*GIDAN MATI*
©BINGEL MITA & RUFAIDA OMAR
KASHI NA FARKO
Buguzum-buguzum ta sanyo kai cikin gidan tana wak'a.
"Ahayye iye nana..."
D'if ta dakata gami da sakin baki adalilin abinda ta hango a tsakar gidannasu.
Maigidansu Mati a k'ofar d'akin kishiyarta Abulle zaune su na hira da dariya. Ganinta ya sanya Mati yin tsuru da idanu yayin da ita kuwa Abulle ta washe baki, cike da dabara ta fiddo takardar naman da ta 6oye a bayanta ta warware ta d'auki tsoka d'ayan da ya rage ta jefa a baki ta na tauna gami da fad'in.
"Maigida kana burgeni, kana kawomin irin wanda na ke so."
Mati ya watsamata kallon muguwar mace, shaf a tunaninsa dagaske ta yarr da takardar tsiren, ashe makirar abinda ta shiryamasa kenan. Ya numfasa gami da share zufa ya na duban Nene batare da ya ce uffan ba.
Nene wacce zuciyarta ta gama kaiwa bango ta fisge mayafin kanta ta had'iye miyan da ya taru a bakinta tsabar na ranta ya biya ta ci d'amara ta hau tafa hannu.
"Allah na godemaKa da ka nunamin abinda ke faruwa a bayan idona! Ashe daman cuta ta ake yi ana dawowa idan bana nan? To yau dubunku ta cika Mati, yau sai an bambance tsakanin aya da tsak'uwa!"
Jin haka ya sanya Mati mik'ewa ya hau fad'an k'arfin hali da borin kunya.
"Ke ya isa! Yimin shiru dak'ik'iya kawai! Kin shigo gida ba sallama ba komai sai wak'en banza sannan ba ki tsaya kin ji dalilin dawowata ba yanzu kishi zai kaiki ya baro ki!"
Kafin Nene ta samu bakin magana, Abulle ta saki wata dariya irin ta wadanda duniya ta yiwa dadi.
"Kai namiji, namiji akace buhun k'aya. Sannunka munafuki, inace mun fi awanni biyu tare? Duk dai abinda za'ayi sai dai a yi don ba na tsoron kowace mai yanayin kul6a, miji ne mun yi aurenmu na soyayya muna zaune lafiya yana kawomin kayan mak'ulashe koda kuwa ba kwana na ba, sai a mutu!"
Da jin haka Nene ta zabura ta yi kanta ta na faman surfa ruwan ashariya.
"Yau sai na nakasa ki tsohuwar bazawara mai bin maza, saidai wannan tsohon gurgun ya k'ara haifar wata."
Ai sai su ka shiga kokawa, Nene ta daddage ta ba ta kyakkyawan cizo a mamanta wanda ya ke fata ce kawai. Wani ihu Abulle ta saki gami da fad'in.
"Kan uban can!" Ta cafki jan gashin kan Nene mai kama da gemun ɗan Bunsuru ta hau ja da k'arfi, ta kuwa shiga ihu har zaninta na fad'uwa sai ga ta zirr babu ko d'an bante. Mati ya tafi da gudu ya d'auki zanin ya na kokarin suturceta ganin magulmatan makwaftansu wato Gidan Delu da Gidan Shafa har sun soma lek'e ta Katanga.
"Menene haka? Ke Abulle don iyayenki sakarta!"
Wani turi da Abulle ta yiwa Nene sai kuwa ta jefata jikin Mati su ka yi kyakkyawan zubewa a k'asa abinka da siririn mutum. Da sauri Nene ta mik'e ta suturta jikinta ta na huci.
"Shegiya mai kalar mayu zan yi maganinki a gidannan, za ki san kin shigo gidan Nene."
Wani banzan harara Abulle ta watsamata sa'ilin da ta ke gyara zaman rigarta.
"Yanzu aka fara tashin hankula a gidannan muddin ba za ki fita a harkata ba. Mace ba ta ajiye komai ba sai ta ci ta yasar da k'aton kashi a masai! Gwara ni, tunda ko ba komai na yi 6ari an ga shaida!"
