Thursday, 18 January 2018

Kashe Fitila 3

*KASHE FITILA*💡 3

*Batul Mamman*💖

       

       *Tuna baya*

Da alamun gajiya ya shigo gidan yana daga kafa da kyar. Baaba ce ta fara ganinsa ta taso da sauri.
"Yaya Awaisu an dace?"

Girgiza mata kai yayi a hankali zuciyarsa a cunkushe da bakinciki.

"To kada ka damu, rabon mutum komai nisan lokaci zai zo gareshi. Ka wuce dakina abincinka yana can"

Cikin sanyin jiki ya wuce ta bishi da kallo. Sai da ta ga fitowarsa da kwanon abincin ta mayar da hankalinta ga Maamu da take zaune tsakiyar matan Harisu guda biyu tana tayasu tsinkar zogale.

Dan daure fuska tayi cikin wasa tace "Kina kallon dana ya dawo ko sannu balle ki tambayeshi yadda akayi?"

Maamu murmushi tayi "tunda kina kusa meye nawa a ciki. Da dai bakya nan sai nayi muku kara"

Baaba ta hau mita ita Maamu bata kyauta mata ba. Matan Harisu suka sa dariyar rigimar surukansu.

Da suka gama Maamu ta tashi ta shige dakinta ta dan turo kofar. Hawaye ne ya taho mata ta sanya habar zaninta ta goge. Tun dawowar Awaisu tana ganin yanayinsa zuciyarta ta karye. Daurewa kawai ta rinka yi tana yaken dole. Shekara biyu kenan yana neman aiki har yanzu shiru. Ita kam Allah Ya sani ta kure matakin jin kunyar Baaba Hure da Harisu. Wanda ya kawota gidan ya jima da rasuwa gashi nauyinsu ya dawo wuyan dansa.

Lokacin da ta auri Mal Sa'adu Abali da danta na auren fari Awaisu tazo. Shekararsa biyu mahaifinsa ya rasu. Yana da shekara hudu ta hadu da Malam har sukayi aure. Taso mayar da shi wurin dangin mahaifinsa amma sam Malam yaki yarda yace bai ga amfanin auren mace kuma a kyamaci 'ya'yanta na wani gida ba. Zaman lafiya suka yi sosai da Baaba Hure. Ita Baaba mutuniyar Katsina ce. Cirani ya kawo iyayenta garin shiyasa ta tashi da iya yarensu. Amma duk da haka tana Hausa da 'yan uwanta. Malam da Maamu wadda ainihin sunanta Safara'u duk 'yan Fika ne, yaren Bolanci sukeyi. Kuma haka duka gidan har yara da shi suke tashi sai dai suna Hausa kadan kadan saboda cudanya da Hausawan cikin gari.

Baaba Hure yaranta hudu. Baraka, Harisu, Ummukulsum da autarsu Zakiyya. Mace ce mai kyaun hali da sanin ya kamata. Sannan mai jajircewa wurin tarbiyar yara. Domin yaran sunfi tsoronta akan Maamu mai sanyi. Ita dai barta da yawan murmushi ko da ranta ya baci.

Haka suke zamansu gwanin sha'awa. Malam ya sanya Awaisu a makaranta Harisu ne yake rakashi  domin autarsu ma ta girmi Awaisu da shekara shida.

Yana aji biyu a sakandire Malam Sa'adu ya rasu. Maamu ta shiga tashin hankali saboda bata haihu ba a gidan tana gudun su bukaci ta tashi bayan an raba gado. Sanin cewa yanzu gidansu ko ta koma babu inda zata zauna saboda yayyenta duk sunyi aure da matansu a cikin gidan iyayensu yasa Baaba Hure tace ta cigaba da zama dasu tamkar gidanta. Karatun Awaisu kuma 'yar buga bugar da Harisu yake yi da nata jarin suka hada suna biya masa kudin makaranta.

