*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
KASHI NA BIYAR
Inna ta d'aga hanci sama taja iska, sai kuma ta furzar ta baki tana hararar kwanukan da Nene ta aje gabanta.
"Uhm ni wai da mushe kikai miyar ne Nene?"
"Me kika gani Inna?" Nene ta fad'a tana so sa kai.
"A'a gani nayi tunda kika doso gurinnan ya cika da tsami da k'arni tamkar wacce ke aiki a kwata ko mutuware."
'Ai fa, komai na yi ban burge ba, to ai sai dai ki mutu, aikin na Mati ne, mallaka kuma tawa ce, sai shegen kinibibi da wani bakinta kamar na ba'kar Akuya...' Ta faɗa da gunguni
"Me kike cewa ne?"
"A'a cewa na yi Binta Sudan ne na balbala a jikina saboda kiji ƙamshin."
"Ko kuma Binta Maliya ba? To wanann dai ƙarni yake sai a sake lale, ki kwashe kwanukan nan daga gabana, anjima zansa Mati ya karbomin Abincin daga gidan Larai."
"Uhm gaba ta kaini, dama ke na tsamewa kai da ƙafar kazar." Ta faɗa da 'kun'kuni tana tattara kwanukan.
"Baki ji ba" Inna ta fad'a
"Ina ji Inna" Ta fad'a tana gabda barin d'akin.
"Idan gyaran zaki yi ki fara gyara can cikin, shi ne ko da kinsa turaren zamu ji dadinsa, amman wanann in gayamiki gaskiya yau sai an turaramin dakin nan da miski zan iya zamansa. Yanzu haka sai na sha kanwa sabida kumburin ciki."
"To masharranciya." Nene ta fadi a hankali tana barin d'akin a fusace.
Abule dake maƙe a gefe tana sauraro ta k'yak'yace da dariya tana juyawa Nene mazaunai. Nene ta yi kwafa tana gyaɗa kai, kafin kuma ta yi dakinta tana mai sauke kaba.
Gab da Maghriba Abule na tsakar gida tayi ɗaurin kirji, da zabira a hannunta tana tsifar kai. Can daga k'ofa kuma Nene ce zaune tana gyaran Tafasa tana yi tana sakin habaici a waƙe.
"Munafuncin dodo dai mai shi yakan ci, yau ba jumma'a ba idi ba, ba kuma kwanan mutum ba ya d'au niyyar wanka harda tazar kai na asara." Nene ta faɗi da karfi tana hararar Abule."
"Oh ni Abu? Lalle idan ta karewa kare barin haushi yake ya koma tunkuyi, na ga dai abin rabo ne auran Mace da ciki. Ki gwada naki salon mana mu gani, ai wani asirin baya ci da turaren hayaki sai an had'a da yan dabaru."
"Uban wa ke asiri da turare?" Nene ta faɗi a fusace tana ture fai-fain tafasa gefe."
"A'a ai kinji matsalarki baki cin ribar magana, yanzu mene na sakin na maguzawa a wannan hirar? Ni kinga wucewata yin abinda zai fisshe Ni. Ta faɗa tana mai sunkutar bokitinta ta fada Makewayi.
Nene ta ciji yatsa tana mai tura baki gaba, sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan da Abule ke d'orawa saman yar katangar bandakin ta langa-langa. Abin mamaki harda wani tsohon dankwalin wata atamfarta me fanteka da mati ya sa mata tun a toshi. Har dai ta juya zata wuce, sai kuma dai ta sake juyowa tana kallon katangar zuciyarta na kiyastamata abinda Abule ke yi da kaya haka. Nan fa idanuwanta suka sake sauka kan wata tsummar rigar Mati da tun yana Saurayi ta sanshi da ita. Wani makirin murmushi ta saki da ta gama hasaso abinda take zato. Ai sai tayi gun 'yar katangar a hankali ta janye kayan bata bar mata komai ba sai zanin da zata yane jikinta.
Da sauri tayi ɗaki gurin Inna dake gyangyadin shaiɗan na gabda Maghriba. Itama Innan sai da ta firgita na ganin yarda Nene ta fad'o Mata ba ko gafara dai.
"Lafiya Nene kika katsemin barci haka dan rashin mutunta Uwar Miji?"
"Bari dai Inna, ai abinda na gani yau idan ban sanar miki ba na cika ma-ci Amana, na rantse miki da izifi sittin Abule cikin zani gare ta. Idan baki yarda da batunnan ba biyoni kofar Makewayin ki gani."
Inna ta watsa mata wani kallo she'ke'ke, sai kuma ta mi'ke tana tura d'aurin kallabinta gaba."
"Muje na gani." Ta fad'a tana yin gaba.
Abule da ta gama jika-jikan ta mi'ke za ta mai da zannuwanta ta d'aure yanda ta saba, ai sai ta tarar babu, ta d'auka ko baya suka faɗa dan haka ta fito a sad'ad'e tana Addu'ar Allah ya kau da idon Nene har ta kwashe. Sai dai fa turus! Ta yi ganin Inna da Nene tsaye tana sakar mata dariyar Mugunta. Jiki na tsuma ta sunkuyar da kanta 'kasa.
"Shegiya guntuwa me bakin hali, abinda ban zaci gare ki ba sai gashi ya tabbata gunki. Uwar wa ta koyamiki wanann kinibibin ko dan ganin yar uwarki na da cikin? Inna ta faɗi tana mai kai mata rankwashi a jikakken kanta.
"A'a Inna lafiya kike bugurmin Abule" Mati ya faɗa da shigowarsa kenan.
"Zaka rama mata ne? Sha-sha-sha kawai, Matarka na cikin Zani dan sakarci ka kasa gane wa."
Ya kwalalo ido yana dubanta, sai kuma ya hau sosa kai yana noƙewa.
"A'a Inna ya za ai na sani, abinda rabon da ayi abu tun watan shekaran jiya.
Ai sai Inna ta hau tafa hannu da Sallallami.
"Haka Auren ya mayarmin kai Mati sai abinda Mace take so?Mene amfanin auren idan ba za ka taki mace tamkar gona ba? Ya kinan baƙar Munafuka sai kin faɗimin abinda kike bawa dana da har kike juyashi haka ko kuma ki tafi gidan Ubanki wallahi."
Ta faɗa tana jawo gashin Abule. Da sauri Mati ya shiga tsakani yana faɗin "Sakarta Inna."
Da dai Abule ta fito daga hannun Inna ai sai tayi kan Nene dake ta sheka dariya a fusace tana faɗin " Bazan fita Ni kaɗai ba sai da ke bakar mujiya muga naki cikin mana in gaske ne." Ta kai mata wawura.
Nene ta kankame jikinta tana ture Abule, ta ɗaga hannu zatai naushi, Abule tayi nasarar bankare hannun ta kuwa gatsa mata cizo a hammata da dazunnan ta barbadawa hammatar toka dan ta rage tsami, ai kuwa bata ɗaga bakinta gurin nan ba sai da ta cisge gashin hammatar Nene har jini yayi tsartuwa.
Nene ta saki ihu tana dafe hammatarta. Abule kuwa ta yi wuf! Ta fisgo zanin Nene sai ga tullin tsummokara ɗaure a ciki. Wani abin mamakin har da wani koren Gajeran Wandon Mati da ya gaje shi tun gurin ƙaninsa yasha doyin jakai da warin fitsari, da Mati ya shafe shekara yana nemansa, yau sai gashi a cikin Nene ɗaure...
Muna zuwa.
No comments:
Post a Comment