KASHE FITILA💡2
Batul Mamman💖
Fika LG-Yobe State
Yara ne suke ta tsalle-tsalle a tsakar gida saboda yau alhamis babu makarantar Islamiyya. Masu dan girman kuma musamman matan kowacce ta kama aikin gida tana yi.
Sallamar da suka ji ce tasa suka tashi babu babba babu yaro suka tafi tarbo mai yinta. Murnar ganin Kawunsu suke yi sai dai ganinsa rike da Rumana tana tangadin karya yasa suka yi cirko cirko. Sarkin surutun gidan ne ya ruga ciki yana sanarwa ga Rumana ta dawo.
Mahaifiyarta wadda ta kasance mata ta biyu cikin matan gidan bata san lokacin da ta janyo hijabi ta fito ba. Addu'a take yi Allah Yasa ba wani abin Rumanan tayi ba Kawunta ya kasa zama da ita.
Ko da ta fito sauran matan gidan wato uwargidan da amaryar duk sun fito suna musu maraba. Ganin yanayin Rumana yasa suka san babu lafiya. Maman Antu kamar yadda ake kiran uwargidan ita tayi saurin riko hannunta suka shiga babban dakin da yake mazaunin falo a gidan. Tuni Awaisu ya wadata musu shi da kayan kallo da kujeru masu kyau.
Bai bi bayansu ba ya wuce dakin Baaba Hure. A zaune ya sameta tana jiran shigowarsa tun bayan taji an ambaci sunansa da na Rumana. Sai da ya gaisheta cikin yarensu na Bolewan Fika sannan yayi mata bayanin dalilin zuwansu.
"Kuma ka tabbata ba aljanu bane da ita?"
"Ko daya Baaba, jiyan nan dai ta bani tsoro shiyasa nace bari na kawota ta huta kwana biyu. Makarantar tasu zanje sati mai zuwa duk da sun san bata da lafiya na sanar musu halin da ake ciki"
"To Allah Ya sauwake, ina 'yar uwata? Kwana biyu ko a waya idan nace yayanka ya kira ba ma samunta"
Dan murmushi yayi "tana nan lafiya, kinsan sai ta ajiye wayar ta manta inda take ma. Alhaji bai dawo bane?"
Kafin ta bashi amsa suka jiyo muryar Alhaji Harisu yayansa. Dakin ya karaso suka gaisa inda ya sake labarta musu dalilin zuwansu. Wannan karon harda matan gidan da Rumana a wurin.
"Zancen banza" cewar Alh Harisu
"Shine zaka biye mata ka baro aikinka ku taho"
Rumana ta tsuke baki, fatanta kada Alhaji ya bata shirin da suka kwashe sati uku suna yi ita da Yusra yace ta koma wannan kurkukun. Ita yanzu ko sunan Abuja ma bata son sake ji.
Shi dai Awaisu lallabata yace ayi kuma a tambayeta dalilin kin cin abinci. Domin ko mutan gidan suna ganinta sunyi korafin ramarta. Yarinyar da ko da tana makarantar kwana kafin komawarta Abuja da kibarta. Ita ko ramar nan ta kewar gida bata yi.
*****
Washegari da sassafe Awaisu da drebansa suka kama hanya.
Sai da Rumana taji tashin motarsu tayi wata kyakkyawar ajiyar zuciya. Za taci karenta babu babbaka, ta mike kafa taji dadin rayuwarta. Abinci kuwa tun daren jiya take yi masa cin hauka.
Bayan kwana biyu da dawowarta suna daki ita da babbar yayarsu da tazo daga gidanta. Hira suke yi Rumana tana bata labarin horon da akeyi musu a gidan Kawun nasu. Karshe ma tashi tayi tana kwatanta irin abin da tayi a clinic din makaranta. Mahaifinsu ne yazo ya tsaya yana sauraren bayaninta batare da ta sani ba. Ita kuma Maryama yayarta da ta ganshi ta kasa cewa tayi shiru sai kai da ta sunkuyar. Tana cikin nuna mata sandarewar da tayi a mota ta kula da Alhajin. Nan jiki ya fara rawa, kanta yayi yana duka ko ta ina.
"Har kinyi wayon yiwa dan uwana sharri Rumana?"
Ihu take yi tana kuka "Wallahi Baba ba karya nake ba. Ba'a bamu abinci sosai a gidan. Daga ni har Maamu bama koshi"
"Rufe min baki sakarai mara godiyar Allah. Sharrin naki harda Maamu a ciki? To zan kira Awaisun da kaina muyi magana"
A fusace ya fita ya shige dakinsa. Ko zama baiyi ba aka sanar dashi Baaba tana kiransa. Ya tashi ya fita.
"Ina gidan nan kake hukunci irin haka ko? duk kiran da nayi maka kuma baisa ka dena ba"
"Kiyi hakuri Baaba wallahi banji ba"
Abubuwan da Rumana ta fada ya maimaita mata. Gyada kai ta rinka yi har ya gama.
"Babu abin da ya dace kayi da ta fadi maganar nan sai bincike ba duka ba."
Cike da mamakin rashin gaskata zancenta yace "bincike kuma Baaba? Awaisu fa ake magana"
"Na sani, fada maka ne kawai banyi ba amma dan zaman da nayi kwanakin baya banji dadi ba. Kuma kasan Maamu da zurfin ciki"
Kallon mahaifiyarsa yayi yana mamakin maganganunta.
Fita yayi yasa aka kira masa Rumana. Ya tsareta da jan ido yace ta fada masa komai tsakani da Allah. Kamar an kunna rediyo haka ta rinka bashi labari kuwa. Tana yi tana kuka, shi kansa Alh Harisu idanunsa kamar gauta don bakinciki da bacin rai. Sallamarta yayi da gargadin kada kowa yaji maganar nan sai ya gama bincike.
Wayar kaninsa ya kira suka gaisa tare da taba barkwanci sannan yace ya hada shi da Maamu. Anyi sa'a yana gida da kansa ya kai mata wayar.
A zaune take sanyin AC yana neman illata ta amma ta kasa kashewa saboda karamin dansa Safwan ya kwashe batiran remote din ya saka a game dinsa. Da ya shiga hankalinsa bai kai kan rawar darin da takeyi ba balle ya taimaka mata. Wayar kawai ya mika mata.
Tana karawa taji muryar Harisu sai kwalla wadda tayi saurin mayarwa. Rabon da suyi magana wane wata biyu. Gaisheta yayi ta amsa muryarta tana rawa. Hakan da yaji kawai ya fahimci tana cikin matsala. Bai zurfafa tambayoyi ba yaje ya sanar da Baaba gobe zaije Abuja taho da Maamu.
Ganin ransa a bace sosai yasa ta dakatar dashi yana kokarin fita "kada ka manta Awaisu danta ne na cikinta, bata nemi taimako ba kada kayi shisshigi. Garin neman kyautata mata ka shiga hurumin da baza'ayi maraba da kai ba"
Cak ya tsaya yana auna maganar Baaba Hure.
"Yanzu sai kawai mu zuba ido idan har gaske ne tana cikin matsala a gidan?"
"Ba ido kawai zamu zuba ba kuma bazamu yi gaggawa ba. Komai na duniya a sannu ake binsa har a gano bakin zaren. Misali yanzu Rumana karya tayi mana, da wane ido zaka kalli kaninka ko Maamu idan suka ji?"
Labarin Maamu
No comments:
Post a Comment