Thursday, 18 January 2018

Gidan Mati 2

*GIDAN MATI*

         ©ƁINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR

KASHI NA BIYU

Daga waje kuwa Nene na jin haka sai ta yi wuf ta fito daga maɓoyarta, can baya take zagayawa ta hau kan ɗan dutse tana kasa kunne a ƙaramar tagar ɗakin Abulle. ta na yi tana leƙa bayanta ko wani zai taho wucewa kasancewar daga nan ana hangen waje a dalilin gajartar katangar.
 .    Ɗakinta ta shige da saurinta, jiki na rawa ta hau sauke kwallayenta tana faɗin; "Idan sammako ku kayo, ni asubanci na yi."
  Ta fiddo wani maganin gargajiya wanda tayi mugun tsanar warinsa, sannan ta mai da kayan ta afka garin kusan rabi a baki. Kan ka ce mene wannan cikinta ya murɗa ga yunƙurin amai da ta soma. Ai a guje ta fito ta isa gaban makwararar ruwa ta hau sheƙa aman iyakar ƙarfinta tana nishi yanda ta tabbatar za su tsinkaya...

"Ni fa kamar kakari nake ji."  Cewar Mati yana kallon Abule.
"Kai fa daɗi na da kai har yanzu baka bambance kukan Jakinka dana Akuyar Delu."
"To idan ma itan ce kinyi zaune salon tamin ta'adin da ta saba?"
   Ya faɗa yana mai mi'kewa tsaye, itama da sauri ta mi'ke tana mai rufa masa baya.
        Ita ɗin ma ta wajen jin tahowarsu ya sata zubewa gefen kwatamin tana mai ri'ke cikinta da faɗin "Wayyo! Mati..."
      Da gudansa ya 'kara so wajen yana mai janyeta gefe.
"Ikon Allah! Nene ashe ke ce. Sannu me kika ci ne haka?"
"Ba komai tun safe nake jin tashin zuciya da rashin jin daɗi."
Ta faɗa da ƙyar tana sauke numfashi.
   "A'a irin wannan ciwon ai ba na shiru ba ne Nene, karki manta da haka Sahura ta mutu da irin shirun nan."
"To Mati ana ta kai wa yake ta larura? Taimaka min zakai Abule ta dubomin 'Yar Magaji, ji nake kamar ana daka yaji a kirjina."
"Huu'umm!" Abule ta faɗa tana tafa hannu.
"Ai wallahi da aiken kishiya gwamma na jibgi Uwar miji. Kai ni ban ma yarda da wannan ciwon ba. Saboda Allah Mati baka ji warin tazargaje ba?"
  Ta faɗa tana mai ɗaɗɗaga hanci sama.
"Me kike nufi ne? Kinga Abule ban san fitina, ya mutum na halin ciwo kina kawo shashanci. Idan na isa dake to maza ki je ki dubomin 'Yar Magaji."

  .        Mintuna kaɗan Abule ta dawo da 'Yar Magaji biye da ita ta rataya wata tutturna jaka me kama da ta wazirin Sarkin kutare.
         Kallo ɗaya tama Nene maƙaryaciyar zuciyarta ta kisa mata menene,
dan haka ta kalli Mati da murmushi.
"Malam ai ba wata larura ba ce mai girma, ƙaruwa ce zaku samu, a taƙaice dai Nene ciki gare ta har na tsawon wata biyu."

      "Kan babban bala'in can! Alkur'an wannan ƙarya ce."
Abule ta faɗi  tana mai buga tsalle gefe, kafin kuma ta yi ɓarin da Nene ke kwance.
   "Ke Nene ki ji tsoron Allah, ina ce ba shekaranjiyar nan muka gama rikici kan tsumma na da kika yaga kikai kunzugu da shi ba?"
"Wayyo Ni Abule! Yau na ga abinda yafi 'karfina, wai cikin ma har kinsan  ya yi wata biyu sai ka ce wacce kika haɗa iri da Mayu. ke kam 'Yar Magaji anyi tantiriyar ma'karyaci wallahi. Matar da ake raɗe-raɗen Aljanu sun sace mata mahaifar ne ke da ciki?" 

"Ke! Ke! Abu kin cika mana kunne da shegen karaɗi. Ki tsayamana abu abin a sannu idan ma ƙaryar ce ai 'Yar Magaji za ta faɗi.

"Wane irin bi-sannu Mati? Ai fa magana ta riga ta ƙare, Nene dai ciki gare ta, maganar ganin jini kuma wanann a bayyane yake, ko Magaji ka tambaya zai idar maka wannan zance. Lalle ne akwai Matan dake jini da ciki. "
           "Ke kuma Abule da kika haɗa Ni da Maita  ina jin dai tsohonki shi ne Bazawari na? Dan haka bushiya dai ba zata wa Kunkuru gorin ƙafa ba , ko zaki mutu dai Nene ciki gare ta na wata biyu."

"Kai kuma yanzu ya rage naka sai ka dinga mata abinda take so. Ni kaga tafiya ta."

Muna zuwa...

No comments:

Post a Comment