*GIDAN MATI*
©ƁINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
KASHI NA BAKWAI
"Maigidana Randar Zuciyata, Idan ka fita kaje shagon Bakari Mai Ashana ka ce a baka Makilin da Burushi." Mati ya washe baki yana kallon kwalelen kanta da yasha zanen shuku yana ta ƙamshin Karkar.
"Wani sabon Abinci ne muka samu Amarya Timah?"
Ta yi far! Da ido "a'a kai dai jeka kawo za ka ga abinda zan maka da shi."
"To shi ke nan, bari na yi wanka sai na fita na siyomiki, kinsan tunda na sameki bana iya fita banyi wanka ba.
Ta yi murmushi "Yauwa kama tunamin abinda na ce zan nuna maka rannan, muje Makewayin na maka kaga sai na cuɗamaka baya ma."
Ta faɗa tana jawo hannunsa su fita. Fisgewa ya yi yana nuna mata waje da baki, sai kuma a hankali ya ce "Ki rufan asiri safiya ce fa? Kinsan su Nene sun tashi kar ya zama abinda zan kasa cin abinci yau."
"Haba Maigida Ni wallahi kanamin irin wannan sai in dinga ganinka ragon maza, ranar kwana nane fa, kuma baka shiga haƙƙin kowa ba dan ka shiga Makewayi da ni, Matarka ce ni, ba ta aro ba, ko ta titi, kuma ko su ka shiga Makewayi da su ba abinda zai dameni tunda na san aikin lada ne.
Ya zare ido yana dubanta "Da gaske aikin lada ne?"
"Kwarai kuwa, ai zaman Aure indai ba cuta lada gare shi."
"Au to muje, amman dan Allah saɗaf-saɗaf bana so Nene ko Abule su tsinkayi motsi na.
"To shi ke nan muje" Ta faɗa tana me yin gaba. Ruwa ta tuttula daga tulu a ɗan kwatashin wankan na su, ta sunkutu ta yi Banɗakin da shi, shi kuma Mati ya hau kewaye tsakar gidan, da dai yaji kamar babu motsi ko daga ɗakunansu, ai sai ya yi wuf! Ya faɗa Makewayin.
Abule ta yi miƙa ba salati ba rufe baki, ta miƙe tana mai riƙe mararta sakamakon fitsarin da ya rike mata ita. A hankali ta fito waje, ganin ba kowa ya sa ta tsugunna nan gefen kwatamin tsakar gidan ta tsiyaya abinta, ta wawwatsa ruwa ba ko cuɗawa ta miƙe, za ta koma ɗaki ta jiyo kamar kacaniya a Banɗaki, a zatonta Kajin maƙotane ke kacaniya, sanin da ta yi sunsha faɗawa wawakeken masansu azo a yi ta hayaniya ya sa ta zari sanda da sauri ta yi makewayin.
Sai dai fa turus! Ta yi tana sakin wani razanannen Ihu ganin Mati zaune a dutse daga shi sai gajeran wando, Amarya Timah kuma duƙe saitin hammatar Mati da wani ɗan ƙarfe a hannunta tana ta kwasar gashin hammatar tana hura masa iska, shi kuma yana dariya gami da fadin "Wai, ci gaba, daɗi wallah."
A firgice Faɗi ta yada ɗan ƙarfen saboda yadda ihun Abule ya kiɗimata, Abule kuwa da ƙyar ta jawo sauran numfashinta tana son daidai ta kanta, sai kuma ta ɗaga sanda ba tai wata-wata ba ta saukewa Faɗi ita a kafaɗarta.
"Sai na nakasaki baƙar mujiya me salon karuwai kawai, dan Ubanki ce miki akai nan bariki ne da zaki shiga wanka da Mijina, ko kuwa ce miki akai ni ɗin zan yarda."
Ta sake ɗagawa za ta rafka mata Mati ya riƙe sandan jiki na ɓari, "Karki kuma dukanta, zan fa rama mata, ke Abule ki fa fita idona da wanann jahilcin na ki, baki san aikin lada ba ne take yi? Ba na son sakarci fa." Ai sai ta yi baya tana kallon Mati sama da ƙasa, kafin kuma ta rangwaɗa guɗa.
"Ahl lalle Mati yanzu na san ka ɗauru tamau! a Minjaye, yanzu saboda wannan me zubin botoramin kake cewa zaka dake ni, Ni Abu? Da ka ce aikin Lada na ga dai kwanana ya shiga daga sanda aka kira assalatu."
"To na ji, yanzu dai wuce ki tafi haka ba zai ƙarawa faruwa ba."
"Bazan tafi ba, Ni fa idan ba jini na fidda mata ba bazan ji daidai ba."
"Haba Abu tawa, na ce kije dai, da daddare zaki ji saƙo."
Ta ɓallawa Faɗime harara dake dafe da kafaɗarta, ki sake gwadamana karuwanci gidan nan ki gani, wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi, shegiya da wani idonki kamar tsaka ta saka kwai."
Af! Abu mai sauki, wai kura ta zo gidan Maharbi, idan karuwancin ne ki gwada naki mana mu gani, ai wallahi babu wata me siffar Fanteka da ta isa ta hanani kula da Mijina. Aikin lada ne yanzu na fara, wanann sandar kuma bashi kika ci." Faɗi ta faɗa tana murguda baki.
Sanin Mati ba zai barta ta sake taɓa Faɗi ba, ya sa ta juya ɗakinta takaici fal ranta.
