Friday, 30 December 2016

KARNINMU 10

KARNINMU...

©FIKRA WRITERS ASSOCIATION

BABI NA GOMA...

Washagari da hantsi, Muazze zaune rumfar Mallam, ga kwanon tuwo gaban sa ya na shirin fara ci,wani dan almajiri ya zo ya durkusa ya na faɗin

"Muazze irin wannan sanwa haka ba ta yi?"

Tuni Muazze ya ja kwanon gaban sa sannan ya ce

"Wallahi ba za ka ci ba! Rabona da abinci tun na baran jiya !"

"Ko loma ɗaya ka emmin dan Allah!" Faɗin almajirin ya na mai haɗiyar miyau.

"Zancen kake so wai ance da gauro ya iyali!" Ya  faɗi tare da juya masa baya, almajiri na ji ya na gani ya hana masa. Hamze wanda da kyar ya ke takawa dan yunwa ya karaso ya durkusa gaban Muazze.

"Muazze na yi bara ban samu ba, tun safe ban karya ba"

Muazze da ya samu ya kai lomar tuwo bakinsa  sannan ya tura masa abincin, ya ce

"Ga nawa ka ci,bani kwanon na ka sai na sake baran, yunwa ba ta da hankali"

Tuni Hamze ya ja kwanon Muazze ya fara kai loma, hanun baka hanun kwarya. In da shi kuma Muazze ya ɗau kwanan Hamze ya bazama bara.

                    ***

Hajja Bilkis ta bakunci gidan Minister. Zaune ta ke a falon Saratu matar minister, in da su ke tattaunawa akan kungiyarsu na kawaye chan  Hajja Bilkis ta nisa ta na mai gyara zama ta ce

"Kayan nan nawa fa sun iso Saratu, zan  aiko mi ki sabuwar yar aikatau da na ɗauka ta kawo mi ki sample"

Saratu ta murmusa sannan ta ce
"Hajja Bilkis yar kasuwa, ke dai kullum cikin sauya yan aikatau ki ke ba kya ko tsoron ɗauko mugun iri"

"Ya zan yi Saratu, yan aikatau din ne ba su da tabbas, yanzu haka ma Talatu ce ba lafiya ni kuma ba zan iya wahala ba shi ne fa yaya ta aiko min da wannan" Faɗin Hajja Bilkis ta na mai duba wayar ta da ke tsuwa alamar shigowar kira. Karawa ta yi a kunnen bayan ta latsa wajen amsa kiran tace,

"Hello Honourable"

Daga bisani ta k'ara da faɗin,

"Ba na gida fa, amma na kira Iya dudu na sheda mata"

Ta aje wayar ta na mai jan tsaki Hakan ya sa Saratu faɗin

"Lafiya kuwa Hajja Bilkis? wannan tsaki haka kamar tsaka?"

Hajja Bilkis na mai kwafa ta ce

"Wannan mutumin mana! wai da la'asar zai kawo min baki gida, in sa a yi abinci da su! dan ma ya maida ni baiwa kawai sai ya kwaso min tarkace!"

"Baki daga ina? ko dai yan jagaliya?"

Saratu ta tambaya. Buɗar bakin Hajja Bilkis sai cewa ta yi

"Ba gwara yan jaliya da gayyar da zai kawo min ba! Dangin sa ne fa daga kauye, duk sanda su ka zo gidan kumewa ya ke da warin talauci da dauɗa, mstw!" ta kara jan wani tsakin

"Heyyye".

Saratu ta yi shewa har da tafa hanun.

"Dangin nasa ne za su zo shi ne bai faɗa miki ba sai yau, yau ɗin ma da rana, gaskiya dai kin yi sake kawata, kin bari Ahmad ya raina ki!"

Kasake Hajja Bilkis ta yi jin batun Saratu,kafin ta ce.

"Saratu? har kura ta ce da kare maye? ashe ki na da bakin magana ke da yanar gizo ta haskawa duniya mijin ki hajaran majaran ya goyo karuwa? Ke ni fa da ni ce ke ko kallan idon jama'a ba zan iya ba bare ma na iya yiwa wata kauɗin baki, ai Hausawa basu yi karya ba da su ka ce bagiringirin ba Saratu, ta yi mai!"

Tuni Saratu ta tsuke fuska ta na mai ɗagawa Hajja Bilkis hannu

"Dakata Malama! Ke fa matsalata da ke cin fuska Balkis, ba za ki zo har in da na ke kice za ki ci min mutunci ba!"

Hajja Bilkis na mai murmushi ta ce.

"Ai ke ɗin ce Kawata na ga ki na neman ki min iyayi, shi yasa na ce mu gani k'asa wai ance da kare ana biki a gidan su"

Gaba ɗaya fara'a da walwalar Saratu ya ɗauke, ganin haka ya sa Hajja Bilkis jan mayafinta, ta yana sannan ta ɗauki jakar ta tana mai faɗin

"Na bar ki lafiya Kawata......"

Haka ta fice Saratu ko tanka mata ba ta yi, ita kuwa Hajja Bilkis ran ta fari fat, ba ta ma san wutar da ta kunna ta bar Saratu ciki ba. Wacce tun fitar Hajja Bilkis ta ke kai kawo, dan ranta ya sosa kwarai, a da ta gani ta yi shiru, amma tunda ya fara ja mata gori daga wajan kawaye dole ta ma tufkar hanci, wannan a gaban ta kenan waya san wanda aka yi bayan idon ta!

                        ***
Tun jiya da luba ta fara zuwa wajen aikin da Minista ya ba ta, yan hayinsu  suka samu labari daga bakin matar kawu yaro,  wasu sun yi mata fatan Alkhairi wasu sun yi tofin Allah tsine.       Dawowarta  kenan karfe huɗu kamar jiya,  tafiya take kamar mai tausayin kasa,  sanye take da kamfala  ɗin kin bubu,  babu ko alkbarkan gyale illa ɗan kwalin da ta kashe ɗauri dashi.

   "mtswww!  Me aka yi da rashin abin hawa,  bari in kira minista ma kawai"  ta faɗi a bayyane tana mai buɗe jaka alamun zata ɗauki wani abun.

  Ita kanta ta manta yaushe rabon da ta hau motar haya ko achaɓa.  Amma fara aikin ta ya sa ta shiga saboda minista ya sa ta kori duk kwastamominta sai dai ya wadata ta da motoci da direbobinsa don harkokinta,  wanda hakan ba zai yiwu zuwa wajen aikin ta ba saboda gudun tonuwar asiri.

    Bata kara taku uku ba,  wata mota kirar camry XSE V-6 mai ruwan zinari  ce ta tsaya a gabanta.  Tafiyarta ta cigaba ba tare da ta kallo shi ba.  Fitowa yayi  da sauri ya zubewa,  tana shirin magana ya ɗaura yatsa a kan leɓenta  ya ce
" Afuwarki nake nema sarauniyar kyawawa,  don Allah kiyi hakuri ki min izinin zama direbanki na yau kaɗai ki ga ko na cancanci  tuka ki"

Kur, ta ke kallonsa tun da ya fara har ya kai aya don kan shi ya tsaya sannan ta gitta ta gefen shi ta cigaba da tafiya. 

   "Kiyi hakuri  ki bani dama,  kin fi karfin tafiya a kafa"  ya sake faɗi yana binta da yar sassarfa.
   
"oh!  So kake ka kashe min aure ko mene,  don Allah ka ɓace min ko in sa a kulle min kai" ta faɗi a tsiwace.  Kallonta yayi sannan ya kalli kan shi da motar da yake kai,  ya ga ai iya haɗuwa ya kai da babu macen da yake tunanin zata yankuna shi,  amma sai gashi ta masa a tsakiyar titi,  amma ji yake kamar yanda mayen karfe ke jan duk wani abin da ke da karfe a jikin shi haka so da sha'awar Gimbiya ke jan shi.

     "Naji, mu je in sauke ki,  don in har miji ne da ke Toh nine nan mijin.  Haba sarauniyar kyau,  ki taimaka min don Allah"  ya faɗi yana mai kara zubewa a gabanta karo na biyu.

Da kyar dai ya samu ta shiga motar,  zuciyar ta cunkushe da haushinsa don duniya in da wanda ta tsana yana bayan mai naci.  Ganin Shirun yayi yawa ya sa shi gyara murya da faɗin,
"Suna na Yasir,  ni ɗan asalin Kasar nan ne,  na yi karatu na a kasar Raitu,  na karanci tukin jirgin ruwa,  na kan yi wata uku zuwa shida saman ruwa duk da kasancewa na ɗaya daga cikin iyalan da suke lamba ɗaya a kasar nan (first family),  na dawo hutu ne sai mahaifi na ya aiko ni wajen ministan birnin nan.  Ashe da rabo in je masa da labarin da yafi kowanne Daɗi. " ya karasa yana murmushi.

Nan take ta kara haɗe fuska,  gabanta na dukan bakwai- bakwai amma ta ɗaure ba tare da ta bayyana hakan a fuska ba.
   
