*GIDAN MATI*
©BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR
KASHI NA HUDU
Assalamu Alaikum mutan gidan." Fad'in 'yar doguwar dattijuwar kuma tsamurmura mai sharɓa-sharɓan tsagu a gefen bakinta, bak'a ce wuluk kamar d'anta Mati. Mati ne a gaba d'auke da k'aramar akwatin kayanta, ita kuwa tana biye da shi a baya.
Abule ta soma fitowa daga d'aki sai Nene daga band'aki suka saki baki suna kallonta.
'Ikon Allah, wai na kwance ya fad'i.' Cewar Abule kenan a k'asan ranta ganin shigar da surukar ta su ta yi, wata k'aramar Atamfa Super ce ajikinta an mata dinkin riga da siket sai wani babban mayafi da ta yafa a kafad'a ba rufin kai ba. Fuskarnan ta sha farar hoda, ba'a gane wa sakamakon bakin fatarta da ya ciza saidai kuma kana gani ka rantse yanayin hunturu ne wanda ya yi sanadin da fatar fuskar nata ya bushe ya yi furu-furu, ga uban jan janbaki da ta lafta a le66anta masu tudu.
A hankali Nene ta maida dubanta ga Abule, akayi sa'a itama ta kalleta sai kuma suka sauke ajiyar zuciya kafin kowaccensu ta shiga rububin tarbarta da amsa sallamarta.
"Waalaikumussalam, lale maraba." Fad'in Nene kenan ta karasa bakinta a washe ta kar6i akwatin Inna, caraf itama Abule ta sanya hannu da zummar kwacewa ta kai nata d'akin.
"A'a menene haka? Yaushe akayi daren kuma da har ace gari ya waye? Malama sakarmin." Cewar Nene ta na k'ara jogana akwatin a jikinta.
Dole Abule ta saki tana harararta ta karasa wajen Inna cike da kissa ta ce.
"Maraba Inna."
Inna ta hau k'arewa Abule kallo, eh kam ta yarda da rahoton da Aminiyarta Ladidi ta kai mata game da Amarya d'an nata. Ta tabbatar mata tafi Nene tsafta kuma ta ga alama. Sai dai kuma ta kasa fahimtar me ya ja Mati ga aurenta? Wannan abu a dunk'ule haka?
"Yauwa sannunki kema."
Ta fad'i tana mai k'arasawa ta zauna a saman tabarmar da aka shimfid'a. Nene za ta yi ciki da kayanta ta yi saurin dakatar da ita.
"A'a 'yarnan dakata."
Zani na kuncewa tana sake d'aurawa ta karkata k'ugu ta tsaya gami da dire akwatin tana jan majina.
"Na'am, to."
Inna ta yamutse fuska.
"Ai kuma sai dai wannan karon ki hak'ura don a d'akin ita 'yar uwarta ki zan sauka. Na gayamaki bana son kwana kan wannan gadon naki mai warin hammatan wanzamai, da kyar idan kin chanja wannan tsohon zanin gadon wanda na gama yayinsa tun jegon mijinki. Ba wa abokiyar zamanki akwatin na ga na ta kamun ludayinta."
Ai sai Abule ta kece da dariya, kallon banzan da Inna ta watsamata ne ya sanya ta nutsuwa. Nene ta cika ta yi tam! Yau ita Inna za ta ci wa fuska akan Abule? Lallai ya dace ta zage damtse.
Tana numfarfashi ta zauna, Inna ta dubeta sannan ta k'ara duban Mati.
"Wai ni Mati wacece me juna biyun a matanka?"
Mati ya hau washe baki.
"Ai duka biyun ne."
Inna ta kwalalo idanu cike da mamaki tana duban Nene, karshe ta sauke idanunta akan Abule da ta zauna tana wani sussunne kai ita a dole kunya. Sai kuma ta hau tafa hannuwa da shewa.
Farin ciki ya cika su don a zatonsu ta yarda suna da cikin. Sai dai ga Inna kuwa sam zuciyarta ba ta amince Nene na da ciki ba, shekaru nawa da aka yi ta rad'e-rad'in ba ta da mahaifa, ai kuma ta saka ayar tambaya. Dabara ta zo wa Inna.
"Yau na ga abin al'ajabi, to ai shikenan, zama ya kamani a k'auyen nan duk da ba na so, amma zan zauna har na ga 'ya'yanka Mati."
Hanjin cikin Nene da Abule ya kad'a sai dai kowaccensu ta yi fuska. Mati kuwa wani dad'i ne ya mamaye zuciyarsa ganin burinsa ya kusa cika.
Abule ke da girki ita ta shiga hidima da Inna, Nene kuwa d'akinta ta fad'a tana tunanin mafita nan gaba.
*** *** ***
Bayan kwanaki hud'u da zuwan Inna ana zaman lafiya kowacce ta ciki na ciki. Karshe kuma sai Mati ya tsuro da wuni a d'akin Abule wai hira da Inna, haka za ta yi ta tsinkayo dariyarsu.
Da abin ya isheta ta shirya ta nufi gidan 'Yar Magaji don neman mafita. Tana isa ta zayyanemata komai, 'Yar Magaji ta buga uban tsaki.
"Ke ce ai ki ka yi sake da ba ki mallake Mati tun fari ba, yanzu da komai zai zo ma ki da sauk'i."
Jin haka Nene ta gyara zama.
"To yanzu ya za'ayi."
'Yar Magaji ta d'an yi jim, sai kuma ta saki dariya ta mik'e ta fad'a d'aka. Can sai ta dawo d'auke da k'ulli ta mik'amata. Nene ta hau jujjuyawa.
"Na menene?"
'Yar Magaji ta d'an murza hanci tsabar warin da bakin Nene yake yi kamar na 'yan ga ruwa.
"Kinga wannan, k'asar k'ark'ashin gadon ma'auratan da suka tsufa tare ne suna soyayya, matuk'ar kin yi turare da shi na kwanaki uku Mati ya kusanceki to an gama."
Nene ta girgiza kai.
"Matsalar mun fi wata biyar bai nemeni ba, ni kinsan na tsani a maisheni jaka."
Wani kallo 'Yar Magaji ta yi mata sai kuma suka kwashe da dariya 'Yar Magaji na kauda kai.
"Dad'ina da ke ba dai warin baki ba."
Nene ta muskuta tana shafa bakin.
"Um to ya na iya da abinda ya fi k'arfin wuta?"
Ta6e baki 'Yar Magaji ta yi.
"Ke ki ka so, ni yanzu dai kinsan ina jiran kaso na, makira ai ina shigowa daman na ga yanayinki na gane makircinne ya motsa."
Nene ta dara.
Suka gama k'ulle-k'ullensu dai Nene ta koma gida da zummar soma gabatar da aiki.
Muna zuwa...
No comments:
Post a Comment