[8/14, 9:37 PM] Salma: FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
💌 SAK'ON NA MASOYA NE🤗
Ina mai neman afuwa kan jinkiri da aka samu na cigaban wanga littafi, Sidiya mai yawan hidama ce, da fatan za a cigaba da mata uzuri. Ina Godiya da kulawar ku. Sidiya ce ke mu ku fata na alkhairi🤝
WAIWAYE
Daga cikin Masallaci aka fara abinda ya had’a jama’a a wannan masarauta, wato d’aurin aure, in da aka umarci waliyin Ango da Amarya su matso kusa. Waziri ne ya fito daga 6angaran Sa’ayrasa, Fabarusa kuma Sarki Abdulrahaman ne ya nuna kan sa a matsayin waliyi.
Daga waje Khalil ne ke ta yiwa Yarima Barde hira, amma shi ina hankalinsa na ga Gimbiya K'amariyya, Allah Allah ya ke a shafa fatiha ya tafi garera don jin soyayyar ta ya ke har ransa, bare kuma yau gabar da ke tsakanin Masarautasu za ta kau, za su yi soyayyarsu a zahirance ba tare da wani shakku ba. Jin an shafa fatiha Yarima Barde ya tashi ya na mai fad’in.
‘’Alhamdulillah tunda an amra sai ku tashi mu tafi ko?’’
Har Khalil da Jafar sun tashi, tuni su ka tsaya cak jin marok’a na fad’in
‘’An d’aura auren *Yarima Abubakar BARDE* tare da *Gimbiya Fatima* akan sadaki (50000 CFA)"
Yarima Barde da sam bai lura da abinda su ka ji ba tsabagen hankalinsa ba ya wajan, a hasale ya kai kallonsa ga abokannasa ya na mai fad’in
‘’Me ku ke jira ne? Mu tafi, Allah Allah na ke na gana da Gimbiyata.’’
Su kuwa marok’a ba su fasa shela ba. Khalil ne yayi k’arfin hali ya ce
‘’Da ma kai ne Barde?’’
Cikin rashin fahimta Barde ya ce
‘’Ni ne wa?’’
‘’Angon da aka amrawa amren.’’
Jafar ya bashi amsa a tak’aice. Kai Yarima Barde ya girgiza cike da murmushin irin ban son rainin hankali fa. Khalil ya ce
‘’Saurara ka ji Barde’’
Nan kuwa muryar wani marok’i da ya zo giftawa ta dafda su ya doki kunnan Barde, fad’i ya ke
‘’An amra auren Yarima Abubakar Barde da Gimbiya Fatima....’’
Nan ya ya tsaya cak tamkar wanda aka zarewa rai, su kansu abokannasa sun girgiza kwaran gaske.
Daga cikin masallaci, ana gama d'aurin auren, inda kowa ya ke mamakin sauyin al’amura da aka samu, musammam jama’ar Sa'ayrasa, shi kuwa Aisar tunanin hanyar fita daga cikin jama’a yake, domin zuwa neman Bintu ba tare da Junaidu ya ankare ba. Bayin Sa'ayrasa ne d’auke da farantin goro da alawa, su ke bin kusirwa kusirwa in da suke mik’a farin tin jama’a na d'iba san ran su.
Bawan da ya zo kusurwar da su Aisar su ke, Aisar ya fara mik’awa, in da ya girgiza masa kai alamar ba ya buk'ata, har bawan zai wuce, nan idanun Aisar su ka sauka bisa yatsun bawan, me zai gani? Zobensa da ya bawa Bintu ne cikin yatsun na shi, bai ankara ba sai ji yayi Aisar ya damk’o hannunshi, a tsorace bawa ya saki farantin hannun sa dan ko shakka babu ya san tawagar shugaban k’asa ne gabansa.Hakan ya dawo da hankalinsu Junaidu da sauran ‘yan tawagar garesu. Aisar na mai duban idanun bawan ya furta
‘’Ina ka sami wagga zo6en? Menene dangantakarka da mai zo6en? Ina Bintu d’iyar bayi?’’
