Monday, 22 January 2018

Gidan Mati 11

*GIDAN MATI*

©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR

BABI NA GOMA SHA DAYA

Abule ta yi k'asa-k'asa da murya.
"Makarin shine a jik'a wandon kwarto a shanye."
  Nene ta zabura tayi zaman 'yan bori wanda ya yi daidai da sullu6owar tusa ta mai k'ara. Abule ta toshe hancinta, a hankali Nene ta numfasa har da lumshe idanu don ba k'aramin sassauci ta samu a cikinta ba.
  "Na shiga uku, yanzu ina zan ga kwar... Af! Fad'uwa ta zo daidai da zama ai Abule, yo bana manta ashe muna da su a kurkusa ba? Ga Basharin Shafa?"
  Abule wacce itama shaf ta mance da batun Jik'an Lamid'on ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin zuciyarta wasai, babban abinda ya sanyamata damuwa da lamarin ba komai bane sai na tsoron kada ya kasance Nene bata warke ba ta tonamata asiri mutan gari su zageta. Ta daki cinyarta tana mai washe rinannun hak'oranta.
  "Kai Allah mungode maka, ai ni dinma kaf tunanina bai je nan ba. Ko jiya da daddare ya haurawa Kulu Gurguwa."
  Suka saki shewa don Nene har ta hango warakarta a sauk'ak'e.
  "Kai Allah Ya k'arowa Bashari ilimin kwartanci, wannan ai gaba ta kaini. Ashe kwarto da ranarsa. (Kun ji jahilci!)"
  Dariya suka k'ara kwashewa da ita.