Nene ba ta jira komai ba ta nufi wajen girkinsu ta rarumo ta6arya ta taho a guje, ai Abulle na ganin haka ta fad'a d'akinta, ga shi ta kasa d'aga labulen kaban k'ofar d'akin hakanan kawai ta turo kyauren.
Nene ta tsaya ta na huci ganin Mati ya sha gabanta.
"Shegiya kai, ashe ke 'yar iskar k'arya ce, yo ki tsaya mana idan ban nakastaki ba anan."
"Haba Nene, ya isa hakanan, muje daga ciki ki ji."
Fad'in Mati hankali a tashe don shi har ya rasa ma yanda zaiyi ga makwafta 'yan gulma na kallo.
"Haba ke kuwa Nene, ki yi hakuri mana."
Fad'in Delu kenan cike sa tsegumi.
Wani banzan kallo Nene ta watsamata, sai lokacin ta lura da tarin magulmatan makwaftansu da ke lek'e.
"Kai! Allah Ya tsaremu da munafukai, mutane ba su ajiye komai ba banda munafunci da gulma, dadin abin dai mijina bai ta6a jibgata ba kuma bai ta6a haikewa wata ba."
Delu wacce tasan ita miji ke jibga ta ja tsaki ta ce.
"Oho dai! Duk acikin so ne." Daganan ta bar lek'en tare da yanmatan yaranta uku. Ita Shafa salin alin ta sauka ba ta ce uffan ba, to ina bakin magana tunda tasan da gaske mijinta kwarto ne na a kwantanta.
Dakyar dai Mati ya kashe rigimar tare da alk'awarin zai kawomata na ta k'unshin tsiren. Abinka da kwad'ayyiya kamar Asma'u a gari, ba musu ta hak'ura.
*** *** ***
Abulle ta ta6e baki.
Mati bai ko kula ba ya ci gaba da maganarsa.
"Sanin kanki ne dai Inna ba ta damu da zuwa k'auyen nan ba tunda Baban su Ladiyo ya d'and'ana mata zaman birni, yanzu kuma musamman don ni za ta zo ayi zumunci. Don Allah Abulle, ke ce k'arama, ke ce kuma ba ta sani ba, ki taimaka ku zauna lafiya har ta tafi. Sannan inda hali inason ayi wani abu."
"Menene shi?"
Ta fad'i da sauri.
Ya yi shiru sai kuma ya numfasa ya sassauta murya.
"K'aryar ciki."
Gaba daya ta zaro idanu ta na dubansa. Ta murza bajajjajen hancinta.
"Yi min gwari-gwari dai."
Ya hau bayani.
"Inna ta sanarmin cewa muddin ta tarar kema ba ki da ciki to lallai za'a samu matsala don kuwa sai na sake ki na yi wani auren. Ni kuma kinsan dai ina sonki ina son zama da ke, don.."
"Tsaya tsaya Mati, shi ke nan wannan abu mai sauk'i ne zan yi, sai dai menene ribar? Wace kyautar bajintar za ka samu bayan hakan don nasan halinka, ba ka aikin banza."
Ya yi 'yar dariya ya shafi sumarsa.
"Kai kai Abu tawa ta kaina, kina da saurin fahimta kam. To bari ki ji, akwai wata tafkekiyar gona ta Inna da kuma gida da ta ke bayar da haya ana biyanta balas duk karshen wata, ba yanda ban yi ba akan ta bani gonar ta k'i, to ta tabbatarmin za ta bani har da k'arin gidan nan ya zama mallakin jikanta."
Abulle ai sai ta hau tsallen murna da sakin gud'a.
Mati ya hau rufemata baki a tsorace.
"Ke ki rufamin asiri kada waccan ta ji."
Tunanowa da Nene da ta yi ne yasa ta saurin sai ta kanta.
FIKRA WRITERS ASSOCIATION
Labarin nan ba karamin dadi yayi ba gaskiya komai yaji normal sisters Allah ya kara basira da fikra gaskiya kun ciri tuta ta ko wani fanni
ReplyDelete