" yana nufin shi ɗa ne ga shugaban kasa,  zan ja kaya kaya kenan sai dai kuma Minista zai zama matsala,  yanzu ya kenan... "

" Kinyi shiru" ya katse mata tunaninta,  nan take ta ɗago ido ta Kalle shi,  da ganin sa yana fama da kuruciya don ba zai girme ta da shekaru fiye da biyar ba.
    "Kwanan nan zaka sauke ni,  zan karasa gida da kai na"  ta faɗi fuskarta a haɗe kamar ba ta taɓa dariya ba.
   "zan iya samun Numb ki tunda ko sunanki rowansa kike min."  ya faɗi a marairaice.
   "babu hali,  na faɗa maka ni matar aure ce"  ta ce haɗe da buɗe kofa ta fita,  shi kuma ya tsaya ya bi ta da kallo.
   
  Sai da ya ga ɓacewarta sannan ya ja motar a hankali zuwa masaukinsa. Ya rufo ɗauki wayarsa da ledan da ya aje a kujerar da luba ta zauna akai wanda a dalilin shigowarta ya aje a kasa.  Yana ɗauka sai yar posa ta faɗo,  alamun an manta da shi a waje.  Dariya kawai yayi yace
   "Ashe dai yar gari ce" 
Ya kwasa ya wuce ɗakin barcin sa.

Thursday, 29 December 2016

Dan Adam 9

Koda ta fita bata k'arasa makaranta ba har saida ta raba kanta da k'ullinnan ta hanyar wurgashi cikin wani k'aton kwata nesa da gida.

  Ummi na zaune acikin ajinsu da misalin karfe hud'u kowa ya fito don yin alwala da sallah kamar yanda aka saba a makarantar, ajin babu kowa sai ita da wasu yanmata kusan sa'annin juna su uku wadanda suma da alama suna fashin sallar ne. 
  Abin duniya gaba d'aya ya tarar mata, babu abinda take tunani sai Hajiya Binta, mamaki da tsoro lamarin mutane ke k'ara bata, idan mutum yana son kansa da yawa babu abinda ba zai iya aikatawa don samun cikar burikansa ba ashe? Ta tsunduma tsundum cikin wannan tunanin ta tsinkayi muryar d'aya cikin yanmatan nan mai suna, Maijidda tana magana wanda yayi sanadin maida hankalinta garesu.
  "Wallahi ban ga wawuya irin Anti ba a duniya, shiyasa da zarar ta fita nake yanda na so a gidannan, ko jiya da ta ficewarta wurin aikin dare a asibiti, kar kuga tsaleliyar budurwar da Abba ya kawo gidannan, agaban idona suka shiga d'akinsa da ita."
  Ido waje suka dubeta, wata fara mai bille, 'yar siririya, Amina ta soma magana.
  "Ke Jidda! Maimakon ki gayamata?"
Wata uwar harara ta watsamata kafin tace.
  "Wa kike tunanin zai gayamata? Amma wallahi ba ki da wayo, bakisan irin kud'aden da nake samu ta hanyar yin shiru da bakina ba? Ai wallahi da dai nabar samun wadannan kud'ad'en na gwammace nayita rufawa Abba asiri. Ko iyayenmu ban sanarmusu ba ballantana wata suruka. Ke Surayya ai kin ta6a ganin Antin, kinga dai bata rageni da komai ba amma wallahi akan kud'i banga wani abu da zai gagareni aikatawa ba. Wai ma da kikemin wani ihu, ba gwara ni ba akan ke da kike dauka ba'a sani ba?"
  Fad'in haka yasa cikin sauri Amina ta kai dubanta ga Ummi wacce saika rantse hankalinta baya kansu yana ga wani dan littafin addu'o'in dake hannunta. Tana jin sadda Amina ke fad'in.
  "Ummi na jinmu fa."
Surayya da Maijidda suka dara. Surayya tace.
  "Itama ai rik'onta akeyi, na tabbatar nata idan an bincika yafi namu bak'i."
  Wannan maganar ya shiga kunnuwanta saidai bata nuna ta ji ba. Suka cigaba da magana. Surayya na fad'in abinda tayi ayau.
  "Ai wallahi kunganni, ko gobe na ziyarci Katsina, sai na k'ara ziyartar Malamin nan, yanzu bakiga yanda nayi mugun raina Saddik'a ba, dad'in zama 'yar aikin budurwa kenan wallahi, agaban mijin saiki rantse ba ni bace mai zugata, idan kin ganmu saikiyi zaton k'awayennan ne, shegiya kuw a duk abinda nace shikenan yayi zaman dirshan a kwakwalwarta. Ko yau da safe saida nabata shawarar ta rage shayar da Khalifa idan ta k'i nononta ya zube."
  Suka tuntsire da dariya.
"Ke Sury, shakka babu kin fimu shu'umanci." Cewar Amina kenan.
   Hirarsu ta katse sa'ilin da d'alibai suka soma dawowa aji, banda 'Innalillahi' babu abinda Ummi ke ayyanawa a ranta, hawaye suka cika idanunta, bata samu nutsuwa ba har saida ta nemi izni wajen Malamarsu da zummar zagayawa ta sha kukanta sannan ta goge fuskarta. Tabbas DAN ADAM nada halaye mabanbanta, yana da wuyar gane hali. Wa zai ga Maijidda, Amina da Surayya ace zasu iya mugun abu kamar haka? Tun zuwanta Kano, jiya da yau ne kad'ai ta fi girgizuwa. Batun Hajiya Binta, da kuma na wadannan bayin Allahn uku. 
  Haka ta koma gida sukuku, ta sha tambaya wajen Ahmad wanda ya kasance babban d'a awajen Ramma kuma mai wayo sosai akan dalilin yin sanyinta saidai babu kwakkwarar amsar da ta iya bashi har suka rabu ta iso gidan. 
   Ta tarar da su Mami sun dawo, ta ji dad'i ainun. Bayan tayi mata sannu ta shige d'aki ta chanja sutura sai bayan isha'i sannan ta fito falon lokacin Mami ta fita gaida Alhaji. Ta wuce zuwa kicin ta dauki abincinta ta zauna agefe tana ci. Daga can saman tebur, Ihsan ce tare da su Adnan, tana ji tana labartawa Adnan had'uwar gidan Intisar da Yaya Haidar, akarshe hotuna ta shiga nunamishi. Zuwa yanzu babu ruwanta da shirgin Ihsan domin ta tsani halayenta, ita kad'ai ta fita zakkah a yaran Mami. 
                        
                   ***  ***  ***
     
   Buguzum-buguzum take tafiya tamkar zata tashi sama, babu ko sallama ta shiga gidan ta hau kwalamata kira.
  "Dije! Dije!!"
Wacce aka kira da Dije ta fito da sauri daga d'aki hannunta rik'e da waya.
  "Zan makivfulashin anjima."
Daga haka ta kashe wayar tana mai watsawa uwarta ta wani kallo kamar mai shirin dukanta. 
   "Menene wai haka Baba?"
  Habiba ta ja hannun 'yarta suka koma d'aka. Cikin sauri ta fiddo da k'ullin magani ta dubeta idanu a waje.   "Kinga Dije wannan, shine warwarar dukkanin matsalolinki, daga gidan Mai Bori nake, ta tabbatar muddin kikayi sha da wankan turaren nan, to fa kin gama samun miji tsayayye a duniya."
   Dija ta yamutsa fuska.
"Karki k'ara kirana da Dije nasha gayamaki nafison Dija, idan bazaki iya fad'a ba ki cemin Khadija."
  Habiba ta washe baki.
  "Allah Ya huci zuciyarki to, don Allah kiyi."
Dija ta kalli k'ullin ta ta6e baki.
"Yanzu idan baki manta ba shekaruna fa ashirin da takwas yanzu, tun inada ashirin kike faman takuramin da shaye-shayen magungunan da basu amfanata da komai, nafi zargin babu abinda suke k'aramin sai bak'in jinin samari. Nidai gaskiya..."
  Tayi saurin toshewa 'yarta ta baki.
"Kul! Kada na k'ara jin kin yiwa kanki mugun fata, wannan bana tantama za'a dace. Ke kad'ai gareni Dije, kinga dole na damu da rashin aurennan naki."
  Dija ta tur6une fuska, ita a yanzu auren ma ya daina damunta tunda tana samun abinda take so hankali kwance. 
   Haka uwar tayita lalla6ata har a k'arshe ta amince zata yi, jin haka ta numfasa gami da washe baki.
  "Yauwa kokefa, tace har ki bushe kada wani ko wata ya ganki, bari na shiga gidan Saude ki rufe k'ofar kada Malam ya dawo."
  Ta amsa sannan uwar ta juya ta shuri takalmanta ta fita, kai tsaye gidan aminiyarta kuma makwafciyarta ta fad'a, gidan da idan baka san shi ba, to fa bazaka ce shine ba saboda gyararrakin da ya samu. 
  A zaune ta isketa a falo tana kallo. Wani gud'a ta saki.
  "Ayyiruri nanaye! Dakyau uwargidan Balarabe, uwa ga Mariya da Atika. Kina sha'aninki fa."
  Suka tuntsire da dariya cike da nishad'i.
 
