Thursday, 18 January 2018

Gidan Mati 10

GIDAN MATI

©BINGYEL FULANI & RUFAIDA OMAR

    BABI NA GOMA

Ihun Nene ya janyo hankalin mutan gidan, gaba daya suka fito har da Abule wacce ta gwaggwa6e a d'aka tana kwa6a lallen. Kan kace me tuni Delu ta gyara zamanta jikin garu tana lek'e, itama Shafa ba'a barta a baya ba wajen ganewa idonta. Mati a rude ya nufeta.
  "Nene, lafi..."
Kii! Ya ja burki sakamakon wari da k'arar sakin tusa da ya bugi kunnuwa da hancinsa. Inna ta sanya salati.
  "Me zan gani haka Nene? Wane irin shashanci ne haka ki wuce Makewayi mana" Nene dake ta kokarin danne mazaunanta da hannu ta daddage ta ja numfashi sama tana mai hade jikinta dan ta tsayar da gudawar, ganin kamar an kara kunnu ta ya sa ta sakin wani wawan ihun "Wallahi ba ta tsayawa, na shiga uku ruwan jikina zai k'are. Kai Mati! Kai mati zan mutu, za ta zuƙen jini" Ai sai ta zabura ta danna a guje zuwa karshen gidan abu na yoyo. Mati ya yi sauri ya bita ganin ta zube gun, "Nene, nene, jin shiru ya sa shi toshe hanci yana jijjagata, sai kuma ya dago a tsorace yana duban Inna.
  "Kamar fa ba ta numfashi Inna"  "kai kauce nan, wane irin ba ta numfashi matsa ni ka ga na ba ta fastu aidi (First Aid)shashasha ko dabarun lafiya baka iya ba dake kanka ya cika da gashin jakai."  "Um Inna yanzu dai bata ba'a ake ba ki duba ta kiga ni Aradun Allah Inna ba ta motsi"
Inna ta dan na masa harara, sai kuma ta hau karewa Nene dake yashe kallo, ganin har yanzu Abun na tuttulowa daga jikinta ya sa ta kallo Mati "Tunda dai kai ne Mijinta matso kusa daidai bakinta ka lalubo harshenta ka gantsara mata cizo, shi ne zai sa ta farfadowa yanzu" Mati ya kalli Inna da ta kauda kai gefe tana jijjiga kafa kamar ba ita ta fadi wannan zance ba, ya waiga ga Abule dake matsar kwalla, ya dora idonsa kan su Delu dake bisa katanga, ai sai ya hau girgiza kai yana mai sharce gumi "Bazan iya ba! Kwarankwatsa dubu Inna wannan zalunci ne, ya zan ciji marar lafiya. Kuma sannan wannan ai Yahudanci ne." ai sai inna ta zabga salati tana mai fashewa da kuka Mati ya ce mata Azzaluma, kafin kuma ta share hawayen tana mai watsa ma masa dakuwa "To ka tsaya jahilci Nenen ta mutu, numfashin mutum na daukewa da minti goma idan bai samu taimakon gaggawa ba yake mutuwa"
  Jin haka ya sa Mati yin wurin Nene da sauri yana lalumar bakinta. Da dai ya zakulo harshen ai sai ya gatsashi da karfi. Baya ya yi yana ganin Nene ta yi wani irin cilla kafa. Tana fadi a hankali " Na mutu Mati" cikin magagi. Abule ta ƙara sautin kukanta "Inna dan Allah mu kai ta gun kula da lafiyan da kika kai Faɗime kwanaki"  Mati ya kalle ta, sai kuma ya yi waje da sauri. Ba daɗewa sai ga shi da mai Baro. Abule ta taya shi kama Nene aka dora ta bisansa. Suka ɗunguma Asibitin ƙauye.
   Bayan dube-duben da likitan ya yi sakamako ya fita. Nene dai banda Maleria ba abinda ke damunta. Likita duk tambayoyin da ya yi sun tabbata ba abinda ta ci na ɓata ciki tunda dai abincinsu guda ne. Dan haka ya daura ma karin ruwa ya rubutawa Mati O.R.S  da Napkin na manya aje a siyo mata. Ta kuma dinga daura napkin din duk bayan sa'a biyu. Karshe ya sallemusu da cewar su je Binni a duba ta da kyau shi kam iya na sa ke nan. Da komawarsu  gida Abule ta yi wuf! Ta fada ɗakin Nene tana sakayo kaba. Kallonta take cike da tausayi ganin harta tsotse rana guda.
  "Ni Nene anya ba maganin fadi kika sha ba? Na ganta sumul fa" Nene dake ji da yoyon kashinta ta mike a hankali  jiki na rawa" Shi ne wlh a randa na tadda shi a bude na sha,  na shiga musanyamin ta yi bakar muguwa wayyo ni. Mene makarin ki taimake ni Abule" Abule ta dafe kirji ido warwaje "Lalle dara ta ci gida Nene! Makarin da wuya Nene, ba za mu iya ba, sai kuma rushe da kuka."
  Nene ta yi ruf da ciki tana numfarfashi.
"Ki fad'amin Abule, ko menene shi zan iya."
  Jin haka Abule ta fyace majina ta soma magana.

No comments:

Post a Comment