Thursday, 18 January 2018

Gidan Mati 9

GIDAN MATI
 
BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR

KASHI NA TARA

"Ke dadina dake jahilci kwarankwatsa dubu, haba ai ko karamin yaro ya san ruwa za a shekama Zubo a zuba Sugar shi ke nan ya zama lemo, batun lalle kuma kin manta Inna da shegen san fadanci kamar matar Bawan Sarki? Ai kawai kururuta mata kai zakiyi har ta sake ta baki kafar ki kunsa. " Nene ta yi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta gintse fuska ganin Fad'ime ta fito zuwa makewayi. "Shegiya kai da wata fuskarta kamar taunanniyar gyada, Allah Abule yadda naki jinin Matar nan bank'i a cemin karta fito raye daga makewayin nan, ba ni zoban ki gani duka gidan zan had'a idan ya so a na tan sai na juye maganin" Ta fad'a tana wartar ledar zobon da Abule ta riga ta siyo. "A'A hankali dai Nene d'an kad'an ya ce a zuba saboda karfinsa." Ta balla mata harara "Wallahi duka zan juye idan za a sha giya asha ta dubu Abule!" Ta fad'a tana mai ficewa daga d'akin. Kai tsaye madafi tayi ta dauko kwanon sha ta juye zobon, ta tuttulo ruwa daga tulu ta sheka bisansa ta zuba Sukari wadatacce ta juya. Nan da nan ta kasafta na kowa, na Inna ta fara dauka dauka za ta kai mata, da shigarta kuwa ta tarar ta tana gyangyadi dan haka ta aje ta juya za ta fita. " Na shige su ni Uwar Biyu, Nene me nake gani haka?" ta juyo da sauri tana kallonta kafin kuma ta saki murmushi. "Zobo ne muka samu tsaraba daga Abule, shi ne na hadamana lemo da shi na san ai kin sanshi a birni." Inna ta balla mata harara tana turo kallabi goshi." To ke ina kika taba ganin anyi zobo ba a tace tikar ba? Wannan zobo za mu sha ko roman zobo? Idan ba ku iya abu ba ku dinga tambayata mana, ni nan da kuke gani na bayan zobo durinkis (DRINKS)har mangwar durinkis (MANGO DRINKS) Na iya, dan haka ban san jahilci d'auki ki ta ce shi sai ki kawon. Sum-sum Nene ta fice jin Inna ta koma yaren 'yan sama jannati. Sake gyarawa ta yi, tukun ta dauki na Fadime ta kai mata daki, komawarta daki ke da wuya Mati ya sawo kai Gidan. Kai tsaye dakin Fadi ya yi yana doka sallama, fasa kai dan karamin kwanon shan baki ta yi ta aje tana amsa masa    da murmushi kafin kuma ta mike tana kokarin zare masa zungureriyar hular da ke kansa. Ya shaki kamshinta da yake so na Karkar dan haka ya washe baki "ALLAH Amarya son ki nake kamar na mutu" Ta yi murmushi tana rangwada kwalelen kanta "A'A Maigidana mai ya kawo mutuwa kuma, muna tare ai." "Hmm! Ba za ki gane ba ne, idan kina kusa da ni ji nake kamar numfashi... KYYYATTT...FYYTTATAT... Ya dakata yana mai kakalo kaki, kafin kuma ya dunkulo majinar yana mai furzo ta waje da ba ta dire ko'ina ba sai cikin kwananshan Fadime dake cike da zobo. Ita da shi suka zubawa kwanon ido kafin kuma ta kwabe fuska. "Haba Maigida na sha ce maka ka dainamin tofe-tofe a bangon daki ko kasa, wannan ko a kan titi ne ba abin so ba ne. Yanzu kalli yadda ka haramtamin abinda tunda na gani yawuna ke tsinkewa. " Ki hakuri na mantane, yanzu bari na karbo miki kasona sai ki sha." ya fada yana mai daukan kwanon ya fice. Bisa randa ya tadda wani kwanon rufe da Fai-Fai Dan haka ya aje wancan ya dau wannan ya tafi. Nene da ta shiga makewayi rage ciki tana fitowa tayo inda ta ajje zobanta, ganinsa bude ya sata doka ashar "Ko wane shegen ya budemin oho, to idanma diba akai an sha wuta bal-bal tunda nawa ne. Ta fada tana hararar dakin Inna, kafin kuma ta daga kwanon ta kwankwade tas! Har kakin Mati. Minti biyar da sha cikinta ya yi wani irin juyi, jin kamar ruwa da wani wari na binta ya sata lekawa abin da ta gani na binta ratata ya sata doka ihu tana dafe mazaunanta "Wayyo ni Mati! Yoyon Kashi ya kamani.

Muna zuwa.

No comments:

Post a Comment