Saude ta bata hannu suka cafke kafin ta k'ara gyara zamanta akan kujerarta wadanda ta siya a sakan tana musu kallon masu kyau adalilin a baya bata mallakesu ba. 
   Habiba ta zauna sharab akan kujera tana k'ara washe hak'ora. 
   "Wallahi duk sadda na ganki kina watayawa bakiji yanda nakejin dad'i a raina ba, kai duniya."
  Wata dariya Saude ta saki.
"Bari kawai Habiba, a duniya banajin inada aminiyar da ta kaiki, karki tona zuciyata kiga tarin kaunar da ke dank'are aciki tamkar wata yar uwata ta jini, ke kin fiyemin dayawa cikin 'yan uwannawa ma wallahi."
  Habiba har lokacin bakinta ya gaza rufuwa. 
  "Burinmu kenan, yanzu don Allah ya kikaga ranar wannan shegiyar? Ai matukar za ki cigaba da bin shawarata za kiyita ganin aiki da cikawa."
  Saude ta lumshe ido ta budesu tsabar dad'in da zantukan Habiba sukayi mata.
  "Tabbas nagani, yanzu fa Balarabe ba shi da kata6us a rayuwa, komai nashi nike iko da shi, hatta da kadarorin da ya gada na iyayensa, yanzu sun dawo mallakina. Bakiga yanda k'aramin albashin wannan Shegiyar na farko ya juyemin zuwa babban jari na siye da siyarwa ba? Ai har abada ke mai kaunata ce Habiba, shiyasa na damu da damuwarki."
   
  "Ga kuma k'iyayyar da kika jazamata a dangin Mahaifiyartata." Cewar Habiba kenan suka feshe da dariya har suna fidda ruwan hawaye. Saude ta nunata da yatsa.
  "Maakira."
"Ban kaiki ba." Habiba ta amsa mata.

  Sai kuma Saude ta koma kalar damuwa.
  "Yanzu Habiba babbar damuwata bai wuce na ranar da Boka yace mu kiyayi zuwansa ba, ranar da Balarabe zaiyi tozali da Ummi."
  Habiba ta harareta.
"Wa zai bar wannan ranar ta zo aka gayamaki? Har abada bazamu kyale ba, wannan bari sai Yaha ta dawo daga Kaduna, ita zatasan tuggun da zata shirya duk lokacin da bukatar zuwa ganin gidan Ummin ya taso."
  Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa daga haka suka rufe babin Ummi suka koma na Dija inda take bata labarin maganin da ta samo mata.
  "Hakan ma yayi, Allah dai Yasa a dace. Ni kaina rashin namiji tsayayye ga Dije yana ta6an zuciya. Allah Ya had'ata da mai mota."
  Habiba ta dara cike da jin dadin wannan kyakkyawar addu'ar da ya fito daga  bakin aminiyar kwarai. 
  "Amin."
Nan suka shantake suna hira, can sai ga Mariya d'iyarta mai shekaru bakwai ta shigo hannunta rik'e da kud'i. Da gudu ta k'arasa ga Habiba tana dariya.
  "Lah, Baba yaushe kika zo?"
Habiba ta rungumeta tana dariya.
"Yar Baba, ban dad'e ba. Mene wannan a hannunki kamar d'ari biyar?"
  Mariya ta kwakume kudinta tana dariya. Ganin haka yasa Saude rik'ota.
  "Waye ya baki kud'i auta?"
Ta mik'awa uwarta.
"Usi mai kanti ne fa ya bani, wai na kawomiki ki sakamin a bankin gwangwani."
  Ta kar6a tana washe baki.
"Kai madallah, Usman ba dai kyauta ba, ince dai kin mishi godiya?"
   Habiba ta gutsiri goro ta soma tauna.
  "Haka yaronnan ya ke ai, ba dai kyauta ba."
  Daga nan suka cigaba da hira kafin daga bisani suyi sallama.

                   ***  ***  ***
           BAYAN SATI BIYU

  Rai a matukar'ar 6ace ta ke dubanta, duban da ba k'aramin kad'a 'yan hanjinta ya yi ba. Ta daure ta numfasa, cikin dakiya ta russuna.
  "Ina wuni Umma."
Maimakon ta amsa, sai ta nunata da yatsa, da kakkausar murya ta soma magana.
  "Kar ki ce za ki ci amanata har haka! Kinyi kad'an ba ki isa ba wallahi!"
  Cikin rawar murya ta soma magana.
"Me..me..nayi Umm.."
Bata kai ga k'arasawa ba, ta sanya hannu ta d'auketa da mari wanda har ta daina ji na wasu 'yan dak'i k'u. Maganarta ce ta maidota hayyacinta babu shiri.
   "Ya kikayimin aikin da na sanyaki?". Gaban Ummi ya fad'i. Ta had'iyi wani miyau dakyar tana duban ofishin mai kula da  makarantartasu inda anan ne Hajiya Binta ta zo ta sameta har Malamin ya basu wuri suyi magana bayan an jik'ashi da kud'i. Babu dai alamar akwai wanda zai kawomata d'auki, dole ta maido dubanta gareta idanuwanta na zubda ruwan hawaye, dakyar ta iya magana.
  "Nayi yanda kikace bayan nayi bismillah."

Hannu Hajiya Binta ta d'ora a ka tana buga salati.
      "Kin kasheni Ummi! Uban wa yace kiyi bismillah? Akan wane dalili zaki karyamin dokar..."
  Sai kuma tayi shiru don tsabar takaici da tsananin 6acin rai har idanunta sun ciko da ruwan hawaye, ita kad'ai tasan irin wuyar da ta ci kafin samun magani garanti wanda aka tabbatar zaiyi aiki sosai akan Hajiya Madina, har bokan ya tabbatar mata cewar matukar'ar bata ga aiki da cikawa ba, toh ta dawo ta kar6i kud'inta. A dokokin saida ya tabbatar cewar a kiyaye ambaton Allah. (Wa'iyazubillah). Mik'ewa tayi jiki babu kwari ta watsawa Ummi wani mugun kallo tayi kwafa sannan ta fice a zuciye. 
  Bayan tafiyarta Malamin makarantar ya dawo, da sauri Ummi ta mik'e ta fice, saida ta zagaya bakin famfo ta ci kukanta ta kuma godewa Allah da Ya kimtsa mata wannan dabarar sannan ta wanke  fuskarta ta bar wajen zuwa aji. 
    Salma wacce ta kasance k'awarta kuma abokiyar shawararta ta dubeta.
  "Lafiya dai Ummi?"
Ummi ta k'ak'alo murmushi.
"Bakomai."
  Salma ta girgiza kai.
"Ina mamakin wannan amincin namu, sai nake ganin tamkar ba ki daukeni komai ba."
  Ummi ta girgiza kai.
"Kiyi hakuri Salma, wani abin ba ya bukatar magana. Kedai ki tayani addu'a. Kada kiyi kokwanto akan yacce nake ganinki, Allah ne Ya had'a zumuntarmu."
   Salma ta murmusa.
"Shikenan, Allah Ya yayemana dukkan matsalolinmu."
  "Amin." Ummi ta fad'a sannan suka bar magana sakamakon karatun da aka soma.
   
Tun zuwan Ummi makarantar bata shiga harkar kowa, daga baya ne suka saba da Salma d'iya ga d'aya daga cikin malaman makarantar, Malama Zainab. Tun bata bayarda fuska, har dai ta dan sakarmata suka saba ganin da ta yi nutsastsiya ce. 
     Haka ranar suka tashi jikinta duk babu kwari. Tana zuwa gida ta soma kici6us da Ramma a tsakar gida.
  "Au, kinga 'yar halak d'inma, to ki shiga ku gaisa da Yaha."
Gabanta ya fad'i. 
  "Yaha?"
"Eh, wacce dai kikasani." Ramma ta bata amsa wanda ya sa ta fahimci maganarta ta fito fili. Ta saki murmushin yak'e, ta tabbatar zuwan na kar6ar kud'in watanta ne ba wai na bincikar lafiyarta ba. Allah Sarki, shiyasa ta ke tausayin kanta, tana tsoron ranar da Mami zata soma gajiyawa da ita ta korata, ita kam wa zata runguma?
  Ta ja kafafunta wadanda suka k'ara yin sanyi ta k'arasa cikin falon da sallamarta. Yaha ta amsa tana daga zaune saman kafet  yayinda Ihsan ke zaune ko kayan makarantar islamiyya bata cire ba tana danne-dannen waya. Fahad kuwa ya cire daga shi sai singilet da short yana kallon (cartoon). Ta washewa Ummi hak'ora cike da mamakin yanda ta chanja.
  'Shegiya, birnin ya kar6eta.' Ta fad'a a ranta. Ummi ta k'arasa ta gaisheta tana mai k'ok'arin sakin fuskarta bayan ta kauda kanta daga duban Ihsan wacce ke jifanta da murmushin rainin hankali da k'ara kallonta a ba komai ba. 
   "Ashe kinzo, sannu, ina wuni."

