Tuesday, 23 January 2018

Kashe Fitila 6

*KASHE FITILA*💡6

*Batul Mamman*💖

Tun daga wannan rana Awaisu yake wasan buya da Harisu. Duk inda yasan zasu hadu su kebe guduwa yake yi. Ranar da zai koma Abuja ma kamar ana korarsa don sauri. Haka ya tafi tasha kafin Harisu ya dawo daga shagonsa inda ya ajiye masa kayan amfani kamar su madara da ganyen shayi da yake son bashi guzurin tafiya.

Baiyi sati da komawa ba Alh Mudi ya dawo daga Kano. Wata rana da yamma ya tura karamin dansa ya kirawo Awaisu. Da ya zo ne ya tabbatar masa da Gimbi ta sanar dasu abin da ke tsakaninsu. Karshe yace yana so ya sanar da yayansa cewa su same shi a Kano shi da Saminu idan har da gaske yana sonta da aure suyi magana.

"Ban yarda da bata lokaci ana soyayya ba indai akwai halin yin auren gara ayi kowa ya huta."

Gaban Awaisu ya fadi jin Alh Mudi ya ambaci ganin yayansa da Saminu. To da wane idon zai kallesu ma. Shi dai Alh Mudi bai san me yake faruwa ba. Albarkacin Saminu yake ganin lallai Awaisu ma mutumin kirki ne kamar yadda ya kula a dan zaman da yayi dasu.

Bai sami damar komawa gida ba sai bayan sati biyar ana hutun Good Friday da Easter Monday. Haka ya tafi jiki babu kwari saboda rashin sanin yadda zai tunkari dan uwansa da maganar auren Gimbi. Gashi Alh Mudi yace su same shi a gidansa na Kano. A son ransa ayi bikin bayan sallah karama tare da na babban dansa wanda suke a Kanon tare da babarsu uwargidan Alhaji.
*****

Kwanansa biyu da dawowa ya rasa abin da ke masa dadi kuma ya kasa fadawa kowa. Maamu tayi fadan da magiya duka yaki cewa komai. Gashi yana matukar son Gimbi baya fatan rasata.

Da daddare yana kwance a dakinsa Harisu ya shigo. Ya tashi zaune amma ya kasa cewa komai.

Harisu yayi murmushi yana kallonsa. Sai da ya zauna a gefen katifar dakin ya soma magana.

"Yanzu ni kake gudu saboda ka soma aiki a Abuja kayi kudi ko. Kana ganin kafi karfinmu."

Awaisu ya zaro ido a razane "Yaya me ya kawo wannan zancen kuma? Wallahi ba haka bane. Allah Ya kiyaye. Bana fatan abin da zai kawo min tunani makamancin haka"

Harisu ya daure fuska "haka kawai za ka fara guduna ne idan ba kana tsoron a ganka tare da talaka irina ba."

Idanun Awaisu tuni suka yi ja saboda rashin jindadin kalaman yayansa. Shi da ya dauki Harisu uba yaushe ma irin wannan tunanin zai zo masa.
"Wata matsalar ce daban Yaya"
Ya fada a raunane.

Harisu yayi dariya a zuci domin ya samu Awaisu ya fada tarkon da yayi masa na son jin damuwarsa.

"Ina jinka, menene matsalar da take hanaka walwala a gidan nan?"

Babu amfani cigaba da boyewar shiyasa ya fada masa maganar da yaji sunyi da Saminu da kuma wadda suka yi da Alh Mudi.

Wani dogon numfashi Harisu ya ja. Ya jima yana tunani kafin ya soma magana cikin nutsuwa.

"Kai ba yaro bane da zan ce baka san abin da kake yi ba. Sannan ka wuce ayi maka auren dole. Duk yadda nake son ka auri Mardiya ba ni zan zauna maka da ita ba. Saboda haka nagode da ka fada min da wuri kafin ayi auren muji kunya. Zanyi kokarin fahimtar da Saminu. Kuskurena ne da ban fara maganar da kai ba na fada masa"

Ko bai fada ba yasan ransa a bace yake kawai ya danne ne "Kayi hakuri Yaya. Itama Gimbi tana da kyawawan halaye idan ka ganta ....."