Babban gida kuwa 6angaran Jakadiya, Bintu na zaune tare da su Jakadiya sai ga Gimbiya K’amariyya ta shigo, ta yi kyau kwarai cikin jajayen kaya, ta d’aura alkyabba ruwan zuma bisa kayan, ga bayi nan biye da ita. Ta zo kar6ar mabudin wajan aje baki na musammam domin kar6ar Yarima Barde.
Ta na zaune ta na jiran Jakadiya ta shiga ciki dan d’auko mata mabud'in, su ka ji an shigo 6angaren Jakadiya an gud’a. Tuni hanjin cikin Bintu ya kad’a don kuwa ta san ta faru ta k’are an yiwa mai dami d’aya sata, aure dai an aura. Tuni ta fashe da kukan da dama ya tsaya k’asan mak’ogaran ta.
Jakadiya ta fito d’auke da mabud’i, yayinda Ladiyo ta shigo jiki na rawa, sai tafa hannu ta ke cikin salati da sallallami. Jakadiya ce ta tambaya ko lafiya, yayin da hankalin kowa ya koma gareta.
Cike da ladabi Ladiyo ta durk’usa gaban Jakadiya ta na mai fad’in
‘’Yau na ga lafiyar Allah Maigari gauro talaka da mata hud’u.’’
Cikin k’aguwa Gimbiya K’amariyya ta ce
‘’Me ya faru ne Ladiyo?’’
‘’Wato Allah shi taimaki Gimbiya, ji da gani dai ba ya k’arewa sai randa kurman bebe ya makance, Sarki Abdulraman na Fabarusa cike ya ke da abin mamaki, wani lamari sai shi.....’’
‘’Yo to wani abin mamaki? Ya ce ya fasa ne?’’
Jakadiya ta tambaya cikin rashin fahimta. Kana Ladiyo ta ce
‘’Eh to ya fa fasa be kuma fasa ba, da ya tashi yin bazata, sai ya amrawa d'ansa Barde Bintu.....’’
Hakan yayi daidai da ihun da Gimbiya K’amariyya ta kurma ta na mai zubewa k’asa sumammiya. Nan da nan aka yi kanta. Bintu kuwa yanda maganar ya doki kunnenta ta tabbatar ta zama kurma, don kuwa ba ta jin hayaniyar da ake gabanta
‘’Ya amra ma d’an sa Barde Bintu....’’
Maganar da ke ihu jikin kunnenta kenan.
®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE! (2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
1⃣
Tuni waje ya kaure da salati da salallamin bayi, Jakadiya ce ta sa aka yi maza aka shigar da K’amariyya daga cikin d’aki gudun gulman da ta san tabbas sai ta yad’u daga bakin bayin da ke wajan. Bintu kuwa ta ma kasa gane komai, kukan ta kawai ta ke, aure dai an d’aura mata, ko ta na so ko ba ta so tafiya ne dole a tafi da ita. Gashi a rasa wanda za a d’aura mata sai saurayin Gimbiya K’amariyya, Yerima Barde na Fabarusa! Hannu biyu Bintu ta d’aura bisa kan ta ta na mai fad’in
‘’Wayyo ni Bintu alk’iyama ta ta zo’’
Daga cik’in uwar d’aka, bayan an kori duka bayin da ke b’angaran Jakadiya, Hajja Kilishi da Inna Salti wanda Jakadiya ta aika Ladiyo da Kyallu su sheda ma su abun da ke faruwa ne su ka shigo d’aya na bin bayan d’aya, biye da su Gimbiya Binta ce, wacce ita ma labari tuni ya je mata.