"Yauwa Ummi, lafiya lau. Oh! Haka kika bi kika chanja? Eh lallai."
  Ta karashe tana k'aremata kallo gami da d'an ta6e baki. 
    Murmushi kawai Ummi tayi. 
"Ai dole ta chanja, cimar ai ba d'aya ba. Anan ai akuyar d'aure ta samu sake."
  Muryar Ihsan suka tsinta ta tsomo musu baki. 
  "What the hell is this?"
Daga baya aka bata amsa. Suka dubi mai shi, Adnan ne wanda ya fito daga d'akinsa daga shi sai dogon wandon makaranta da singilet. Yana watsawa Ihsan wani kallo mai nuni da lallai bai ji dadin maganarta ba. 
  Ihsan ta had'e gira gami da d'aga kafad'a mai nuni da ko ajikinta ta cigaba da danne-dannenta tana dariyar rainin hankali. Yaha kuwa ta bata amsa.
  "Ai fa, da gaskiyarki 'yar Mami."
  Ummi ta mik'e.
"Bari na chanja kaya."
"Muje toh." Suka d'unguma da Yaha zuwa ciki, duk kokarinta saita hawaye ya zubomata ta daukesu da hannunta, wannan cin zarafi ya soma yawa, amma bakomai, tana ji a jikinta komai zaizo k'arshe in sha Allah.

  Tana chanja kaya, Yaha kuwa na tsaye tana k'arewa d'akin da ita kanta kallo. Dakin yana ayanda ta ta6a ganinsa saidai suturar Ummi take kallo duk ta chanja. Baki ta ta6e.
"Oh'oh, hum, da gaskiyar Ihsan. Wannan irin samun sake? Yaushe aka sanyaki a makarantar?"
  Ummi cikin dakiya ta amsa.
"An kwan biyu."
  "Lallai, amma bakomai tunda kina abinda ya dace, har kud'i Hajiya ta k'ara na aikinki. Kinga nan dubu shida, ta bani dubu uku. Idan naje zan damk'awa uwarki."
  Ummi ta amsa da to kawai, daman batasa ran za'a bata komai ba.
  "Ina su Baba?"
Yaha ta harareta.
"Kalau suke, da dai kin bar saka kanki a layin 'yan gidan Balarabe, bana tunanin ma wani cikinsu yana tunaki."
  Ummi ta jinjina kai tayi 'yar dariya na dole.
"Bazan bar tuna shi ba, ko ba komai shi ne ya haifeni."
  "To 'yar makaranta. Bari na rage mara dai."
Bayan shigarta bandaki, kuka sosai Ummi ta yi, dakyar ta rarrashi kanta. 
  Saida akayi Magriba sannan Yaha ta shirya tafiya, har titi ta rakata, tafiyar bata dad'i ba don kuwa magana take gaggasamata wai ita ko 'yar satar nan ma batayi don a samu a tara na aurenta cikin sauri, har suka rabu batayi mata hud'ubar arziki ba. Ummi dai ta gama tabbatarwa a duk duniya babu wani dan uwanta na jini mai kaunarta. Ko a hanyarta ta komawa gida tana tafe ne tana hawaye saids ta iso daf da gidan sannan ta gyara fuskarta. A farfajiyar gidan suka had'u da Adnan, ta dauke kai zata shige yayi azamar shan gabanta. Ta dubeshi tana dan murmushi.
  "Lafiya?"
"Sorry." Ya fada cikin sassanyar murya harda rik'e kunne.
  Abin sai ya bata dariya, ta dara.
"Me kayimin?"
Ya gyara tsayuwa.
"Banyimiki ba amma Ihsan ta miki."
Ta girgiza kai.
"Ayya, ni ya wuce. Kuma ai gaskiya ta fad'a."
  Ya daure fuska.
"Ba gaskiya bace. Karki k'ara daukar hakan amatsayin gaskiya. Ga idanunki sun nuna alamun ma kin koka. Kiyi hakuri Ummi."
         ***   ***   ***
  UMARUL FARUK DANZAKI

Kwance yake saman doguwar kujera dake a tsararren falon mahaifiyarsu. Idanunsa a lumshe kai ka rantse bacci ya ke, a can d'aya 6angaren na falon kuwa wanda nan ma komai ya ji, Hajiya Babba ce da bak'uwarta suna lissafin kayayyaki. Rabin hankalinsa na garesu, rabin kuwa kan jefashi duniyar tunani wanda kokusa baya kaunar hakan. Ya ja guntun tsaki gami da mik'ewa zaune, wayarsa ya d'auka ya bud'e (data), nan take sak'onni suka shiga tururuwar shigowa wayarsa, duk daga (Whatsapp). Ba sabon abu ne awajensa ba, yana da tabbacin kusan maza abokan aikinsa da yan uwansa sunfi yawa, mata masu turomasa sak'o k'alilan ne don bai basu damar mallakar lambarsa ba, saidai har mamaki yakeyi na yacce mafi yawa na 'yanmatan suka samu. Babban dalilin kenan da ya yiwa kannensa gargad'i akan kada su yarda su k'ara bawa kowace yarinya lambarsa. Sun ji gargad'in kuwa don sun kiyaye.

   Kai tsaye ya soma bud'e sak'onnin yana karantawa. Ga mamakinsa ya tsinceshi a wani group na Zumunta. Koda ya shiga yan uwansu ne burtik, mata da matasan. A sunayen (Admins) ya hangi wacce ta tsundumoshi ciki.
  "Iklima?" Ya fad'a a fili fuskarsa cike da mamaki, ya koma cikin group inda ya ji tana mishi marhabin da shigowa. Ayayinda wani dan baffansu dake Adamawa ya sanyo alamun dariya. Guntun tsaki ya ja gami da ficewa batare da yace uffan ba.
  Yana fita kuwa suka hau kyakyata mata dariya harda masu turo sak'on murya wanda hakan ba k'aramin k'ular da ita ya yi ba. Daman sun san halinsa, ba yau ya soma arcewa daga groups ba, da dai zaka mishi magana ta akwatin sirri, anan kam zai iya baka amsa, harma idan ka ci sa'arsa kuyi hira mai tsayi da dariya.  
    "To sai anjimanku."
Muryar Bak'uwar Hajiyarsa ce ya katseshi daga danne-dannen da ya ke a waya. Ya dubeta ya gyad'a kai cikin dan murmushi ya amsa 
  "Allah Ya kiyaye hanya."
Daga haka ta yi gaba tana mai amsawa da Amin. Mik'ewa ya yi ya koma wajen da Hajiyarsa ke zaune. Ta maida lesussukan gabanta gefe ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi.
  "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, Sadauki nawa ya akayi ne?"
  Ya d'an turo baki kamar mace, abin ya bawa Hajiya dariya ta girgiza kai.
"To shagwa6arce ta motsa?"
Ya shafi sumarsa yana 'yar dariya, itama tana tayashi, aduk yaranta tafi so da tausayinsa kasancewarshi mutum marar son hayaniya ga kuma hak'uri da rauni. Kullum addu'arta bai wuce na Allah Ya had'ashi da mace ta gari ba, ba wacce zatayi amfani da rauninsa da hakurinsa ta cuceshi ba. Ya katse tunaninta ta hanyar sanarmata batun group da aka sanyashi ya fice. Da murmushi dauke saman fuskarta tace.
  "Toh banda abinka Sadaukina, ai k'ara dank'on zumunta ne, ina zaka so ku had'u da d'an uwanka a hanya ayi abin kunya ba ka san da zamansa ba? Kaga mu ma duk muna da group na zumunci, na yan Adamawa daban, namu na dangin mahaifinku daban."
  Ya dauki filo ya sanya agefenta ya kwanta yana mai juya mata baya. Ya lumshe ido.
  "Hajiya duk wannan takura rayuwa ce, nafi ganewa mu gaisa ta private ko kuma na kira mutum ko ya kirani. Surutu ne zalla sukeyi."
  Ta dafa kansa.
"Zumuncin kenan Sadauki, wani ma hakan ya nema ya rasa. Wasu na can basu da dangin ma da zasuyi musu hakan."
  Bud'e idanu ya yi, tabbas Hajiya ta fad'i gaskiya, babu wacce ya tuna sai Ummi. Yana ji ajikinsa, akwai wani babban lamari a rayuwarta, har yau ya kasa cire kwad'ayi akan sanin tak'amaiman tarihinta.
   "Hakane Hajiya."
Daga haka ya basar da zancen.
"Wai yaushe yarannan zasu dawo?"
  "Af, su Baraka ai ansamu gidan zuwa, suna can nasan suna zuba da Intisar."
  Ya girgiza kai gami da ta6e baki.
"Ai Yaya Haidar shi ya barsu."
Hajiya ta rik'e ha6a.
"Au kai kace babu mai zuwa gidanka?"
  Ya mik'e zaune ya rungume filon yana dariya kad'an-kad'an.
   "Bance ba, amma kada a yawaita."
"Eh lallai Sadaukina, ga shi har yau ni banga surukar tawa ba, Alhajinku ma na fama."
   Ya yamutsa fuska.
"Ni wai..." Sai kuma ya yi shiru gami da mik'ewa da daukar wayarsa.
  "Aifa, daga ansoma maganar gaskiya saika gudu."
  Ya yi murmushi mai bayyana hak'ora.
   "Kai Hajiyata, ya dace dai ku d'an huta, ga na Baraka nan fa tafe, abin sai ya yi muku yawa."
  Hajiya ta harareshi.
"Wane irin yawa? Ai hutunmu yana bayan aurar da ku lafiya."
  Ya gyada kai.
  "Hakane, bari na d'an fita."
  Ya fice da sauri kada ta cigaba da magana d'aya wanda shi amsarsa har zuwa lokacin bai wuce A'a ba, don kuwa ba zaice ya ta6a soyayya ba balle  har ya ji yana son auren wata mace.
    
