Monday, 22 January 2018

Kashe Fitila 5

*KASHE FITILA*💡5

*Batul Mamman*💖

Abu kamar wasa sai gashi komai ya kankama dangane da samun aikinsa. Awaisu ya koma Fika sanar da mutan gidan halin da ake ciki da tafiyar da zaiyi Lagos.

Kafin ranar tafiyar Maamu ta tura shi wurin yayanta ya karbo rago biyu cikin tumakin da ake yi mata kiwo ya sayar. Da kudin wanda ko sisi bata cire a ciki ba tace yayi kudin mota da guzuri.

Kamar kullum kyakkyawar addua yayi mata tare da godiya.
"Ba godiya zakayi min ba. So nake idan kaje ka dage yayi abinda ya kaika. Lokaci yayi da ya kamata ace kana da iyali kaima sannan ka fara ragewa dan uwanka nauyi. Ga zuri'a Allah Ya bashi sosai. Kaga yanzu cikin yaran sai ka rinka biyawa wasu kudin makaranta idan ka fara daukan albashi"

"Maamu kenan, Allah Ya bani iko. Nifa babban dana ma sunansa Haris. Tun yanzu ya kamata ki fara kirana Abu Harith irin na Larabawa"

Neman abin da zata buga masa tayi saboda rashin kunyar da yake yi a gabanta. Ba shiri ya tashi ya gudu.

Bayan kwana biyu Harisu ya raka shi tasha ya wuce Lagos. Watansa daya wurin induction din sababbin ma'aikatan banki. Ana gamawa ya koma Abuja domin jiran posting. A wannan lokacin ne kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsa da Gimbi. Tun yana ja da baya har ya amince. Ji yake yafi kowa sa'a. Mace kamarta tana soyayya da talaka irinsa.

Da taimakon Alh Mudi ya samu aka barshi a Abuja maimakon Ilorin da aka tura shi da farko.

Ganin yana da kwanaki goma kafin lokacin fara aikin ya hada kayansa sai gida. Gimbi harda kuka da zai tafi saboda sonsa take da gaske. Alkawari yayi mata cewa bazai wuce sati ba zai dawo sannan suka rabu.

Yana isa gida yara suka fito ana ta murnar dawowarsa. Ya shiga ciki nan ma su Baaba sai murna aiki ya samu. Nan yake jin kwanaki hudu da suka wuce matar Harisu ta biyun ta haihu. Kai kace shi aka yiwa haihuwar ya fita neman dan uwanansa yana murna.
*****

Washegari suna zaune a bakin shagon Harisu suna hira Awaisu yace ya zabawa jaririya suna Ummu Ruman. Amma Rumana za'a kirata.

"Kai kuma a ina kaji wannan sunan" Harisu ya tambaya yana kallonsa.

"A littafin tarihi"

"Idan munje gida sai kayi mata huduba dashi" cewar Harisu

Duk da cewa ya riga yayi mata da suna Aisha amma baya son batawa kaninsa. Shima kuma Awaisun da yasan da hakan bazai taba kawo wani sunan ba.

Sai yamma suka koma gida. A bakin kofa ya tarar da dansa na biyu yana shirin fitowa.

"Sarkin yawo ina zaka da yamman nan"

"Baba kayi bako daga Kano. Shine aka ce na kirawo ka"

Harisu ya shiga ciki dakin Baaba inda suke yana tunanin waye yazo.

Abin mamaki Saminu ya gani tare da matarsa da yaransu biyar. Tsabar murna ya rungumeshi suna dariya.

"Bala dreban tifa ne ya fada min haihuwar nace to lokacin tada zumuncin mu fa yayi. Dole mu hada kan iyalinmu."

"Sosai kuwa, sannu yaya hanya"

Matar Saminu mai suna Amina da yaransa duk suka gaishe da Harisu. Ana ta barkwancin yadda zasu rinka magana tunda Hausa a gidan bata zauna sosai ba. Baaba da Awaisu sune masu Hausar sosai. Awaisun shima ya shigo suka gaisa. Fita yayi sauran kudin hannunsa yasa ya siyo lemo, kaji da kwai ya bawa Maman Antu uwargidan Harisu domin karrama baki. Yaushe zai manta Saminu a rayuwarsa.

****
Kwanansu hudu a gidan duk an saba kamar sun dade tare. Yaranma kowa da abokin sa ban da babbar wadda ta girmi duka yaran gidan.

Ana gobe zasu tafi ne Harisu da Saminu sun zauna hira da daddare Harisu ya sako zancen da yake ta son yi.

"Mardiya shekararta nawa ne yanzu?"

"Ka ganta tayi tsayi ko? Shabakwai zatayi da azumi.  Badi zata gama sakandire in sha Allah"

Harisu yayi murmushi "To Allah Yasa abin da zan zo dashi yayi maka. Nace mai zai hana mu hadata da Awaisu?"

Saminu ya kalle shi sosai "da gaske kake yi?"

"Indai ka amince. Wallahi Saminu ban taba ganin mutum irinka ba. Halayenka abin koyi ne ga wasu.  Idan na bari damar nan ta wucemu ai na cuci zuri'ar Awaisu. Mai alkhairi irinka dole a kyautatawa 'ya'yanka zato"

Saminu ya kama hannunsa kam "in dai haka ne na bawa Awaisu Mardiya halak malak inyi maka ta yara"

Dadi ya kama Harisu suna dariya "in sha Allah Awaisu bazai bamu kunya ba. Dama watan da ya wuce na gama biyan su Zakiyya kudin gidan Malam da ya fada rabonsu a gado. Gyara shi zanyi sosai kafin shekara  mai zuwa shima Awaisun ya tara abin da ya tara sai su zauna a ciki. Ba munyi maganar a Abuja zaiyi aiki ba? To muna sa rai zai sami muhalli kwanan nan. Kaga sai su koma can ya sa ta cigaba da karatu ma"

Saminu farinciki ya cika zuciyarsa. Shi yana yiwa Harisu kallon mutumin kirki. Shima Harisun kallon da yake yi masa kenan.

Sun yanke shawarar sanar da Mardiya babbar 'yar Saminu da Awaisu shawarar da suka yanke domin jin ta bakinsu da kuma basu hakkinsu don kada a zalinci kowa.

Awaisu wanda yake bayan kofa tun bayan yaji an ambaci sunansa ya fasa karasawa wurinsu. Ji yayi kamar an dora mada dutse a kansa. Shi kadai ya soma magana a hankali "yanzu wannan yarinyar da bata gama zama mace ba za'a bani? Wallahi da sake. Ko ban hadu da Gimbi ba babu inda zan kai wannan yarinyar"

No comments:

Post a Comment