*GIDAN MATI*
©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR
KASHI NA UKU
"To ai sai ki kauce daga samanmu tunda dai shegen baƙin cikinki ya jawo kinji abinda Tsohonki ke aikatawa a waje."
Mati ya faɗi yana hararar Abule da tayi tsaye hannu bisa ƙugu tana jinjina maganar 'Yar Magaji.
"Oho dai, daɗin ta Bazawari aka ce ba Ɓarawon Jakai ba."
Ta faɗa tana hararar Nene dake yatsine-yatsine.
.
"Kyale ta kinji Nene uwargidan Mati, muje na raka ki ɗakI ki kwanta, daga yau ko tsinke ban yarda kin ɗage a gidan nan ba, wanda ba zai iya gani ba yayi zuciya mu gani a ƙasa." Ya faɗa cike da lallami.
Ita ɗinma miƙewa tayi cike da kwarkwasa har da riƙe rigar Mati. Gab da zata ɗaga labulen kabar ta ne ta waigo ta kalli Abule fuskarta ɗauke da murmushin kaɗan kika gani.
Dogon tsaki itama taja tana hararar ɗakin bayan shigewarsu. "Wai Kura ce ta samu damar miƙe ƙafa, ayi dai mu gani, muna nan za ka zo kana min 'yar murya. Har yaushe ma akai daren?" Jin shiru ba su amsata ba sai tashin dariyarsu da take ji ne ya sata juyawa a fusace zuwa na ta ɗakin.
Kwana biyu gidan shiru daga uhumm sai hu'umm wai uwargulma tayi cikin shege. Duk san Abule na ta gane gaskiyar cikin Nene abun yaƙi yiwuwa. Sai ma barinta da takaicin arba da ledar Burodi da Tsire da take yi kullum safiya. Idan ma ta yi dakon hana ido barci dan a kasa da ita Mati baya shigowa gidan sai dare ya raba, kafin ta gama barcinta ya kaɗa na sa Jakan yayi gaba tsabar rashin gaskiya.
Sauri take ta isa gida, dan ta fara gwada maganin saka laulayin da Gwaggonta ta bata ta dinga shansa duk dare, bayan ta sanar mata da abinda ke faruwa a gidansu. Ta tsinkayi muryar Delu na kwaɗa mata kira.
Kamar ba za ta tsaya ba, sai dai taja tunga ganin Delun harda ɗan gudunta.
"Uhm! Tunda na taho nake Addu'ar Allah ya sa na ganki, dan kuwa ba za ai wannnn cin Amanar a gaba na ba."
Gabaɗaya ta mai da hankalinta kanta
"Me ya faru Delu? Na sanki baki maganar banza."
"Ke dai Allah ya raba mu da Miji mai ɗabi'ar hankaka. Mati na gani yanzun nan gun 'Yarbaiwa mai Fara ya sai har ta Naira Hansin wai Uwargida ke kwaɗayinta, baki ganta ba fal ledar..."
"Fara fa kika ce? Farar da tunkan muyi aure yake min alƙawarin cinta?" Ta tari numfashinta.
"Idan ƙarya nake miki wannan zance tsawar bana ta sauka gonar Malam Alkur'an."
"A'a me na jan masifa? Zai yi fin haka ko dan ya nunan shi Namiji ne kwandon zawo, barni da shi, yau ko zai mutu ba za ta ci Farar nan ita kaɗai ba. Ke har ke sai kin ɗanɗana, na gode miki Delu, bari na ƙarasa gidan.
Da sallamarta gidan ta yi jifa da kallabin kanta gefe, luma yatsunta ta yi cikin gashinta ta fara wargaza shi, kan kace mene wannan ta tada hankalin gashinta ya yi tsaitsaye tamkar gemun Mahaukaci da ya shekara ana jifansa. Nene dake gefe ana ƙoƙarin sai ta kai, sai gani tayi Abule ta zube tana wani nannaɗewa, doka ihun da zata yi sai ga shigowar Mati yana mai da aljihunsa baya. Ganin Nene jiki na ƙyama ya sashi yin wurin Abule yana salallami.
"Karka ƙaraso! Kana ƙarasowa idan muka fyauɗe ka sai ka dangana da Gyatumarka" Yaji murya na gargaɗinsa kamar ta Kuyangar Kutare.
Turus! Yayi ƙafafuwansa na rawa kafin kuma ya zube ƙasa yana kallon yarda Abule ke naɗewa bakinta na dilalar yawu.
"Kiyi haƙuri Abule wallahi bansan kina da larura ba."
Ya faɗa kamar zai fashe da kuka.
Taja majina.
"Kai! Ka iya bakinka, wanann ba lalura ba ce, kai ne ka kira mu da kanka da kake taɓa mana Goɗiya kana sa ta kuka."
Ta faɗa tana zare manyan jajayen idanuwanta.
"Ƙarya take min bantaɓa sa ta kuka ba, Nene shaida."
"Munafuki menene wannan a aljihunka na hagu?"
"Fa..fa ...fara ce."
"To wa ka siyo wa?"
"Abule mana, ita ce Amarya ta da bana iya motsi sai da ita."
"To bawa waccar ta kawo farar nan gabanmu, gargaɗin ƙarshe kuma ka kuskura ka ƙara kawo ko Dusa ce ba ka haɗa da Goɗiyarmu ba sai mun musanya mata yaron cikin da take ɗauke dashi da Kadangare."
"Ban..ban..gane ba..."
"Au! Dan fitsara ma baka San Goɗiyarmu na da cikin ka ba?"
"Na sani, ku yi hakuri. Ke Nene miƙa musu Farar mana."
Ya faɗa yana jefa mata kullin ledar dake ta kyallin mai .
Abule ta kalla idonta kamar zai faɗo dan tsoro, gani take kamar bakinta ma ya koma gefe, dan haka ta Yi baya cikin hawaye.
"Ba zan iya ba Mati."
"To kuwa zan fita na barki da su, ki miƙa musu ko za su tafi."
Ya faɗa da tsawa.
A ɗarare ta miƙa ledar gaban Abule dake naɗe, a guje ta juya zuwa ɗakin ta ta lafe bayan kaba tana hangen su.
Ƙatuwar Hamma Abule ta saki, kafin kuma ta ɓingere gefe maƙale da ledar farar ta. Akwai alamun Borin ya sauka.
*** **** ***
Muna zuwa
No comments:
Post a Comment