     ***  ***  ***
    
  
Ahmad Bashir Danzaki, haifaffen garin Kano. Ya kwashi tsawon shekaru sittin a rundunar sojoji yana aiki kafin ya yi ritaya. Matarsa d'aya tun lalle, Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiya Babba. 
  Yaransu shida cif, Usman shine wanda ya yi karatunsa kacokam akan kasuwanci. Ridwan ke bi mishi, shi din ya kasance kwararren likita a fannin mata, sai Haidar wanda ya ke lauya, sannan Faruk wanda yake ma'aikacin banki.  Baraka wacce suke sa'anni da Adnan da Iklima, tana aji na karshe a sakandare wanda tare suke tafiya. Sai auta Ikram, wacce sa'ar Ihsan ce, itama tare suke tafiya da ihsan, suna aji na biyu a babbar sakandire.  
       
  Umarul Faruk ya kasance ma'abocin son zane, daidai da dakinsa idan ka shiga haka zakayita cin karo da takardu masu dauke da zane kala-kala. Sau da yawa haka mai gyara sashensa, Bala, zaiyita kwasarsu yana zubarwa. Son zanensa bai ragu ba saida ya soma aiki ka'in da na'in, alokacin ya zamana babu kwakkwarar lokacin zane, wani sa'in kuwa sai ranar da babu aiki yakan ta6a.  Idan kuwa ka ganshi a falo, to fa hira ce ta motsa. Kokuma yan uwansa sunzo nan zasu had'u suyita kwasar hira suna dariya har mahaifinsu. 
   Rayuwarsu tana tafiya cike da sha'awa, ga ilimin addinin da na boko. Babu mai takurawa wani, hakan bai hanasu kiyaye dokokin Ubangiji ba.

             WANNAN KENAN..

                 ***   ***   ***
   Alhaji Atiku Modibbo zaune a k'ayataccen falonsa bayan ya kammala cin abinci. Ya kai duba ga sanyin idaniyarsa da ta fito daga d'akinnasa bayan kammala feshe d'akin da maganin sauro, murmushi suka sakarwa juna, ya rik'o hannunta ya zaunar da ita a gefensa.
   "Bakya tsufa Madina, menene sirrin?"
  Mami tayi dariya gami da yin farr da ido. 
  "Oh Abban Ihsan, kai dai kullu yaumin baka rabo da zolaya."
  Ya yi dariya.
"Ina zolaya anan? Babu sai tsagwaron gaskiya."
  Sukayi dariya. Ya rik'o yatsunta yana murzawa.
  "Kiramin d'ana."
  Ta cire yatsunta, zata mik'e ya dakatar da ita.
  "Ina wayarki? Kiyi amfani da ita mana."
  Ta sa hannu ta dauki wayar a saman tebur kafin ta hau laluben lambar Adnan. 
  Lokacin yana zaune a falo suna kallon Dadin Kowa suna kyakyata dariya har Ummi dake gefe zaune. 
  Bayan ya d'aga ta sanarmishi kiran Abba, a take ya mik'e ya fita.

   
Da sallama ya shiga falon bayan sun amsa. Ya k'arasa ga Abbansa ya zauna agefen kafafunsa.
   "Abba gani."
  Da murmushi saman fuskarsa ya dubi d'annasa.
  "D'an Abba, ya makaranta? Naji kun soma jarabawar karshe ko?"
  Adnan ya sosa kai yana murmushi.
"Eh Abba, komai yazo karshe in sha Allah."
  Abba ya jinjina kai. 
"To haka akeso, Allah Ya taimaka."
  Mami da Adnan suka amsa. Ya cigaba da magana.

  "Kaje kayi nazari dakyau, saika zo ka sanarmin makarantar da kakeson zuwa k'aro karatu a k'asar waje. Kada kayi gaggawa ka bi sannu, idan ka sanarmin sai mu bincika mu ga yanayin ingancinsa. Allah Ya yi maka za6i na alheri."
  Wani dad'i ya daki zuciyar Adnan, ya yita nanata ambaton Allah a zuci, a k'arshe cikin tsananin murna da d'oki ya hau yin godiya ga mahaifinsa. Haka ya tashi ya koma falon Mami cikin tsananin murna.
   Yana shiga ya saki k'ara don tsabar farinciki har yana doka tsalle. Tunda suke basu ta6a tsallaka Nijeriya ba, sai a wannan karon da yake fatan burinsa ya cika.
  Gaba daya suka zubamishi ido. Ihsan a guje ta taso.
  "Yadai broda?"
Nan ya sanarmata, ai don dadi itama ihun ta sanya gami da rungumeshi, shima Fahad agefe yana tsalle. Ummi kanta itama saita tsinci kanta cikin farinciki matuk'a, domin burinta ta ga duk wani masoyinta cikin farinciki.
    Ya yi dakinsa a guje, Ihsan ta mara mishi baya tana mai cewa.
  "Yi browsing mu dudduba makarantun."
   Bayan shigewarsu ta numfasa, babu jimawa da shigarsu wayar Adnan ta dauki k'ara. Da sauri Ummi ta mik'e ta dauka da zummar kai mishi. 
  Hoton Faruk ta ci karo da shi 6aro-6aro akan screen din wanda Haidar ke  rik'e da hannunsa shi kuma yana dubansa da murmushi mai bayyana hak'ora. Gaba d'aya sai ta tsinci kirjinta na bugu.
  "BRO FARUK." Sunan dake saman screen din kenan, ta ajiye wayar da sauri, ta kama hanyar d'aki har lokacin wayar na k'ara, haka ta juya ta koma ta dauka. Haka kawai ta tsinci kanta da d'agawa batare da tasan dalili ba. Ta gwada (sliding) wajen koren kamar yanda ta sha ganin Adnan ya yi idan zai d'aga waya. Cikin sa'a kuwa ta soma jin maganarsa yana sallama. 
   Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata, jin maganar Adnan kawai ta yi a kanta.
  "An kirani ko?"
A razane ta juyo ta mik'amai. Kasa magana tayi sai kai data gyad'a. Allah Ya taimaketa batare da Ihsan suka fito ba. 
  Ta juya da sauri ta nufi dakinta. Tana ji sadda yake fad'in.
"Afuwan dan uwa wallahi Ummi ta d'aga, fitowata kenan daga d'aki."
  Daga haka ta shige ciki da sauri.

  Shigarta d'akin ba wuya ta ji an kwankwasa k'ofar, a gigice ta dubi bakin k'ofar. Adnan ne tsaye yana murmushi. Ya mik'omata waya.
  "Kar6i, za ku gaisa da Yayana. He's my best." Ya k'arashe cikin muryar rad'a yana mai kanne mata ido d'aya, ta yi mamakin rashin ganin kowace alama a fuskarsa kamar yanda nata fuskar ya nuna tashin hankali tsantsa. Ta kasa kar6ar wayar har saida ya yi mata magana karo na biyu, alokacin tasa hannu ta kar6a, kasancewar har lokacin cikin zumudin daddadan albishir na mahaifinsa yake, yasa yana mik'amata ya juya zuwa dakinsa on don ganin abinda Ihsan ta binciko da (Laptop) dinsa. Ta tsaya cak tana duban wayar har lokacin a matukar tsoro take. Kawai sai ta ji idanunta sun cika da kwalla, to wai me zata ce? Inama tun farko bata d'aga wayar ba? Batasan cewa ya katse ba saida ta ji sabon ringing wanda ya kad'a har cikin ranta. Hotonsa ne dai 6aro 6aro wanda idan kiran ya katse bata gani, hakan ya tabbatarmata cewa a sunansa kawai ya sanya. 
  Tana hawaye ta danna ta kara a kunnenta, ji takeyi inama kada ta d'aga, ita kam ta shiga tara...!