Jakadiya ta umarci bayin da su ka taka mata baya su yi jiran ta waje. Bayan an watsa ma Gimbiya K’amariyya ruwa, da rokan Allah ta farfad’o ta na mai bin su da kallo kamar lokacin ta fara ganin fuskokinsu. Kanta bisa kan cinyar Inna Salti, Jakadiya zaune gaban ta sai kuma Gimbiya Binta wacce ta dad’e da gigicewa da jin lamarin da ya faru, in ban da kuka babu abinda ta ke don gani ta ke duk laifin Bintu ne ko shakka babu ita da uwarta ne su ka sa musu hannu wannan balk'in ya fad’a kan ‘yar uwarta.
Ko da idanun Gimbiya K’amariyya ya sauka kan Gimbiya Binta, ita ma d’in ta fashe da kuka don sai a sannan ne ta dawo cikin hayyacinta sosai. Cike da damuwa Hajja Kilishi ke tambayar
‘’Menene ne? Gide menene ke faruwa? Tun dazu fa nake tambayar ki Binta amma amsa ta gagara daga gareki, yanzu kuma mun samu ta farfad’o maimakon a sami sauki ina, kun maishe da gida kamar wajan makoki! Shin ba kwa gudun abinda zai je ya dawo? Kun fa san gidan ga cike yake da baki da kyar na sami hitowa daga cikin jama’a, ko rufa mana asiri ku sheda mana abun da ke faruwa.’’
Cikin kuka muryarta dak’yar ya ke fita, Gimbiya K’amariyya ta amsawa Hajja Kilishi, ta na mai fad’in
‘’Na shiga uku Hajja, Inna Salti na shiga uku, na d’au wuk’a na dab’a ma kaina, Allah Ya nuna min ikonSa, Barde…..Yarima Barde na Fabarusa……’’
Kuka ya ci k’arfinta, ta kasa k’arasawa sai shasshek’a ta ke. Cikin rashin fahimta Inna Salti ta ce
‘’Barde? Me ya faru da Barde na Fabarusa?’’
‘’Ni kam ta dad’a sa kai na cikin duhu, jakadiya wagga yarinya ba gamo ta yi ba kuwa?’’
Cewar Hajja Kilishi cike da damuwa.
‘’Yarima Barde da Didi masoya ne, shi ne dalilin ta na k’in amincewa ta auri sarkin Fabarusa wanda yake mahaifi a gareshi.’’
Gimbiya Binta ce ta amsa ma su.
‘’Kayya! Kai wagga lamari da me yayi kama! Kun ga irin ta ko? Gashi dai an cuci d’iyar mutane kin kuma cuci kanki K’amariyya, anyi gudun gara an tadda zago! Jakadiya dai ga irinta nan dai kin gani don kuwa wagga kulli ke da wagga d’iya ku ka kulla.’’
Fad’in Inna Salti ta na mai nuna matuk’ar b’acin rai.
Jakadiya da tunda aka fara maganar ta sha jinin jikin ta, jikinta ya yi sanyi kamar wacca aka tsunduma cikin ruwan sanyi cewa ta yi
‘’Uhum Allah shi ja da ran ki, yo to ni me zance? Ni ina naga ta ce wa? ‘’
Cikin kuka don kuwa idanunta sun rufe K’amariyya ta furta
‘’Don Allah ku taimaka a warware wanga lamari, don Mai Sama, kwarankwatsa zan iya rasa rayuwata, dan Allah ayi maza a shedawa takawa kafin na rasa raina, Ammu ki taimaka min…..’’
Kai Hajja Kilishi ta jinjina kafin ta ce
‘’Gide Takawa zai saurari wanga azzance kuwa Jakadiya? Yanzun ga ya na can wajan liyafar d’aurin amren nan......’’
Kafin Jakadiya ta amsa Gimbiya Binta ta yi saurin taran numfashin ta ta hanyar fad’in
‘’Ku taimaka tun kafin a makara, dan kuwa ba Sidi ba ko ni ma ina tara muddin ba a warware wanga
amre ba, ya d’iyar bayi za ta amri mutum kamar Barde, dan Allah Jakadiya ki sama mana mafita tun kan na had’iyi zuciya na mutu dan kuwa ciwon da na ke ji ya ma fi na Didi’’
‘’Makara kam an riga an makara, saidai fa a jira bayan komai ya lafa a yiwa Takawa magana watakil shi bai zai rasa dabara ba.’’
