Thursday, 18 January 2018

Gidan Mati 8

*GIDAN MATI*

BY BINGEL FULANI & RUFAIDA OMAR

KASHI NA TAKWAS

Kamar wasa cikin Fad'ime ya tabbata, Inna  har Asibitin K'auyen ta mik'a ta tare da Abule da Nene wadanda suka tik'e akan sai sun bisu sun ji da kunnuwansu. Itama Innar ba ta yi gigin hanasu ba don ta fi so su ji abinda zai hana su bacci.
  Ranar kam sun riga su yin gaba, zagi da tsinuwa ba irin wanda Fad'ime da Inna basu sha ba.
   Tun daga wannan lokacin kuma sai sabon tashin hankali da makirci ya k'ara ɓallewa a gidan. Akwai ranar da Nene ta shigo da Kuliya cikin gidan, sanin cewa Faɗime ba ta so. Hakanan ta lallaɓa ta  d'ora mata ita bisa gadonta tana cikin barci. Allah ne ya tsare da kwallayenta na jere basu zubo bisanta ba, saboda yadda ta dinga razana tana bige-bige a ɗakin. Ƙarshe dai Inna ta cece ta  da fitsari ya fiddo ta, ta juyo motsi ɓarin Faɗimen. Shi kuwa Mati yana can ya saki gañɗa ɗakin Abule. Sai washegari ne  Inna  ta sanar masa, karshe dai ta yi maganin abin da cewa duk wacce ta k'ara kawo wani Abu gidan ko da Ɓera  ne, ko ta jefi Faɗime ko Mati da bak'ar magana to a bakin aurenta. Da wannan aka samu bakinsu ya rufu suka koma rara  gefe, ƙarshe dai Nene ta tattara ta tafi wani ƙauye bikin kanwar kishiyar matar babanta.

  Inna  zaune gefen Fad'ime tana lalla6ata  ta samu ta ci kwad'on Zogalen da ta had'amata, ita kuwa Abule tana tankad'e Garin Tuwo tana wak'e-wak'en habaici. Fitowar Nene daga bayan gida ya sanya suka bita da kallo. Tayi daurin k'irji da tsohon zanin da ta ci 'yanmatancinta da shi duk a huje, k'asan duk ya rarake har idan ka zura hannu a 6uli guda zai ta6o mazaunanta. Fatarnan kallo daya za ka yi mishi kasan akwai nakiyayyar d'aud'a da bai kammala fita ba, jikinta  kuwa babu alamar ya wanku. Sai kyalli takeyi da nason datti da hamami dake tashi.
  "Ke jik'ar Maduga, wai wankan da ruwan Taɓo ki ka yi shi ne?" Cewar Inna.
Juyowa ta yi ta mata murmushi, sai kuma ta yi gaba tana murzo wata naɗaɗɗiyar dauɗa a wuyanta.
"Ah'ah Nene magana fa nake miki." Fasa ɗaga labulen kabar ta ta yi ta juyo tana kallon Innar, sai kuma ta haɗe mata hannuwa biyu tana roko alamun ta kyale ta.

"Uhm! Sabon salo, wai gemu a kafaɗa, halan da kika je bikin rashin magana kika koyo? To ai gaba ta kai mu, tuntub'en me carbi" Inna ta faɗa tana riƙe hab'a.