Dan Adam 8

Ta dubi sararin samaniya, hasken farin wata ya taimaka kwarai wajen k'ara haskaka unguwar, hakanan kuma akwai hasken fitili domkn unguwa ce ta manya. Ta numfasa ta soma bin hanyar da taga Danliti ya biyo da su dazun. Tafiya kawai takeyi batare da tasan takamaiman inda zata nufa ba bayan nan, hakazalika batajin ko son ta koma wajen walimar. Ta gwammace idan ma saceta ayi muddin za'ayi nasarar rabata da wajen nan. Ita kam ta tsani cin zarfi da disgi. Tayi nisa amma ba sosai ba, ta ga mota a gefenta tana tafiya sannu-sannu, wannan baisa ta tsaya ba ballantana kuma ta waigo. Ta ji k'arar hon da k'arfi, ta runtse ido tana mai cigaba da tafiya kai ka rantse Ummi tsabar yanga ce takeyi, ga wanda ya santa kuwa yasan tafiyarta ce hakan, saidai duk da hakan na yau yafi na kullum don tana taku ne jikinta babu laka, gaba daya a sanyaye yake, zuciyarta banda bugu da sauri-sauri babu aikin da takeyi.
"Ummi."
Taji faduwar gaba jin muryar Yaya Faruk. Ta waigo da sauri ta dubi motar, kasa jure kallon kwayar idanunsa tayi masu kyau da fisgar hankali tayi gefe da idanunta batare da ta cigaba da tafiya ba.
"Shigo."
Ta daure ta kara dubansa tana mai share hawayen da suka zubomata, girgiza kai tayi.
"Kayi hakuri Yaya Faruk, bazan iya komawa..."
"Gida zan kaiki." Ya katseta da fad'in hakan. Ta danyi jim, tana tsoron kada Hajiya tayi fad'a saidai kuma ta gwammace fad'an Hajiya da dai ta k'ara komawa wajen da ba'a dauketa a bakin komai ba face wulakantacciya. Jiki babu kwari ta sanya hannu zata bud'e gidan baya, ya rigata bud'e na mazaunin gefensa.
"Nan za ki shigo." Gabanta ya fad'i. Ta kasa cewa komai duk kuwa da cewar ta raina aji, matsayi da kuma girmanta ace wai itace zaune agefen matashin da ya had'a dukkan wadannan abinda takejin ita din bata da shi, abin kamar dai a mafarki. Da bismillah a bakinta ta shiga ta rufe a sannu, ajiyar zuciya ta saki jin wani azababben kamshi ga kuma sanyin Ac da ya ratsa jikinta. Ya soma tuk'i cikin gwanancewa bayan ya maida gilas ya rufe, ya k'ara k'arfin Ac kad'an. Saida suka bar layin gaba daya sannan ya rage gudun da yakeyi ya soma magana tamkar baya so, magana mai cike da nutsuwa da kasaita.
"Bansan da haka ba, idan ma nasani toh watakila zuciyata ce wacce ke jin tsananin tausayi yaran da kuma jin haushin iyaye masu barin yaransu yawan aikatau, ya sanyani kasa nutsuwa nayi tunani mai kyau akan haka. Akan abinda na fad'a, ina neman afuwa, kiyi hakuri kinji?"
Ya karshe yana k'ara k'ank'an da muryarsa tamkar mai rad'a. Wannan yasa zuciyar Ummi cigaba da harbawa da sauri-sauri. 'Nayi hakuri fa yace?' Ta tambayi zuciyarta, ta lumshe ido ta bud'esu, ashe daman masu kudi sukan yi laifi kuma su bawa 'yan aikinsu hakuri? Ikon Allah.
"Kinji?" Ya k'ara furtawa cikin kara kankanta murya, sai kuma alokacin ya dubeta. Gani yayi fuskarta ta yi fayau, hakanan idanunta sun d'an kumbura adalilin kukan da ta ci. Haka kawai ta ga ya gangara gefen titi ya tsaya. Tayi duba da wajen, wajejan gidan gwamna ne na garin Kano, abinda yasa ta rike hakan ma bai wuce adalilin Fahad da ta ta6a ji ya fad'a ba.
Ta dubeshi kad'an, shima ita ya fuskanto. Ta kauda kai tayi narai-narai da fuska tamkar mai shirin yin wani kukan.
"Na hakura, ni daman banyi fushi ba. Ni wace da zanyi fushi da.."
"Ni d'in wanene da na fi karfin ayi fushi da shi?"
Ya katseta ta hanyar jefomata tambayarnan. Tayi kasa da kanta batare da tace uffan ba.
"Ni ba kowa bane face DAN ADAM, kuma duk dan Adam ajizi ne, yakan kuskuro, wani da saninsa wani kuma baisan ma kuskuren bane. A rayuwa, bani da raayin shiga lamuran da bai kasance matsalata ba, ban fiye damuwa da shiga rayuwar mutane har ma na takura musu ba ok? Abinda ya kaini har nayi miki batun bai wuce na fusata..."
Sai kuma yayi shiru bai k'arasa ba.
"Kiyi hakuri." Shine abinda ya k'ara furtawa. Cikin rawar murya Ummi ta share fuskarta wanda zuwa yanzun batasan dalilin kukannata ba, ta dangana da tuna mahaifiyarta da tayi wacce kokusa bata ta6a jin dumin jikinta ba.
"Ya wuce Yalla6ai, don Allah ka daina bani hakuri."
Ya zubawa fuskarta ido kafin ya saki murmushi mai 6oyayyar fassara.
"Thank you." Daga haka ya soma tafiya, tana jin wayarsa na faman ruri. Duk bai dauka ba, sai ana uku ta ga ya dauka. Haidar ne, hakuri ya shiga ba shi ya sanarmishi wani uzuri ne ya hanashi karasowa da wuri amma yana nan tafe. Daga haka sukayi sallama.
Ummi tayi lamo tana tunane-tunanenta, ko a mafarki idan akace mata Faruk nada mutunci har haka, toh zata iya musawa idan tayi la'akari da yanayinsa koyaushe cikin daure fuska, sa'a ce ke sanyawa kaga fuskarsa a sake kamar yanda sa'ar ce ta ci ta ganta dazun dauke da murmushi.
"Mene sunanki na ainahi?"
Ya watsomata tambayar batare da ya maida hankali ga dubanta ba.
"Hasiya." Ta fad'a a tsanake kamar ta karawa sunan dadi domin kuwa babu wacce ta fad'omata a rai alokacin sai mahaifiyarta wacce sunanta ne ta ci.
"Nice name, suna kika ci ne?"
Ta gyada kai.
"Sunan mamana ce."
Da mamaki ya dubeta.
"Mamanki tana nan?"
Ummi idanunta suka k'ara ciko da ruwan hawaye, ta k'ara narkar da murya tana son yin kuka.
"A'a ta rasu wajen haihuwata."
Maganar ta dakeshi, ya daure ya hadiye abinda ya ji na tausayinta, saidai duk da hakan saida muryarsa ta kasa 6oyewa.
"Allah Yayi rahma agareta."
Ta amsa da amin cikin zuciyarta. Duk da wani 6angare na zuciyarsa tana so tasan fin haka game da ita, saidai bai ga wata hujja da zai kare kansa ba idan ta nemi sanin dalilin tambayar duk da baya zaton haka din.
Har suka isa babu wanda ya k'ara cewa uffan, hakazalika, kowanne da irin tunanin da yake. A zahiri Ummi ta fi karkata ne ga tuna rayuwarta, babban abin tambayar da bata da amsa shine inda zata ga dangin mahaifiyarta, a 6angare guda kuwa, tana mamakin Faruk da halinsa wanda batasani ba. Bata manta gargadin Ihsan gareta a kwanakin baya.
'Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki.'
Wani murmushi mai ciwo ya su6uce mata daidai kuma lokacin da Faruk ya kallota, kawai sai ya tsinci zuciyarsa cikin jin sanyi, ko babu komai bazata fita motarsa da fushinsa ba.
Tsayuwar da ta ji yayi ne yasa ta fahimtar sun iso don gaba daya ta luluk'a tunanin dabi'un Ihsan wanda ya sha bamban da na sauran yaran Mami. Suka dubi juna ido cikin ido, gaba daya sun ji wani iri wanda tsakaninsu babu wanda ya bada tunani na daban.
"Saida safe."
Ya sanya hannu ta 6angarensa ya ciremata (lock). Batare da ta amince sun kara hada idanu ba ta amsa.
"Nagode, Allah Ya tsare hanya. Don Allah ka sanarwa da Mami na taho gida kada ranta ya 6aci, idan da hali kada ka nuna kai ka kawoni don Allah."
Yayi shiru yana mamakin dalilinta na fadin hakan, sai kuma ya ta6e baki ya daga kafada kadan.
"Nifa ban iya karya ba, ba kuma zan fara saboda ke ba ok? Idan ta tambaya zan fadamata."
Ya karashe da murmushi yana dubanta, ta kauda kanta. Banda toh babu abinda tace ta sauka. Ta rufe kofar batare da ta kara kalla ba sakamakon duhun gilashin.
Ya bita da kallo har ta shige ciki, ya numfasa. Mace kam har mace Ummi ta kai. Shine kawai abinda ya ayyana a ransa daga haka ya ja motarsa yabar wajen a miliyan. Mintuna goma bai cika ba ya isa ga wajen party. Ya kuwa iske Mami na nemanta, nan ya sanarmata yanda akayi, yayi kokarin cewa a hanya ya ganta tana kuka tana tafiya ya taimakamata baisan abinda ya faru gareta ba. Mami tayi mamaki, karshe ta yanke da zarar sun koma zata ji ko menene.
"Mutuminki gashican ya iso."
Da sauri Iklima ta kai dubanta ga inda kawarta Hassana take mata nuni, wani wawan ajiyar zuciya ta sauke har tana hamdala a fili. Abin ya bawa Hassana dariya, kawai gani tayi Iklima ta ja hannunta.
"Muje ki rakani na gaisheshi."
Hassana ta so k'in zuwa don gudun kada ya disgata, saidai dole hakanan ta bi bayanta suka nufi inda yake a tsaye bayan amarya da ango suna gaisawa.

