da kuma gida ai ya gwammace ya k'ara auren ya samu haihuwa.
  Ya mai da idanunsa kan Innarsa.
"Shikenan, ki nemo min mata."
Ai sai Inna ta rangad'a gud'a.
"Ayyiriririii! Haba ko kaifa, yanzu na tabbatar da cewa kai jini na ne. Sai ka shirya don kuwa yanzu za ka yi aure."
"To amma..."
"Amma me? Inna ta katseshi tana harararsa.
"A'a wai dama gani na yi su biyun ma mangalar jakai na biyu bata iya rikesu da ita, shi ne nake tunanin kar ta ukun ta shigo kuma idan ina cin abinci sau biyar a rana na dawo sau uku."
"To batunu ƙiyama sarkin ci, in ce dai gidan nan nawa ne?"
"Naki ne har ni d'inma." Ya faɗa yana dukar da kai.
"To tunda ni zan ma auren mene na tunani? Idan ta ciyarwa kake zan ƙarama akuya da rago ka kiwa ta. Ina ce dai shi ke nan?" Ta waigo ɓarin da su Abule ke tsaye.
"Ku kuma sai ku shirya don kuwa falleliyar budurwa zan samar masa, ba irinku zawarcin titi ba."
Bak'in ciki ya turnuk'e Nene da Abule. Musamman Nene da ta tabbatar bata kai na ta matancin ba, amman dai ai ita ce ta fari, kuma  ma ta toshe yanda ba za a gane ba, don haka ta karkata baki.
"Allah na tuba ko dubu zai auro ba kamar ni a zuciyarsa, ni ce dai Nenen Mati, kaf k'auyennan an shai da soyayyarmu."
Inna ta bankamata harara kawai ta wuce d'aki. Shi ma Mati da saurinsa ya fita ya hau jakinsa ya fice. Abule ce ta saki shewa.
  "Aikin banza wai bille a d'uwawu, duk dai abinki bai sanya an fasa auroni ba, dad'in abin ma ba abinda bansani ba. Ina ce da sa hannun aljanu da 'yan bori a aurenki da shi ko?"
  Nene ta fusata, za ta kai mata bugu tuni Abule ta nufi d'aki, ta mai da dubanta ga masu lek'e.
  "An yi asara munafukai da tsakar rana babu ko kunya!"
  Babu wacce ta tankamata acikinsu, ta gama haukanta ta fad'a d'akinta.
      
BAYAN WATA BIYU

Ta faru ta k'are, duk wani shiri da gyare-gyaren da ya dace a yi na zuwan Amaryar Mati an kammala, amaryar ba wata bace illah Faɗime d'iya ga aminiyar Inna, Ladidi. Daidai da lefe Inna ce ta koma birni tare da Ladidi suka haɗo. Abu kamar wasa dai aka sanya biki sati biyu, duk irin borin Nene da Abule bai sa an fasa ba, ganin babu Sarki sai Allah ya sanya suka hak'ura.
  An kawo Amarya lafiya lau da gud'a da komai, cikin 'yan rakiyarta har da Shafa da Delu.
  Kwanan Amarya d'aya a gidan Inna ta tattara ta koma birni da zummar sai nan da sati biyu za ta k'ara lek'owa.
       Nene na zaune ta tsefe kitsonta wanda ya kusa shekara yayin da Abule ke kwance saman tabarmar kaba tana jifanta da wak'e-wak'en habaici tana ramawa suka tsinci muryar Mati da Amaryarsa suna shek'a uwar dariya, suka dubi juna da sauri kamar wadanda aka mintsila suka nufi k'ofar d'akin nata har suna bangaje juna, ƙarshe dai suka nutsu suna lek'esu.
  Amarya Faɗi  ke kwance saman cinyar Mati, shi kuma yana yagar tsire yana sa mata a baki suna hirarsu cike da nishad'i. Nene ta dafe kirjinta gami da had'iyar yawu. Ba ta jira komai ba ta yi wuf ta shige ganin haka Abule ta ja baya tana mai rike ƙugu.
  "Kan uban can! Wato  Mati dama amanarmu ku ke ci? To wallahi ba za ta sa6u ba! Sai dai ayi raba daidai!"
Za ta d'auke ledar naman Faɗime ta cafke hannunta ta mik'e tsaye.
  Baki Nene ta saki ganin shigarta.
  "Riga da wando a gidan nan? Jakar Uba! Mati karuwar birni Innar ta auromaka ashe banda labari?"
Harara Mati ya sakarmata bai ce komai ba don wani sa'in yana shakkarta. Faɗi ta kauda fuska gami da murgud'a bakinta da ya sha jan baki.
"Ke Malama don Allah ki bar nan wallahi warinki na tayarmin da zuciya. Ga dukkan alamu dai ko wankan tsarki ba kya yi."
Ta saki hannunta.
"Kuma wallahi ki ka k'ara ta6a ledar nan sai na  miki ihun mahaukaciya. Ce miki akai Ni haɗamammiya ce irinki? Ga naku kason can a gefe dan bazan yarda Miji na ya tashi da shanyayyen ɓarin jiki ba ranar gobe ƙiyama."
  Nene ta hau tafa hannu da shewa.
"Hehehe!  Yau nake ganin bariki a gidan nan, ashe kuwa yau wata za ta bi tsohon najadu barzahu. Idan kin fasa kirana mahaukaciya ba ki cika d'iyar Ladidi mai siyar da kayan maye ba!"
  Fad'in haka keda wuya, ta kai hannu za ta d'auki ledar,  Faɗime ta damk'i gashinta ta mai da ta baya, tayi taga-taga za ta fadi k'afar Mati dake ƙasa ya miƙe ta kwashe ta sai gata Tim! A ƙasa tayi zaman 'yan bori.
     Faɗi ta juya da Mini-minin idanuwanta ta dubi Mati "Sannu Maigida bata dai jima ciwo ba ko?"
Mati ya washe baki ya ce "Faɗi Amarya ina gabanki ai bana jin ciwo."
Ta yi masa far! Da ido ta ce, "Mai gidana na sha ce maka Timah zaka dinga kirana yarda kawuna na birni ke faɗi.
Taɓɗijam! "Yau na ga sabon salo wai tafiya bariki da Uwa" Cewar Abule daga bakin ƙofa.

        Amarya ta waigo ga Nene dake baje ƙasa tana cije baki, "Ke kuma ki ci gaba da shiga shirgi na, wallahi da ruwan sanyi zan dafaki dan ban iya dambe tsakar gida ba, balle na haifawar maigidana talauci, ku da kuka saba kuje can ku ƙarata, ga tsiyarku nan." Ta faɗa tana tura musu kasonsu na tsire.



Muna zuwa.

MUN GA YABONKI YAKE GARKUWAR MUNANA, MUNA GODIYA.

No comments:

Post a Comment