** ** **
Tun bayan da akayi cacar baki tsakanin Abule da Fad'ime gidan ya k'ara kacamewa. Tsakanin Abule da Nene sai ka rantse tun da can kansu a had'e yake tsabar amincin da suka k'ulla na munafunci. Koda suna cikin habaice-habaicen su ne Fad'ime ta fito tsakar gidan nan za su ɓige da shewa suna watsamata bak'ak'en magana a fak'aice. Ko kallon inda suke Fad'ime ba ta yi balle su saka ran za ta tankamusu.
Ranar wata laraba wanda ya yi daidai da cikar Inna kwanaki goma sha shida a birni, Abule da Nene suna zaune a gaban d'akin Abulen suna k'us-k'us tare da Shafa makwafciyarsu. Shafa ke yi musu tallar magungunan gyara na mata kala-kala. Ta d'aga wani k'ullin gari tana fad'in.
"Kun ga wannan? Na rantse da daren farkona da jikan Lamid'o yana da masifar kyau. Ke wannan da ku ke gani sunansa 'Saki Matar Uba'."
Nene da ke soshe-soshenta ta dubi Abule suka yi wata iriyar shewa gami da cafkewa.
"Inda ranka ka sha kallo! Yo Allah na tuba idan kura na magani ta yiwa kanta mana!" Fad'in Abule.
"Atoh, taya ni gani! Wai Matar kwarto da tallar maganin mata." Nene ta cafke.
Jin haka ya sanya Shafa kallonsu a fusace kafin ta d'an kalli d'akin Fad'ime, ga dukkan alamu batasan ma me suke yi ba. Ta maido dubanta gare su cike da borin kunya ta ce.
"Oho dai, gwara ni akan ku, haka za ku k'arata a borori."
Ta hau tattara komatsanta a sadda suka yo mata ca! kowannensu da bak'ar maganar da yake yarfamata. A daidai nan kuma Faɗi ta fito daga ɗaki da gudu zuwa bakin makwararar tsakar gida ta hau sheƙa amai kamar ba gobe.
Nene ta miƙe ido waje tana tafa hannu, yayin da Abule ta dafe kirji tana duban Faɗi dake duƙe.
"Duka-Duka yau kwana nawane da Auren ni Nene? Taya ni lissafi Abule.
Abule ta hau kasafta yatsun hannunta, sai kuma ta zare ido waje.
"Duka-duka kwana goma sha bakwai kenan, kar dai da ruɓaɓɓan kwai aka shigo?"
"Oh ni Nene, wannan wace irin haɗama ce haka, ranar farko da rabon ciki kamar marainiyar Karya? Ke kuma maƙaryaciya kika cemin ba ai komai ba ranar jikin tagarsu kika kwana?"
Abule ta ɓalla mata harara, "tuna dai, ke kika cemin ranar da aka kawo ta jini take, koma dai menene ni ban yarda da wannan Salon ba, ban taɓajin cikin dake bayyana kansa daidai da lissafin zuwan Amarya ba. Sai dai idan da shi aka shi..." Nene ta yi Wuf! Ta rufemata baki jin sallama kamar ta Inna.
"Barta ta ƙarasa mana manyan Akuyoyi, ai na dade tsaye ina sauraronku, wanda ya gani dai shi ya ji kunya wai kallon fitsarin makaho. Idan ba ku da kuke cikin ƙauye, haihuwar ƙauye, renon ƙauye, auren ƙauye, ina na taɓa ganin ana laɓewa sabuwar Amarya? Kunyi asara wallahi Nene, matsa ni na duba 'yar mutane, shashashai masu wankin kai da ruwan daddawa, idan ma da cikin ta shigo sai me? Na ce sai ƙaƙa? Irin kune a jahannamar ma can ƙasan wailun kuke. Sannu 'yarnan, sannu."
Inna ta k'arashe tana mai k'arasawa ga Fad'ime wacce aman ya d'an lafawa.
Gefe guda ta ajiye akwatin kayanta, ta yaye gyalenta ta dora saman akwatin kafin ta tattare zaninta dinkin rafa siket. Ruwa ta zubo a buta gami da mik'omata.
"Tayani duba Abule, toh wallahi ba za ta saɓu ba bari Matin ya zo, ni ban yarda wannan cikin nasa bane, ga dukkan alamu dai mutum da abinsa ya zo, ai daman ni nasan za'a rina, angama yawon ta zubar an k'untso.."
"Ki ka k'ara magana a wajennan sai na nunamaki ni ce nan na isa da Mijinki don kuwa yana zuwa zan sanya ya sallamaki ga tsohonki."
Nene ta yi d'if ta ja hannun Abule wacce ranta ke ƙuna suka fad'a d'aka. Shafa kuma da ke gefe kunne waje, tayi saɗaɗa ta fice daga gidan.
"Mun shiga uku Abule, yanzu idan ta tabbata matarnan juna biyu gareta ya za mu yi?"
Fad'in Nene kenan yayinda gumi ke tsirfomata. Abule wacce ta rasa bakin magana tsabar bakin ciki da tashin hankali, sai a lokacin ta iya bud'e bakinta ta ce.
"Hum, ni na rasa ma abin cewa wallahi."
Sallamar Mati ce a gidan ta katse su, suka yi shiru suna sauraron yanda Inna ke gayamasa rashin lafiyar Fad'ime da kuma cewar Fad'imen na tunda ta zo ba ta ga Al'adarta ba.
Muna zuwa
No comments:
Post a Comment