Haidar ya dubeshi yana mai kai bakinsa saitin kunnensa.
  "Tsaya muyi hoto mana."
Yana murmushi yayi kokarin zillewa, abin saima ya bawa Haidar domin kuwa yafi kowa sanin Faruk bai fiyeson hoto ba. Ya dank'eshi, a hakan ma sunsha hotuna wajen jama'a masu wayoyi, dakyar ya tsaya yana duban Haidar fuskarsa dauke da wani hadadden murmushi, a haka aka daukesu.
  Cikin masu daukar hoton, har da Iklima wacce gaba daya ta gama narkewa cikin so da kaunar Faruk wanda ya gama tafiya da ruhinta.  Bata bi ta kan Hassana ba ta mara mishi baya da sauri tun baikai ga k'arasawa wajen yan uwansa ba wadanda su yake yiwa kallon abokai domin Faruk ba shi da babban amini ke6antacce da za'a kira nasa akoyaushe. Bazai rasa abokan ba, duk wata shawara acewarsa yayyunsa sun isheshi.
  "Ina wuni Yaya Faruk." Muryar da ya tsinkaya kenan daga gefensa. Ya kai dubansa gareta, take kuma sai ya tsuke fuska tamkar ba shine ke murmushi ba yanzun. Kansa kawai ya gyada sannan yayi gaba. Da sauri ta juya itama tun baikai ga bata kunya ba. Tun kafin ta kai ga Hassana, take watsa mata harara har ta dangana da mazauninta. Alokacin ne ta samu damar yi mata magana.
  "Ai ga irinta, saida nace kada kije amma kika k'i saurarona, yanzun da ya jefeki da kallon banza ai kinji dadi."
  Tana maganar a fusace. Iklima idanunta akan Faruk wanda ke hira abinsa hankali kwance, ta murmusa.
  "Yasan ya had'u ne shiyasa yake shan kamshi ga yanmata. Wallahi ina sonsa fa."
  Hassana ta ta6e baki. "Shi kuma baisan da zamanki ba."
  Sai alokacin ta dubeta tana harara.
"Wai me kikeson ki cemin? Kin manta  alak'armu da shi ne?"
  "Naga Ihsan ma k'arewar alak'a da shi ai." Hassana ta fada gami da jan dogon tsaki sannan ta cigaba da maganarta.
  "Shi namiji idan yaga kin fiye zakemishi rainaki zaiyi wallahi, ki kula dakyau leema, kisan dai dabarar da zakiyi ki shawo kansa, amma idan har zaki cigaba da yi mishi irin wannan shishshigin agaban jama'a, toh fa zaki raina kanki."
  Iklima tayi shiru tana sauraronta, ga dukkan alamu dai maganganun Hassana yana shigarta. Tayi na'am da shawararta na cewa ta dinga yi mishi ladabi a fili da kuma online.(chatting), a sannu idan suka saba sai tayi kokarin shawo kansa.
  Haka aka tashi taron kowa cike da farinciki idan an cire Iklima wacce bataji dadi ko kadan ba na yanda Faruk ya gwatsaleta ba.

Koda su Mami suka koma gida, ta tuntu6i Ummi akan dalilinta na barin wajen (party), bata 6oyemata yanda sukayi da Ihsan ba, da kukan da Faruk ya ga tana yi ya taimaka ya kawota gida. A take Mami ta nemi Ihsan a waya amma fir ta karyata tace batasan ma da zaman wata Ummi awajen ba. Ranar duka ne kawai Ummi bata ci ba, amman ta sha fad'an Mami sosai, acewarta bazata lamunci a dinga yiwa yaranta karya ba akan abinda bai zama halinsu ba. 
  Haka Ummi tana ji tana gani aka k'aryatata aka bata laifi, dole ta bawa Mami hakuri sannan ta bi umarninta ta chanjawa Fahad kayan bacci ta nemi makwancinta. Bacci gaba daya gagararta yayi don ta kasa tsaida hawayenta, sai wajen asuba ta samu ya dauketa. 
       Washegari suka shirya tafiya Abuja kai amarya. Da yawansu ta mota zasu tafi, ciki harda Mami. Hakan yasa da sassafe ta kammala komai, kasancewar kwana daya zasuyi ta amince Ummi ta zauna agidan tare da su Adnan. Ta mascara mata cewa ta rik'e amanarta. Daga haka sukayi sallama, ita da Ramma na binsu da adduar sauka lafiya. 
   Misalin karfe biyar na yamma, babu kowa a sashen Mami sai Ummi dake kwance a tsakar gida. Fahad da Adnan sun fice yawo, Ihsan kuwa har lokacin bata dawo ba, da alama da ita aka nufi Abuja, Ramma kuwa daman tun tafiyar Mami tana kammala ayyukanta ta bar gidan. 
  Muryar da ta ji tayi sallama ne yasa babu shiri ta mike zaune a matukar razane. 'Hajiya Binta?' Ta fad'a a ranta cike da mamaki. To mene ya kawota sashen Mami alhalin a baya ba shigowa takeyi ba? 
  Fuskar Hajiya Binta a sake  ta k'arasa shigowa ciki tana d'an waige-waige. 
   "A'a Ummi, ba kowa ne sai ke kadai?"
Ummi ta russuna cikin ladabi ta amsa mata.
  "Eh Hajiya. Ina wuni."
Hajiya ta zauna a saman wata kujerar roba cikin karamar murya kamar mai rad'a ta amsa.
"Lafiya lau Ummin Hajiya. Sai kyau kike k'arawa Masha Allah."
  Murmushi ta dan yi mai kama da yak'e domin ba wani sabo tayi da ita ba, banda munanan kalamai da take watsamata aduk haduwarsu, babu abinda ke shiga tsakaninsu. Maganar Hajiya Binta wacce ta k'ara matsowa dab da ita ya katse tunaninta.
  "Ummi ina neman wata alfarma daga gareki, matuk'ar kika amince kika yi yanda na sanyaki, toh ina miki rantsuwa da Allah zakiji dadin rayuwarki. Ina tabbatar miki sai kin samu 'yanci agidannan kamar kowace 'ya matukar kikayi yanda nace."
  Ummi ta ji kanta yayi dumm. Ta rasa gane alkiblar da maganganun Hajiya Binta suka dosa. Ta dubeta duba na neman karin bayani. Hajiya Binta ta kara lek'en bayanta, bata ga wani ko wata dake tahowa ba. Ta fiddo wata bak'ar leda daga zaninta ta bud'eshi gami da nunawa Ummi. Ummi ta zaro ido cikin matukar kad'uwa ganin wani abu wanda aka duk'unkule da farin zare mai yawa wanda har ya zamana baka ganin komenene aciki sai zaren da yayi kamar bal. 
  Ji tayi ta soma gumi cikinta kuwa wani hautsinewa ya yi na ban mamaki. 
   Hajiya Binta wacce gaba daya ta gama kwadaituwa da samun cikar burinta ta cigaba da magana.
  "Wannan kadai zaki ajiye a k'ark'ashin gadon uwardakinki, daga tsakiyar gadon, shikenan kin kammala mini komai. Wallahi Ummi zakiji dadin rayuwa fiye da zatonki. Zaki samu duniya yanda baki ta6a kawowa ba. Za kuma ki jera da yaran gidannan a zuwa makaranta mai tsada, a fannin ci da sha da kuma sutura. Rik'e kiyimin yanda nace."
  Ummi na k'ok 'arin magana ta tsaidata ta hanyar damk'a mata abin a hannunta. Ta jefeta da murmushi.
  "Zan nemeki gobe." Daga haka ta mik'e sai kuma ta dawo baya. Fuskarta a murtuke ta dubeta, duban da ya k'ara hautsinata.
  "Karki soma yunk'urin tonamin asiri, muddin kika soma sai na lahira ya fiki jin dadi. Ki kula." Daga haka ta fice da sauri. A nan kofar shiga ta tarar da aminiyarta ta, Hajiya Luba wacce ke tsayuwar gadi kada wani ya taho ya iskesu.  Tana ganinta cikin rad'a tace.
"Angama?" Hajiya Binta tayi dariya.
"Ta isa daman ta k'i?"
  Sukayi dariya k'asa-k'asa gami da cafkewa sannan suka bar wajen da sauri.
  Ummi ta shiga tsaka mai wuyaaa....!
 

   Gaba d'aya gigicewa tayi, tayi sauri yarr da kullin a kasa kafin ta cigaba da ambaton Allah a fili. Ita kuwa Hajiya Binta me take nema haka a duniya da har zata iya yiwa wani asiri? Ummi a iyakar tsawon rayuwarta ta tsani mugunta ta tsani mai yinsa. 
   Ta k'ara kallon kullin cikin zubar hawaye, tunanin kada Adnan ya dawo ya isketa da shi yasa ta mike a gaggauce gami da daukarsa da hannun hagu don kuwa tsoro da kyankyaminsa take. Allah Yayi mata tsari da aikata mummunan aiki irin wannan. Shine addu'ar da take ta nanatawa a ranta.  Kai tsaye ta nufi dakinta da shi ta kulle cikin bak'ar leda da zummar washegari idan zata makaranta ta yarr koda acikin kwata ne. 
   Bayan ta adana shi inda babu mai gani tunda ba mai shigowa dakinta, ta fito ta zauna jigum, gaba daya a tsorace take. Kuka kam ta sha, a karshe dai tayita addua akan Allah Ya ku6utar da ita daga sharrin Hajiya Binta. 
  Bayan dawowar su Adnan dole ta saki ranta kada su gane. Ya damkamata karamar robar (ice-cream) da suka siyo, suma suka zauna a falon suna kallo suna shan abinsu hankali kwance. Ita dai sha takeyi amma kokusa kallon baya gabanta, koda ta soma jin dadinsa da zarar ta tuna da Hajiya Binta sai jikinta yayi lakwas. Karshe rufe robar (ice cream) din tayi gami da shigewa daki bayan ta nemi zubomusu abinci sun tabbatar mata sun k'oshi. Daman ta ga alama, kawai dai gudun kada ace tayi laifi ya sanya ta tambaya.
   A ranar Ummi dai bata runtsa ba, gani takeyi kamar wani abin zai sameta asanadin kullin da ke a dakinnata. Bata ta6a fatan ace tana da wayar hannu ba sai a wannan dare, da babu abinda zai hana ta sanarwa Antinta ko don ta bata shawarar yanda zatayi. 
     