A haka ya kammala ya fara shirin jami'a. Maamu ta sayar da gonarta ta biya masa kudin ya tafi Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) ta Bauchi inda ya karanci Banking and Finance.
Lokacin nauyi ya fara yiwa Harisu yawa ya soma tara yara.

A haka dai da karume karume suka rinka tallafawa har ya gama da sakamako mai kyau. Ga shakuwa tsakanin 'ya'yan gidan wanda bai sani ba bazai taba gane cewa Awaisu ba dan Malam bane.

A halin yanzu aiki yake nema ruwa a jallo abu ya gagara. Maamu kullum burinta ya sami abinda suma zasu gwadawa Baaba Hure da zuri'arta karamci ba don su biyasu ba. Sai don kawai ta nuna musu cewa bata taba manta alkhairinsu ba gareta.

Harisu ya kara aure iyali suna ta karuwa. Ya ciyar da dolensa ya ciyar da ita da danta. Wannan yasa take jin babu dadi.

*****
Bayan kwana biyu Harisu yaje Kano saro kaya a Kantin kwari kamar yadda ya saba duk karshen wata. Sunansa yaji an ambata ya juya yana neman mai kiran.

Murmushi ya saki tare da sassarfa wurin karasawa wurin wani mai shago suna dariya tare da rungume juna

"Harisu Abali"

"Saminun Kano"

Sake rungume juna sukayi sannan Saminu ya ja hannunsa suka shiga cikin shagon atamfofi. Lemo mai sanyi yasa aka kawo masa sannan ya bayar da kudi a siyo musu abinci.

"Ikon Allah, ashe rai kan ga rai" cewar Saminu yana kara kallon abokinsa.

"Ga zahiri dai, sama da shekara biyar sai yau Allah Yayi ikonsa"

Hira sukayi sosai ta yaushe gamo. Saminu yayi zaman Fika inda suka saba sosai da Harisu. Daga baya ya dawo garinsu Kano ya cigaba da kasuwancinsa. A hirar yake tambayarsa kaninsa ya fada masa ai har ya gama jami'a.

"Aiki fa?"

"Nan fa daya, yanzu ma tare muka zo zai fara tayani kasuwanci kawai kafin aikin ya samu. Yanzu ma yana Wambai wurin masu robobi"

Harisu da Saminu sun sha hira  sannan suka yi sallama da alkawarin haduwa washegari kafin su koma Fika.

****

Washegari kafin azahar sun isa shagon Saminu yi masa sallama. Yana ta tsokanar Awaisu an girma an dena kiran Yaya da an taba shi. Ya hada musu 'yar tsaraba daidai misali sannan ya ja Harisu gefe.

"Mutumina nayi maka karambani fa, jiya bayan rabuwarmu naje gidan wani tsohon dan kwangila da nake sayar wa shadda"

"Kana nan da shige shigen ka mutumina" Harisu ya fada yana murmushi.

"Me za'a fasa..yanzu dai mu bar wannan zance. Cikin hira nayi masa bayanin ina da kani da ya gama karatu yana neman aiki. Sai dai anyi rashin sa'a bansan me ya karanta ba. Shiyasa bayanin nawa bai cika ba"

Farinciki sosai ya bayyana a fuskar Harisu
" da gaske kake?"

Murmushi yayi ganin abokin nasa yaji dadi "yanzu dai yace sati mai zuwa zashi Abuja wurin wani kusar gwamnati. Shine yace idan zai yiwu Awaisu ya same shi a can ranar alhamis"

Kati ya dauko mai dauke da sunan mutumin da nambar wayarsa ya mika masa.

"Gashi Allah Yasa a dace. Idan yaje sai ya fada masa cewa shine kanin Saminu Zawachiki"

Harisu ya rike hannuwansa ya ma rasa kalmar godiya "idan munje zaka ce. Ai dole na rakashi. Allah Ya baka ladan zumunci."

Yafito Awaisu yayi da hannu ya matso kusa dasu ya fada masa halaccin da Saminu yayi musu. Shima godiyar yake yi kamar zasu ari baki su biyun.

No comments:

Post a Comment