Cewar Hajja Kilishi yayin da tashi tsaye jiki sanyaye, tak’ara da fadin.
‘’Kunsan mu na da baki, duk abinda za ku yi kada ku manta da martabar Takawa, ku kula ku kame kanku kada ku jawo mana abun da zai halaka yankin ga gaba d'aya’’
Ta na gama Magana ta juya abun ta ta fice, ta bar Inna Salti tare da Jakadiya cikin al’ajabi. Gimbiya Kamariyya gani ta ke sam Hajja Kilishi ba ta damu ba saboda ita dama ba ta ta6a haihuwa ba shi ya sa sam ba ta damu da lamarinsu ba. Ita kuwa Gimbiya Binta abinda ya tsaya mata a rai bai wuce na ta na murnar raba Bintu da masoyin a Aisar, sai gashi ta zama matar wanda har ta gama rayuwar ta a doran k’asa ba za ta sami kamar shi ba, abun takaici ta yiwa yar uwarta asarar masoyi, duk akan wanda sam be ma san ta nayi ba.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
[8/14, 9:37 PM] Salma: ®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
2⃣
Daga cikin masallacin Sa’ayrasa, ko da bawa ya tsinci kansa gaban Aisar, hannunsa damke cikin na sa yayinda yake jero masa tambayar da shi kansa bai ta6a jin ko da makamancin sunan ba a matsayinsa na bawan barga da kwananan ya dawo cikin sawun bayin da ke kula da lambu. Zufa ne ya shiga keto masa, cikin kame-kame da in’ina ya ce
‘’Eye? Na’am lillahi warasulihi wanga zoben tsintarsa na ka yi, idan kuwa na yi karya aratta kashe ni….’’
Maimaikon Aisar ya saki bawa sai dad’a damke hannu bawa yayi. Cikin neman d’auki bawa ya kai dubansa ga sauran yan tawagar na shugaban k’asa ya na mai neman d’oki. Hakan yasa Junaidu tausaya ma bawan duk da ko shakka babu ya san zoben hannun bawa mallakin d’an uwansa ne. Kana ya na mai shiga tsakanin bawa da Aisar ta hanyar ciro hannun Aisar daga cikin na bawa yayinda yayiwa bawa nuni da ya ciro zoben, nan da nan bawa ya ciro zoben, ya mik'awa Junaidu kai durkushe ya na mai fad’in
‘’Tuba na ke, aradun Allah tsinta na kai, ku min rai……’’
Nan bawa ya fashe da kuka, wanda hakan ba k’aramin dad’a kular da Aisar ya yi ba, ji yake kamar ya shek’eshi har sai ya matso gaskiya daga bakin bawan.
‘’Ka ga ba kuka za ka yi ba, babu abun da zai ma muddin ka fad’a masa gaskiya, shin in aka sami wanga zoben?’’
Cewar Junaidu ya na mai kok’arin saka idanunsa cikin na Bawa don gano inda bawa ya dosa. Shi kuwa bawa ya gama rikicewa sai rantse rantse kawai yake, fad’i yake
‘’Tsinta na ka yi, kwankwasi tsinta na ka yi a lambu, aradu tsinta na ka yi.’’
Jin an furta
‘’Ko shakka babu gaskiya ya ka fad’i, don na shedi wanga bawa mai gaskiya ne.’’
Gaba d’aya hankalinsu ya koma ga mai maganar. Sanye ya yake cikin bakar jamfa wanda aka masa ado da bakin zare, idan ka d’auke rawaninsa da yake fari komai na jikinsa bak'i ya sanya, kai kace wani taron bakin ciki ya halarta, ko da shike a nasa 6angaran hakan ta ke. Kallo d’aya Aisar ya masa ya d’auke kai ya na fad’in
'’A matsayinka na wa za mu k’ar6i shedanka?’’