         Ganin haka ya sa Abule  ture tankaɗen gefe, ta mike zuwa dakin Nene.
Da shigarta ta same ta tsaye tana jan Jagira a girarta me kama da ta Tunku. Ai sai ta yi turus! Da mamaki tana ƙare mata kallo daga ƙasa zuwa sama. Ta sha Atamfa koriya fatau, da dinkin rigarta irin na Lema, wani abin mamakin har kallabin irin na atamfar ne, ba wai wari da wari ba. Kwalliya dai irin wacce ko da tana Amarya ba ta taɓa yinta ba. Sai ƙamshin man kadanya ke tashi da ta mulkawa jikinta. 
"Wannan kallon fa? Ban fa san irin kakannin ki ba?" Ta faɗa tana kaɗawa Abule hannu ganin yarda ta ƙame.
"A'a mamaki kawai nake, tunanina  ko dai ƙanwar Nene aka  musaya mana.
"Uhm! Kibar mamaki, kawai nasihar da Innata tamin kan zaman duniya da ƙiyama nake ta tunanowa yau."
"Anya kuwa Nene? Ke din ce kike tuna wanda ya mutu? Abokin kuka ai ba a ɓoyemasa mutuwa. Ki faɗamin abinda ya faru dake kika saki makaman haka? Ko duk tsoron kar Innar Mati  ta kora ki gida ne?"
Ai sai ta gundumo ashar tana me ture ɗaurin kallabin da ta dade tana murd'ashi dan ya yi kyau gefe. "Ni wallahi har kin ɓatamin rai, tsohuwar banzar can zan ji tsoro? To Talle Bodara ce ta ba ni maganin Ɓari, sharuɗɗan cikar maganin shi ne ko daka Ni Uwar Miji za ta yi kar na sake  na tanka ta. Kin ganshi a bakin Masai ake barbaɗashi."
Ta karashe gami da bankad'a k'asan katifarta, wani k'ulli ta fiddo a bak'ar leda ta nunamata.
Abule ta washe baki don tsabar farinciki. Ganin babu damar ihu ya sanya ta kaiwa Nene runguma sai dai tun kan ta k'ara sa had'a jikinta da na ta ta yi baya da sauri tsabar tashin da Nene ke yi kamar mai warin k'ashi.
  "Dagaske ki ke yi?"
Nene ta ta6e bakinta.
"Ni idan na fad'i abu na fi son ki yarda, zan miki k'arya ne? Nan da ki ke ganina ba ta wasa bace ba. Bari ki gani, wuyarta dai Fad'ime ta tsugunna saman Masai, ko kwad'o ne a cikinta sai ya fad'o.
  Jin haka suka saki shewa gami da cafkewa, sai kuma da sauri suka rufe baki.
"Um kinga bari na je kafin wannan Tsohowar karuwar birnin ta ankara."
Dariya Nene ta yi.
"Ai mukam Allah Ya had'amu da suruka."
  Suka dara sannan Abule ta fice.
      
      ***
  Shiru-shiru ciki zai zube anjima, gobe, bai zube ba. Ko ciwon kai Fad'ime ba ta yi ba ballantana a kai ga ciki.
  Ganin haka Abule ta yanke gwada ta ta sa'ar ko za'a dace. Nene ta ba ta goyon baya d'ari bisa d'ari, da wannan ta shirya tafiyar kwana daya da sunan ziyartar jikar abokiyar kakarta.
  Dawowarta akayi sa'a babu kowa sai Nene a gidan da ke faman zazzaga bala'i ta katanga tare da Delu wai Akuyar Delun ta shigo ta cinyemata shanyar da ta yi ta k'anzo.
  Ganin Abule ba k'aramin dadi ta ji ba, itace har da rungumarta tana tsalle, da ace akwai mutane a gidan da sun sha mamaki.
Bayan sun k'ule a d'akin Abule ne ta hau bata labarin abinda ta samo.
  "Ba k'aramar wuya na sha ba in fad'amaki. Ban ta6a rawar 'yan bori ba amma shege la'antaccen bokannan sai da ya sanyani yi. Amma tunda kwalliya za ta biya kud'in sabulu da sauk'i. Bari ki gani."
Ta ɓalle ɓarin zaninta ta fiddo k'ullin magani har biyu ta nunawa Nene.
  "Ya ce na kwa6a lalle da garin na d'aurawa Inna a k'afa don rufe bakinta. Shi kuma wannan."
Ta nuna d'ayan,
"A had'a Lemon Zobarodo a sanyawa Fad'ime a ciki ta shanye."
  Shiru ya biyo baya kafin Nene ta jinjina kai.
"Tabd'ijam! Aiki ja! Yanzu banda abinki ina mu ina iya haka? Ni kinga banda kwaɗa zobo da kuli ba abinda na sani kansa, sai yau da na ji ana lemonsa, kema  kuma na san duk sammak'al. Inna kuwa ba ta yanda za ta amince waninmu ya d'auramata lalle. Ina mafita?"

Muna zuwa

No comments:

Post a Comment