Monday, 22 January 2018

Kashe Fitila 4

*KASHE FITILA*💡4

*Batul Mamman*💖


Ranar laraba da yamma Harisu da kaninsa suka isa Abuja. Da tambaya suka karasa gidan Alh Mudi Maibuta, dan kwangilan da Saminu ya nemi taimakonsa akan neman aikin Awaisu.

Gida ne babba irin na mutanen da naira ta zauna musu. Daga bakin gate din maigadi ya tambayi sunansu da abin da ya kawosu. Suna fada ya saki fuska tare da sanar dasu Alhaji ya bayar da umarnin yi musu iso da zarar sun karaso.

Wurin wata katuwar bishiya ya rakasu inda Alhajin yake zaune yana shan iska. Gefensa 'yan mata ne guda biyu sanye da kaya iri daya.

Tun tahowarsu Awaisu wurin babbar ciki ta kafe shi da ido tana murmushi. Shi kuwa hankalinsa bai ma kai gareta ba. Cike da girmamawa suka gaishe da Alh Mudi. Shima fuska a sake ya amsa musu sannan yace su shiga wani daki kusa da na maigadinsa.

Abinci yasa aka kawo musu aka yi musu tarba a mutumce. Sai da suka ci suka koshi sannan ya dawo ya karbi takardun Awaisu. Murmushin fuskarsa ya fadada
"Ikon Allah ashe kaima Bauchi kayi karatu. Kila ma ka taba haduwa da Gimbi."

A ladabce Awaisu yace "Wane ne hakan?"

Alh Mudi ya hau dariya "Yarinyar wajena ce, sune a zaune ita da kanwarta shigowarku dazu. Da yake sunan mahaifiyata gareta shine nake kiranta Gimbiya. To kuma kasan mutane, a hankali sunan ya koma Gimbi."

Harisu da Awaisu suka gyada kai suna Allah Sarki.

Alh Mudi ya cigaba da bayaninsa
"Shekararnan ta gama ATBU din amma Business admin ta karanta. Nayi magana da wani sun karbeta a banki zatayi bautar kasa. Shine kaga ina dariya da na ga kaima bangarenka kenan, to zan tura masa takardunka gobe. Kaga abin ma duk zaizo da sauki"

Godiya da addu'a suka rinka yi masa. Murmushi kawai yayi
"Saminu akwai kirki. Kaya kawai nake saya a wurinsa amma ina jinsa kamar dan uwa saboda iya mu'amalarsa da mutane"

Harisu yace hakane domin shima shaida ne.

Daga nan Alh Mudi ya yace lallai sai Awaisu ya zauna a Abujan domin idan ya bayar da takardun washegari mai yiwuwa zuwa litinin a bukaci ganinsa a bankin.  Sannan yayi alqawarin bashi makwanci har zuwa lokacin. Harisu ya rasa bakin godiya. Mutanen kirki basa karewa a duniya. Sai dai haduwa dasu dace ne. Duk kudin Alh Mudi Maibuta bashi da dagawa da girman kai.

Da safe Harisu ya koma Fika bayan yaja kunnen dan uwansa akan ya kula da kansa kuma ya kame mutumcinsa.
*****

Tun tafiyar yayansa baya fita ko'ina. Kullum yana daki sai sallah da take fitar dashi wadda Alhajin ko wani saurayi da Awaisu bai tantance matsayinsa a gidan ba suke jagoranta. Safe, rana da dare maigadi zai miko masa abinci ya karba da godiya.

Yau lahadi sun idar da sallar magariba Alh Mudi yace ya shigo falonsa su gaisa da iyalin gidan. Domin idan har ya sami aiki an barshi a nan Abujan to dole kafin ya sami wurin zama nan zai cigaba da zama tare dasu.

"Ni kuma ba mazauni bane, shiyasa na ga ya kamata kasan mutanen gidan suma su san ka"

A baya ya bishi suka shiga wani falo wanda aka kawata da duk wani abu na jindadi. Kafin su zauna wata mace ta shigo sanye da hijabi da alamun sallah ta idar. Sai 'yan matan ranar da suka zo biyu da wani yaro da suke sallah tare wanda bai wuce shekara goma ba.

Awaisu ya gaisheta ta amsa da fara'arta ta tambayi sunansa.

Kafin ya amsa babbar wadda yake tsammanin ita Alh Mudi ya kira da Gimbi tace "A.S Abali, Mama shine yayi vice president na S.U.G a makarantarmu"

Da mamaki ya dago yana kallonta. Shi dai bazai iya tuna fuskarta ba amma dai abin da ta fada gaskiya ne. Kyaunta kuwa tuni yayi tasiri a zuciyarsa.

Maman tace "Gimbi rawar kai, ai ba ke na tambaya ba. Naga yayi shiru ne shine nake son jan shi da hira ya sake damu."

Ta koma tana kallonsa "Alhaji yayi min bayanin komai game da kai. Allah Ya bamu ikon zaman gaskiya da amana"

"Amin Hajiya nagode. Allah Ya kara girma"

"Amin, sai dai Mama ake kirana ba Hajiya ba"

Daga nan sun dan taba hira wadda hankalinsa gabadaya yana kan Gimbi. Tunda ta fadi sunansa dazu zuciyarsa take kawo masa sabon tunani game da ita. Sai dai a wurin ya yakice shi. Ai ido ba mudu ba amma yasan kima. Ina shi ina 'yar babban gida irin wannan.
*****

Washegari da sassafe ya tashi ya shirya kamar yadda Alh Mudi ya umarce shi. Yana wurin maigadi suka fito tare da Gimbi. Taci kwalliya tayi kyau sosai.

A bayan mota ta zauna kusa da babanta shi kuma Awaisu yana gefen dreba. Babu inda ya gane a wurin da suke tafiya sai dai kawai yaga an rubuta Zenith Bank. A reception Alh Mudi ya barsu shi da Gimbi ya wuce wurin manaja.

Hira suke tabawa jefi jefi saboda shi dai ya kasa sakewa da ita duk kuwa da cewar ya fahimci sakon da yake boyewa a zuciyarsa itama shine a cikin ta ta zuciyar.

Ba jimawa Alh Mudi ya fito ya bukaci Awaisu ya shiga wurin Manaja. Shi kuma suka shiga wani dakin daban da Gimbi. A nan ne aka yi mata bayanin aikin da zata rinka yi.

Shi kuma Awaisu takardu ne aka bashi yayi ta cike cike. Bayan ya gama aka sanar dashi zai dawo washegari interview sannan yaje Lagos sati na sama training na wata daya daga nan ya jira posting.

No comments:

Post a Comment