‘’A matsayinsa na Yarima Nuhun Sa’ayrsa ranka shi dad’e.’’
Fad’in bawan da ke tafe da Yarima Nuhu kenan, ganin idan ba a yi dagaske ba yanda ran Yarima Nuhu ya ke a dak’ule komai mai afkuwa ne. Jin haka Junaidu ya bawa Yarima Nuhu hannu suka gaisa haka sauran yan tawagar amma ban da Aisar wanda idan ransa yayi dubu ya 6aci, don haka a kusa ya ke. Sanin hakan ne ya sa Junaidu yin saurin yiwa Yarima Nuhu bayani, ya na mai nuna ma sa zoben. Ganin zoben da kuma jin wanda Aisar ya ke tambaya Yerima Nuhu ya san ko shakka babu Bintunsa ta arziki a ke nema, zoben nan shine zoben da ya kar6a daga hannunta ya wulgar. Wato wannan shi ne Aisar d’in da yake soyayya da Bintunsa….
Bawan nan dai da ke tafe da Yarima Nuhu ne cike da ladabi ya furta
‘’A hakik’anin gaskiya wanga bawa ada bawan barga ne, be dad’e da dawowa sahun bayinmu masu kula da lambu ba, saboda haka ina mai tabbatar maka ba zai san wagga d’iyar bayi da ku ke magana akai ba, dan yanda alama ya nuna ko shakka babu ta na daga cikin bayin cikin babban gida tun da har aka iya tsintar zoben hannunta cikin lambu, haka nima da na ke bawan kofar gabas, ba mai yiyuwa ba ne na santa, domin kuwa ba mu da wata alak’a da zai had’amu da bayin cikin babban gida’’
‘’Shin ina za mu sami wagga d’iya?’’
Aisar ya tambaya ya na mai fatan samin mafita daga bakin bawa. Nan take bawa ya masa alk’awarin tayashi cigiyar Bintu nan ba da dad’ewa ba, sannan su ka sallami wannan bawa da zoben Bintu ke gareshi. Yarima Nuhu ya shaida mu su abinda ya kawo shi gare su, wato sheda ma su ana buk’atar su d’akin taro. Ya na gama shaida mu su yayi gaba dan kuwa yanzun da ya gane Aisar shi an samrayin da ya kwace zuciyar Bintu ya fi ma sa d’aci akan auren da aka d’aurawa Bintu a yau, dan wannan ya san ba mai d’orewa ba ne musammam idan aka yi la'akari da wanda aka d’aura mata.
Dakyar Junaidu ya lalla6i Aisar, sai da ya masa tuni da ba fa su kad’ai ba ne, akwai manya cikinsu, sun zo d’aurin aure ne bisa wakilcin shugaban k’asa ba wai hakan nan bak’akatan su ka zo ba, sannan ya samu ya d’an shawo kansa, ta hanyar masa alk’awarin bayan komai ya lafa Junaidu da kansa zai tsaya har sai sun samo Bintu kafin su juya gida, ko da kuwa hakan ya na nufin raba tafiya da tawagar ta su. Da wannan su ka yi tattaki zuwa d’akin taro ba tare da sun bari manya daga cikinsu sun fahimci abinda ke faruwa ba.
Yarima Barde kuwa da dabara Yarima Jafar da Khalil su ka ja shi mota, gaba d’aya ya zame mu su tamkar mutum mutumi, ya d’auke mu su wuta. Cikin mota sai da su ka d’au kusan rabin awa babu wanda ya iya furta komai.
Dogarin Masarautar Fabarusa ya zo ya buga musu kofa, nan ya zube ya na mai sheda mu su umarnin Sarki Abdulrahman na a ma su iso gareshi.
‘’Su na cikin masallacin ne?’’