  A yammacin ranar Shafa na durkushe a gaban murhu tana kokarin iza wuta ta tsinkayi sallamar Nene da Abule.  Da mamaki ta dubesu kafin ta mike. Abule ta ci burki anan tana k'arewa gidan Shafar kallo domin rabonsu da shiga gidan har sun mance. Daga can gefen garu ta hangi jerin manyan duwatsu wanda ta taimakonsa ne Shafa ke k'arewa cikin gidansu kallo. Ta6e baki ta yi gami da bin sahun Nene da har ta shige rumfar Shafar ba tare da ko neman izni ba.
  Shafa za ta yi magana Abule ta hanata ta hanyar rik'o hannunta tanamata alamar ta yi shiru gami da yi mata nuni da gidansu, nan take ta fahimci ba su kaunar Fad'ime da Inna su san da zuwansu. Ta gyara zaman d'aure kirjinta suka shige ciki.
   Nene ta washe baki.
  "Shafa Shafa, Shafar Bashari, uwargida ran gida! Kin tare gaba kin tare baya, turmin tsakar gida sha lugude!"
  "Wannan haka yake." Fad'in Abule tana gyada kai kamar k'adangaruwa.
  Shafa ta yamutsa fuska tana kallonsu d'ai-d'ai.
  "Halan dai Nene acan asibitin har allurar mahaukata suka manta suka yi maki?"
  Nene ta hau daure fuska za ta kwa6omata mai zafi ganin haka yasa Abule saurin tarewa.
  "Kai Shafa, dad'ina da ke zolaya. Nene ai taki ce, banda abinki ai makwafci ance ya fi dan uwa, a baya ma rashin fahimta ne."
  Dariya Shafa tayi gami da tafa hannuwa. Nene da Abule suka dubi juna, dakyar dai suka shawo kanta ta yarda zata sauraresu.
  Nene ce ta soma magana bayan ta gyara zaman nafkin dinta.
  "Ki taimakeni Shafa ki bani aron wandon Bashari."
  Shafa ta fiddo idanu gami da dafe k'irji.
"Yau naga ta kaina! Nene me zakiyi da wandon Basharina? Anya Nene ba ki samu matsalar kwakwalwa ba? Au to na fahimta, wato dai duk matattarar kwararar gudawar da aka sanyamaki bai isheki ba sai kin had'a da wandon Basharina? To mine amfanin na Mati?"
Nene ta share zufa tana girgiza kai. Abule ta cafke zancan.
  "Kinga Shafa duk ba haka bane, wannan maganar da za mu yi sirri ce, don Allah ki rufamana asiri."
  Shafa ta dan zubamasu idanu na 'yan dak'ik'u kafin ta gyada kai don ba za ta bari gulmarnan ta wuce ta ba.
  "Ina jin ku."
  Abule ta zayyanemata duk abinda ya faru da kuma makarin asirin.
  Shafa ta saki shewa har da tafa hannuwa.
  "Yau abin namu ne! Oh ni matar na Lamid'o!"
  Saida ta basu wuya Nene harda matsar kwalla sannan ta amince da sharad'in Nenen za ta kyautarmata da tunkiyarta da take kiwo. Ba musu Nene ta aminta daganan ta mik'e ta fita zuwa d'akin kwanansu ta hau lalube.
  Jimawa kad'an sai ga ta rik'e da wani tsohon wandon Bashari da ya gada gun Lamid'o ta mik'amata.
  "Gashinan, kuma kada ya kai gobe a wajenki, ko ta katanga ki jehomin."
Nene ta hau godiya kafin kuma cikin lallami ta ce.
  "Ki taimakamin Shafa, ki bani sabon d'inki mana."
  "Cab! Ai idan kinga Bashari ya yi sabon dinki to mutuwa akayi a danginsa don haka ban bayarwa, idan ba kwa so ku k'ara gaba."
Ta k'ara he tana girgiza k'afa gami da jefamusu tafin hannunta.
  "A'a me ya yi zafi? Mu je Abule hakan ma ya wadatar" " To karki manta dai ki jefon ta katanga." Da komawarsu kuwa Abule ta tarkata lallen ta watsar Masai, shi zaman duniya dama rabo ne, idan ba ka da shi kuwa za ka zo ne a banza ka koma a wofi. Tuna hakan ya sa ta nutsuwa ta ma fita daga batun Fadi. To haka ma ga Nene sai wayar gari akai aka ganta sumul tamkar mai bugun Iska. Itama ta mai da rayuwarta shiru ta hanyar aro nutsuwar dole. Daga bisa ni ta kulla Amintaka da Shafa ba ma ta zaman gidan balle ta zubda hali.  Bayan watanni, ranar wata laraba wanda ya yi daidai da kwanan Inna guda a birni ta je hado kayan haihuwar fadi. Faɗimen ta tashi da nakuda. Gidan daga Abule sai Nene dake shirin fita.
  Ta gyara zaman yafenta tana mai sauke kabar shiga d'akinta. Ta juyo gami da duban Abule, za ta yi magana kenan suka ji nishi da salatin Fad'ime. Cikin hanzari suka dubi juna.
  "kinji abinda na ji?" Abule ta ya tsina fuska" na ji mana kila abinne ya zo."  "To ya za ai ko mu dubu yar magaji... " Abule ta ƴi saurin rufe mata baki. "Ke gafara, kinmanta yanda ta musanya miki magani? To yaune ranar ramuwa dan haka maza kwaɓe gyalen nan ki dauka surfe mu yi yanzu dan karma makota su jiyo bayan awa guda ma lekata."  Da sauri Nene ta aje gyalen ta juye hatsinta a turmi suka hau dukansa ba ka jin karan komi sai tunkwal-tunkwal.
  Fadime cikin azaba haka ta rarrafo bakin kofarta tana kiransu amman suka yi biriss da ita. Har sai da suka bar jin muryarta tukun suka zubda taɓaren suna ma su nufarta. Ganin ruwa gefenta ya sa Nene zare ido "Ke abu ai  fayar ta fashe."
Abule ta karasa itama tana lek'e-lek'e, a karshe suka kinkimi Fad'ime suka maidata ciki. Haka suka kar6i haihuwar santalelan d'anta suka yanke cibi. Nene dake rike da jaririn wanda bai bar komai na Mati ba, katon kan Fad'ime ya yo. Ta yiwa Abule ido kafin ta fice zuwa d'akinta rike da jaririn wanda ta cusawa yatsanta a bakinsa gudun kada sautin kukansa ya ankarar da gulmammun makwaftansu.
  Abule ta dubi Fad'ime wacce ba k'aramin k'aruwa ta samu ba wajen haihuwa sai murk'ususu ta ke da alamar dai akwai abinda ke damunta. A hankali ta sulale ta bi bayan Nene. Idanu ta ware a tsorace ganin Nene na kokarin sanya jaririn cikin kwali.
  "Nene! Bakya tsoron asirinmu ya tonu?"
Nene ta harareta.
"Kinsan iyakar tsawon lokacin da na dauka ina ajiyar kwalinnan? Ai bazan bari damarnan ta kufcemin ba, yau dan kwal ubannan sai kwanan daji."
  Kafin Abule ta ce wani abu suka tsinkayi sallamar Mati.
  A razane suka dubi juna har Nene batasan sadda ta cire yatsanta daga bakin jinjirin ba ai kuwa ya canyara kuka.
  "Lafiya Fad'i? Kin haihu ne?"
  Mati dake jefowa Fad'insa tambayoyi ya tsaya gami da saurin bin inda ya jiyo kukan jaririn.
  Duk kokarinsu na kada ya fahimci shirunsu saida ya gane. Nan ya hau salallami, wani wawan tsalle da ya doka sai gashinan gaban Nene, ya kwasheta da mari kafin ya fiddo jaririn daga kwali.
  "Ka gantanan, yasin ba hannuna ciki! Yanzu na shigo daga makwafta ina.." Fad'in Abule yayinda Mati ya katseta da sauri.
"Dalla can rufemin baki kema bakar munafuka! Wato kun yi shirin kashemin mata da d'a ko?"
Sautin karar Fad'ime ya kid'imashi, a guje ya fice zuwa d'akinta.
  Kan kace me Shafa da Delu sun shigo domin tun kukan jaririn na farko sun tsinkaya saidai ba su k'ara ji ba sai yanzun da Mati ke balbalin fad'a. Lek'owarsu suka san abinda ke faruwa suka bazamo cikin gidan.
Su ya bari a wajen Fad'ime yayinda ya fice nemo abin hawa don mik'a Fad'ime asibiti.
  Delu na gyara jaririn tana zubamusu habaici Shafa na tayata. Su kam kowacce na d'akinta sun k'unshe gaba daya a tsorace suke da abinda zai biyo baya.
  "Shegen, ashe d'agamin k'afa kawai ya ke." Fad'in Nene a k'asa-k'asa tana shafa kuncinta.
  Mati na dawowa aka wuce kai Fad'ime ga likita bayan ya kora Nene da Abule gidajensu da shika (saki) d'ai-d'ai.

No comments:

Post a Comment