Bai karasa ba Harisu ya mike batare da yace komai ba yayi hanyar fita. Tunaninsa bai wuce yadda zai fita kunyar Saminu ba. Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba yace
"ka shirya muje Kanon gobe kafin lokacin komawarka aiki."
*****

"Zancen banza kai, ina Awaisu ina 'yar masu kudi. Ko kuwa so yake ya janyo ace yayi auren jari? To ma a ina yake tunanin ajiyeta idan anyi auren.  Yaushe ma ya fara aikin da zai jajibo aure irin wannan"

Maamu ce take ta fada bayan Harisu ya sanar da ita da Baaba batun tafiyarsu Kano neman aure. Haka tayi ta fada yana bata hakuri da nuna mata magana kawai zasu je yi ba auren za'a daura ba.

Ranar da suka isa Kano Saminu jiki a sanyaye ya tarbesu. Wannan ya dagawa Harisu hankali ko har Alh Mudi ya sanar dashi komai. Baya son abin da zai taba alakarsu ko kadan. Shi Awaisu dama ya kasa kallonsa ma. Tunda suka zo yake sunkuyar da kai.

Bayan sun dan huta ne suka zauna tattaunawa. A nan Saminu ya dubi Harisu "Alh Mudi yazo gidan nan da kansa akan yana son na bawa dansa auren Mardiya. Sanin cewa munyi magana da kai nace na bayar da ita ga Awaisu. Shine yayi min wani bayanin daban da ban gama fahimta ba "

A kunyace Harisu ya fada masa abin da ke faruwa.
"Kayi hakuri abokina, bani da masaniya akan hakan. Da tun farko bazan bijiro da maganar hadasu ba"

Awaisu duk sai yaji babu dadi. Yanzu da Alh Mudi baizo nemawa dansa ba shikenan ya bata zumuncin abokan.

Muryar Saminu ce ta katse masa tunani "Babu komai, ai kaga yadda Allah Yake nuna ikonSa. Sai muje gidan ka fada masa ka bada auren Mardiya ga Fawaz a matsayin waliyinta tunda bani da dan uwa namiji. Shi kuma Awaisu sai na nema masa auren Gimbi"

Sai a lokacin Harisu yayi murmushi hankalinsa ya kwanta ganin Saminu bai dauki abin da zafi ba.

Washegari kuwa suka dunguma sai gidan Alh Mudi aka daidaita magana. Sallah karama da sati biyu aka sha bikin Awaisu da Gimbi. Ganin cewa bai samu muhallin kirki ba Alh Mudi ya bashi gida da sunan Gimbi a Abuja inda zasu fara zama kafin ya sami nasa. Ita kuma Mardiya suka tare a Kaduna ina Fawaz yake aiki.
*****

*Bayan shekara 12*

Cikin shekarun da suka gabata Awaisu ya sami budi sosai. Domin har gida ya gina kato a Abuja yana shirin tarewa. Inda Allah Ya kara taimakonsa shine kasuwanci da yake yi. Duk da yana aiki ga rashin lokaci haka ya sami yara biyu 'ya'yan kawunan sa da ya budewa shago suke sayarda atamfa da shadda. Abu kamar wasa sai da ya hada shaguna hudu a jere a Wuse market. Ga kwazonsa a wurin aiki yasa ya sami mukamin manaja a bankin.

Gidan Harisu kuwa yasha gyara sosai har mota ya saya masa sannan ya kara masa jari. Zamansu gwanin sha'awa. Tsakaninsu da Gimbi babu wata matsala. Dayake itama aikin bankin take yi bata da lokaci na zuwa Fika sosai. Yaransu hudu babban ciki Haris, sai Daula mai sunan babar Gimbi, Amir mai sunan Alh Mudi da kuma auta Sa'ad suna kiransa Mu'allim.
*****

A gajiye Awaisu ya shigo bayan isha yaran suna ta murnar dawowarsa daga Fika. Sai da ya gama dasu ya wuce dakinsa. Sauri yake yi idanunsa su gane masa matar da yake jin bazai taba iya hadata da kowa ba saboda irin son da yake yi mata ga kuma albishir a bakinsa.