Yarima Jafar ya tambaya, in da Dogari ya ba shi amsa da
‘’A'a, sun wuce ga d’akin taron masarauta tunda jimawa, Yarima kad’ai ake tsimayi ranka shi dad’e.’’
‘’Mu na nan tafe.’’
Cewar Khalil, yayinda Dogari ya tashi da sauri ya na fad’in
‘’A iso lafiya.’’
Yarima Jafar na duban Yarima Barde ya ce
‘’Ka bawa zuciyarka hakuri mu amsa kiran Mai Martaba’’
Ko kallonsa be yi ba bare ma ya nuna alamar ya san da shi ake, kamar an aje dutse. Ganin haka Khali ya ce da Yarima Jafar.
‘’Ka san halin Barde a sama ya ke, ina zaifi mu lalla6a mu je a dai ga fuskarshi, in ya so sai mu nemi izinin tafiya ta hanyar ba da uzirinmu ga Mai Martaba.’’
Da wannan shawara su ka fito daga motar, amma Yarima Barde fitowa ta ma sa wuya, sai da Yarima Jafar ya ma sa tuni akan wanda ya sa a yi kiransa sannan ya fito cike da k’asaita, dama shi idan ransa ya 6aci nan fa sarautar ta sa ke bunk’asa. Ko da dogarawan da ke tsimayinsu su ka ga fitowarsa tuni su ka rufa musu baya, zuwa d’akin taro, kai kace Sarki Abdulrahman na Fabarusa ne da kansa ke tafe.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
: ®
✏📖
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!(2)
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
GARGA'DI
KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.
3⃣
Dakin taron ya cika fal da jama’a, tawagar Aisar da shigowar su ke nan, na su 6angaran na shugaban k’asa su ka zauna. Haka ma hakiman Sa’ayra da Fabarusa, Agadez, Diffa da sauran Hakiman yanki da sassa na jamhuriyar Nijar wajan su na musammam su ka zauna. Haka kuma yankin Sarakuna wanda Sarkin Sa’ayrasa mai gayya mai taro ya hakimce, kusa da shi kuma Sarkin Fabarusa ne zaune cikin aminci. Hakan ba k’aramin farantawa jama’a rai yayi ba, wai ashe dai akwai ranar k’arshen gaba tsakanin Sa’ayrasa da Fabarusa? Shin dama akwai rana irin ta yau da za a ga Sarakunan wanga yanki zaune cikin aminci?
Busa na alkgaita ke tashi daga waje, jama’ar Sa’ayrasa kwan su da kwarkwatar su sun yi dandazo cikin d’akin taro, murna gun su ba a cewa komai domin kuwa a yau yunwa zai kau a k’asar su. Ganin shigowar su Yarima Barde tuni dogarai su ka hau yiwa ango kirari. Shi kuwa Yarima Barde sam ba cikin hayyacin sa ya ke ba, amma in aka d’auke Yarima Jafar da Khalil wanda dama sun san halin da abokin na su ya ke ciki babu wanda zai kalle shi ya ce ya na cikin wani hali, sai dai ma ayi tsammanin tsabar sarauta da miskilanci ne yake d’ibar sa.
Sai kuma Mai martaba Sarki Abdulmalik na Fabarusa, wanda kallo d’aya ya yiwa d’an na sa Yarima Barde bayan ya kai gaisuwar sa ga Mai martaba Sarki Sule na Sa’ayrasa, ya gane halin da ya ke ciki, kasancewar wajan mahaifin na shi ya yo gadan kafiya, cijewa da kuma yin burus kamar be san abun da ke faruwa da shi ba, amma in aka tona cikin zuciyar su, Allah kad’ai ya san tafasar da ta ke. Murmushi Mahaifin na sa yayi, cikin ran sa kuwa yacewa ya yi
"d’an mu Abubakar, alkhairi ne mu ka kulla ma ka ba sharri ba, nan gaba za ka gode ma na kwaran gwaske’’
Ganin Yarima Barde durk'ushe gaban Sarki Sule, haka ma abokan na sa biyu, hannun su na dama dunkule suna mai jinjina ga Sarki Sule, fadawan Sa'ayrasa su ka amsa ma su da
"Jinjine dama lafiya alher, gaishe ka Yarima Badde, an gaishe ku samari"
Sarkin Sa’ayrasa kuwa cikin nuna ya amsa gaisuwar ta su shi ma ya dan daga na shi hannun daman a dunk'ule. Yarima Barde ya shiga ran sa saboda kamala da kwarji na sa, ji ya ke ina ma ina ma, ina sirikin na sa ne na gaske, da ya san haka Sarkin Fabarusa zai aikata, da ya bayar da d’iyar sa ko da kuwa ba a san ran ta ba ne.