Taci kwalliya tayi kyau sosai tazo ta tarbe shi tana murmushi
"Ashe ka shigo maimakon ka kira kafin ku karaso na hada maka ruwan wanka"

Ya shafi gefen fuskarta yana murmushi "kada ki damu, zo ki zauna kiji albishir din da nazo miki dashi har biyu. Dayan ina hanya akayi min waya aka fada min"

Kaskon turaren wutan da yake gefen gado ta dauke sannan ta dawo ta zauna kusa dashi yana rungume da ita yayi ajiyar zuciya.

"Gimbina Allah Ya yarda. Visa dinku ta fito"

Ta dago kai da sauri cikin farinciki "wace visa kuma?"

"Dama na boye miki ne sai komai ya tabbata. Na biya muku Hajji ke da Yaya Harisu, Baaba da Maamu. Sai Yaya Zakiyya tunda su Anti Baraka da Ummu mazansu sun kaisu. Kinga za ta tayaki kula dasu Baaba. Albishir na biyu kuma kuna dawowa nake so mu tare a Apo. To babban abin jindadin shine dasu Maamu zamu tare"

Shiru yaji Gimbi taki dagowa bare tayi magana. Ko da ya dago kanta hawaye  take yi sosai. Wani sonta ne yake shigarsa domin yasan kukan farinciki take yi. Rungumeta yayi yana shafa bayanta.

"Dama nasan zakiyi murna sosai Gimbina. Shiyasa ban fada miki batun tafiya Hajjin ba sai da na gama. Tunda kinga ni naje har sauu biyu kuma last year munyi umara tare dake. Shiyasa bazan bi ku ba. " ya cigaba da cewa
"Kuma fa yadda naso har da Baaba zamu tare. Sai dai lalurar idonta yasa Yaya yaki yarda. Shine na hakura ba don naso ba. Burina ya cika zan dawo da Maamu kusa in kula da ita. Itama taji dadin arzikin da Allah Ya bani. Ta dade tana jin nauyin su Baaba da Yaya Harisu. Duk da naso hadawa da Baaba hakan bai samu ba. Amma zan dauko Rumana. Gimbina da ina da yadda zanyi fa wallahi Yaya Harisu ya dena fita neman kudi. Komai ni zanyi masa"

Can kasan makoshi tace "uhmm hakane." Domin ji take yi ya cikata da surutu mara kan gado.

Mikewa yayi ya shiga bandaki domin yayi wanka ko zaiji saukin gajiya.

Yana shiga Gimbi ta fice ta tafi dakinta ta rufe kofar da mukulli. Gadonta ta hau ta saki kuka cikin tashin hankali. Ko da wasa bata taba kaunar zama da uwarmiji ko dangin miji ba. Can daga nesa dai yayi musu kyauta suna kauye ba sai sun rabesu ba.

"Tabdi, akwai matsala. Matar da ko Hausar kirki bata iya ba sai anyi magana tayi ta yankare hakora tana murmushi. Shine don kana jin ka fara kudi zaka dauko min su ka kawosu ko neman izini na bakayi ba. Da sake Awaisu....bana cikin matan da za'a hada da uwarmiji ace mu zauna lafiya gida daya"

Dankwalinta tayi jifa dashi ta rasa me yake mata dadi. Ita fa shi kadai take so ba danginsa ba. Duk halaccin da tayi masa ta aureshi talaka ko gidan zama bashi dashi. Shine yanzu arzikin nasa kuma sai sun raba tare da wadda bata nan lokacin da suke nema. Ta hana kanta sukuni tana fita aiki duk domin ta taimaka masa. Ba don kada ace tayi sharri ba ma sai tace gabadaya gidan Harisu wari yake yi mata idan taje Fika. Shiyasa bata son zama idan taje.

No comments:

Post a Comment