Ko da Yarima Barde ya had’a ido da Mahaifin na sa, sai ya yi saurin saukar da na sa idanun. Duk wannan abun da ke faruwa a kan idanun yayan Barde, wato Yarima Sadauki na Fabarusa wanda tun da ya ji abun da mahaifin na su ya aikata bisa ga auran da ya d'aura ya k'ara jin tsanar Barde ya dad'u a kirjin sa. Domin kuwa shi ya kamata Sarki ya d'aurawa aure shi da ya ke babban d'an sa ba k'anin sa, hakan da yayi shi ya nuna k'arara Sarki Abdulraman ya fi kaunar Barde, ya kuma fi fifita shi akan Sadauki. Hakan ne kuma Yarima Sadauki ba zai lamun ta, dan ya san ba k'aramin girma aka zubar ma sa ba a idanun jama'a, dole kuma ya d'au Mataki. Idanun sa kan Barde, cike da tsana ya ke duban sa yayin da aka yiwa su Barde nuni ga na su wajan zaman, wato kusa da Yarima Sadauki da abokan sa su ka zauna.
Tun shigowar su Yarima Barde idanun Yarima Nuhu ke kan sa, ji yake kamar ya je ya sheda ma sa wacece Bintu in ya so kowa ma ya rasa. Haka ma Aisar wanda ya san burin Bintu na ganin Yarima Barde ko da sau d’aya ne a rayuwar ta, wai ta rasa wanda za ta kira mai kyawun duniya sai wanga buzu! Cewar Aisar cikin ran sa yayinda wani bakin kishi ya ta so ya mamaye ran sa, shi dai fatan sa Allah ya sa ya sami damar ganin Bintu tin ka a tafi da ita cikin bayin da za su raka gimbiya Binta Fabarusa, ko dan Yarima Barde dole ya d’auke ta, sam jinin su be had’u ba, dan haka Bintun shi ba za ta yiwa matar Barde bauta ba, ko da kuwa duka dukiyar sa za a buk’ata domin mallaka ma sa Bintu, a shirye ya ke ya rasa komai.
Bayan an sami nutsuwa ne aka bud’e taro da addua’a, sannan aka shiga abun da ya tara su a wajan. Su Yarima Jafar sun so su nemi izinin tafiya, amma hakan be samu ba, sai hakura su ka yi su ka zauna kamar gumaka, ba um ba um um, ga abokan Yarima Sadauki da shi kan shi Yarima Sadauki sai harbin iska su ke. Barde kam duk be san ana yi ba.
Sarkin fabarusa ne ya fara jawabi, ya mai nuna farin cikin sa na kulla aminta da auratayya wacce ta kawo k’arshen gaba tsakanin Masarautar ta su biyu. Bayan haka ya gabatar da takardar shedar sun bayar da bashin da masarautar Sa’ayrasa su ka buk’ata, ya kuma ce tun da an zama d’aya, sa iya biya a tsanake sannu a hankali ba tare da tashin hankali ba.
Nan waje ya kaure da ihu da sowa na jama’a, kowa na nuna jin dad’in sa da kuma alfahari da halin girma irin na sarkin Fabarusa. Dogarawan Fabarusa su ka shiga jera kirari ga Sarkin Su, fad'i su ke
"Lafiya Sarkin yakin Sarkin musulmi
Lafiya maida garin wani kango
Lafiya Barden mahadi
Lafiya Sukukun bakaka
Lafiya Darzaza amalen sarakuna
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya hana kangara
Lafiya Sakaka babban bako
Lafiya Bango madafar bayi
Lafiya hadarin kasa maganin mai kabido
Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Lafiya adali, lafiya salamun, salamun salamun"
Jikin sarkin Sa’ayrasa ba k’aramin sanyi yayi ba. Sai da waje ya lafa sannan Sarki Abdulraman ya k’are jawabin na sa da adduar zaman lafiya tsakanin Masarautar da kuma fatan Allah ya bawa shugaban k’asa lafiya.
Sai da sarkin Sa’ayrasa ya sa hannu a takardar ta hanyar amfani da hatimin masarautar ta sa, yayi na sa jawabin na nuna farin ciki da godiya ga masarautar Fabarusa, sannan kuma ya yaba da halin dattako na Sarki Abdulrahman dan har ga Allah ya bashi mamaki matuk’a. ya k’are jawabin na sa tare da fatan alkhairi tsakanin Masarautar biyu. Cikin ran sa ya na alhinin aurar da d’iyar bayin da yayi maimakon d’iyar sa, maimakon ya kawo k’arshen gaba, gudunmawar dad’a k’arfafa gaba yayi muddin sarkin Fabarusa ya fahimci yanda ya haince shi saboda san zuciya.
Daga tawagar shugaban k’asa Kwaminishinan da yayi jawabi ne ya mik’a gaisuwar shugaban k’asa tare da gudunmawar sa na buhuhunan hatsi, shinkafa da dabino ga masarautar ta Sa’ayrsa, wanda sam kyautar ta shi ba burge su ta yi ba, a fad’ar su sai da yunwa ta ci ta cinye su har su ka kai ga neman taimako gun abokan gaba sannan zai wani kawo musu gudunmawar sa na bogi. Kafin kwaminishna ya k’are jawabin sa, wayar Junaidu ta d’au k’ara, ko da ya amsa kiran tuni fuskar sa ta canza, cikin dabara ba tare da ya bari an san halin da ake ciki ba ya ja Aisar su ka yi waje.
A cikin mota ya ke sheda masa ai jikin Shugaban kasa ya dad’a tashi kiran da aka masa kenan, su za su fara yin gaba in ya so sauran tawagar za biyo su a baya gudun kada a d’aga hankalin jama’a. Aisar ya na ji ya na gani haka su ka bar yankin Sa’ayrasa, ya na mai kudirin dawowa da sun sami kan Shugaban k’asa.
Daga d’akin taro kuwa tawagar shugaban k’asa sai neman su Aisar su ka yi su ka rasa, bayan sun kira su ne su ke sheda mu su ai sun yi gaba saboda wani uziri da ya taso, duk da dai ba du sheda mu su ainihin abun da ke faruwa ba, sai da jikin su yayi sanyi matuk’a.
An kamala taro yayinda aka ci aka sha, dan kuwa yau take salla a masarautar Sa’ayrasa. Yarima Jafar ne ya nemi a kai su ga masaukin su da ke su dama nan Sa’ayrasa za su kwana su da tawagar Yarima Sadauki. Amma bakin ciki da kuma Allah Allah da ya ke ya bud'e ido ya gan sa a Fabarusa domin shedawa Mahaifiyar sa cin fuskar da aka masa ya sa Yarima Sadauki fasa kwana, nan ta ke ya juya shi da tawagar sa ba tare da sun jira Sarki ba. Su Yarima Barde kuwa da wasu dogarawa aka had’a su domin kai su masaukin su.
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪H
Enter your comment...nice story
ReplyDeleteLabari yayi Ina cigabansa
ReplyDeletePlease Ina cigaban
ReplyDelete