     Washegari Adnan suka fice makaranta, ya tabbatarmata su Mami sai wajen yamma zasu dawo. Hakan yasa suna tafiya ta bude dakin Mami don daman mukullin yana hannun Adnan sai a yanzun ya damk'amata. Ta tsaya cak a tsakar dakin tana tuno da mugun aikin da Hajiya Binta ta sanyata. Tausayin Mami ya mamayeta.
  "Baiwar Allah kenan, tana zama da ita da zuciya d'aya, ashe tana da wani mugun kulli dangane da ita." Cewar Ummi a fili don bil hakki tausayin Mami ya gama mamayeta. Haka ta gyaramata ko'ina tsaf ta wanko bandaki ta goge duk inda ya dace sannan ta feshe dakin da turare ta kulle. 
   Tana shirin soma gyaran falon Mamin ne. Ta tsinci sallamar Hajiya Binta. Gaba daya saida ta ji tsayuwa na neman gagararta. Dakyar ta samu nutsuwa bayan karanta addu'o'i. Ta nufi falon tana mai amsawa cikin dakiya. Wani zun6ulelan hijabi ne ajikinta, fuskarta ya nuna bata jima da tashi daga bacci ba. Ta sanya hannunta a k'ugu, fuskarta a murtuke wanda ya rud'a Ummi saidai tayi iyakar kokari bata bari ta fahimta ba. Da sauri ta durkusa.
  "Ina kwana Umma."
Batare da ta amsa ba, ta zarce ga abinda ya kawota.
  "Kinyi aikin da na sakaki?"
  Ummi ta k'ak'alo murmushi.
"Fitowata kenan ma daga aikin Umma, nayi yanda kika umarceni."
  Wani sanyi ya ratsa zuciyar Hajiya Binta don har ga Allah bata yiwa Ummi kallon mak'aryaciya, dari bisa dari ta yarda da cewar ta aikata. 
  "Tabbas kin biyani Ummi, kuma muddin Hak'ata ta cimma ruwa, bazan watsamaki k'asa a ido ba. Abu d'aya nake gargadinki akai, ki kiyaye bakinki. Wallahi Ummi kikayi kuskuren tonan asiri saina k'ullamiki mummunan sharri."
  Daga haka ta fice da sauri. A can kofar da ta raba sashensu da na Hajiya Madina, sukayi kick6us da Ramma. Ta gaisheta tana cike da mamakin ganinta. Hajiya Binta ta amsa cikin basarwa gami da fad'in.
  "Ashe kuma Hajiyar bata dawo ba? Na dauka tana nan na aikomata tallar dogayen riguna."
   Ramma ba don ta gamsu da wannan shirgaggiyar ba, ta amsa da.
  "Ai Hajiya munyi waya sai zuwa yamma tacemin zasu iso."
  "Allah Ya kawosu lafiya."
  Daga haka ta wuce da sauri don ta tabbatar da wuya idan karyarta ta samu shiga. Ummi wacce tub jiyo muryar Ramma ta biyo bayanta a guje cikin kad'uwa, ta ji tattaunawarsu. Tayi saurin komawa. Bayan shigowar Ramma ta hau kwalamata kira da k'arfi, a rud'e ta k'araso. 
   "Baba Ramma ashe kin zo, ina kwana." Cewar Ummi ba a nutse ba. Ramma ta zubamata ido, gaba daya zargi ya d'arsu a ranta. 
  "Lafiya naga Hajiya Binta anan? Ki fadamin gaskiyar abinda ya kawota."
  Ummi wacce ta soma had'a zufa ta bata amsa batare da ta kalleta ba.
  "Um..nima nayi mamaki,  tambayata tayi ko Mami sun dawo nace aa shine ta tafi."
  Ramma ta gama hango rashin gaskiya k'arara a fuskar Ummi, saidai kasancewar tasan k'arya baya daga cikin d'abi'arta yasa nan take ta amince.
  "Toh Allah Ya kyauta, wannan dai salon munafuncine, tana nan ba'a shigo ba sai bayan da ta k'aura. Mutane dai ba tsoron Allah, Allah Yasa ba wani mugun abin ta..."
  Sai kuma ta datse maganar da fad'in.
  "Um, Allah na tuba. Bari na kama abinda zai fishsheni."
  Daga haka ta fice daga falon, Ummi Ta sauke ajiyar zuciya don gaba daya ta gama tsorata. Ita kanta jinta takeyi wata marar gaskiya

Dan Adam 7

Washegari ya kama ranar da za'a daura aure da kuma yini. Tun safe da mutanen dakin Mami suka farka, babu wanda ya koma bacci. Daga Maigidan har sauran yaransa maza, shirye-shiryen karyawa sukeyi su wuce d'aurin aure, yayinda Mami itama ke shirin tafiya gidan biki. Ummi kuwa, ayyukanta ta shiga yi cikin sauri-sauri bisa umarnin Mami, don kuwa a son Mami, tafiso tana can a daura aure maimakon ace bata isa ba. Itama Ramma sanin da tayi na cewar Mami da wuri zata fita ne, yasa ta shiryawa da wuri, bata da wani aiki a kanta mai yawa kasancewar yaranta sun je k'auye. Wannan karon dai Ummi ta ji maganar Amina, don kuwa ta shafe fuskarta da hoda sannan ta sanya jan baki kalar ja sai kwalli data zizara a idonta. Ita kanta tasan tayi kyau, irin kyawun da bata ta6a ganin ta yishi ba, ko don ba kwalliyar takeyi ba?
  Ankon bikin da Mami tayi musu ne a jikinta, ya zauna d'abas kamar a jikinta aka d'inkashi, ya fito da kyakkyawar surarta wanda ita kanta batasan tana da diri mai kyau ba kamar haka. Har ta dauki mayafi ta yafa sai kuma ta ga sam ba zata iya ba, hakan yasa ta janyo farin hijabinta wanda ya hau sosai da atamfarta mai adon fari da koren fulawoyi. Kiran da Mami ta kwalamata ne yasa ta amsawa da sauri don bata da masaniyar cewa Mamin ta shigo falon domin itace a fadar Alhajinsu.
  "Masha Allah." Shine furucin da Ummi tayi a ranta, duk iyakar yanda take ganin ta fito tayi kyau, sai ta raina shigarta ganin shigar Mami, ba irin ankonta bane a jikinta. Wani tsadadden  leshi ne ruwan madara mai duwatsu dinkin doguwar riga da zani ta sanya, anyi aiki a gaban rigar leshin wajen kirji, banda kamshi babu abinda kakeji yana tashi a falon. Hannunta rike da jaka da mayafinta. Ta dubi Ummi duban tsaf kafin cikin sakin fuska tace. "Ashe dai kin iya kwalliya." Abin  ya bawa Ummi mamaki, kodayake dai tasan yau Mami cikin farinciki take. Ramma dariya tayi kawai, itama tayi tsaf da ita tana rike da karamar jaka na kaya wacce ta tabbatar na Mami ne.
   "Shiga ki cewa su Hajiya Binta idan sun shirya su fito mu wuce."
  "Toh." Sannan ta kama hanya da mamakin wannan irin iko na iyayen gida irin Mami, wato bata damu da ta sanarmusu su shirya ba tun farko saida ta tashi tafiya. Sashen Hajiya Binta ta soma zuwa, a zaune ta sameta tana latse-latsen waya ko wanka batayi ba. Ciki-ciki ta amsa sallamar Ummi, gabanta na dukan tara-tara, ta durkusa ta shaida mata sak'on Mami. Kamar ba zata ce komai ba saidai ta dubeta a wulakance har saida ta ji ta muzanta.
  "Ki sanar da ita cewar tana iya tafiya, don banason had'a tafiyata da shirgi."
  Ummi dai toh kawai ta furta sannan ta mike.
  "Tsaya Ummi." Cewar Iklima wacce ta fito daga d'aki cikin shirin shadda ruwan k'asa mai turuwa, dankwalinta a hannu da ribuna. Gaba daya suka dubeta. Ta dubi Hajiyarta.
  "Ni zan bisu yanzu mu tafi."
  Hajiya Binta ta bita da mugun kallo, ta tabbatar wannan rawar kafar da takeyi bai wuce na son ganin Faruk ba, ita kuwa ta ci alwashin koda Iklima zata mutu, ba zata ta6a bari ta auri jinin Mami na kut da kut ba.
  "Banyi miki iznin binsu ba, ke wuce ki isar da sak'ona. Tana iya tafiya."
  Ummi jin haka yasa ta juya gami da dan ta6e baki, da sauri ta kara gaba batare da ta jira jin yanda zata kaya tsakanin 'ya da uwarta ba.
     Kai tsaye dakin Anti Amarya wato Hajiya Lubna, ta nufa. Ita kam babu laifi tana da tsafta itama duk da cewa ko rabi-rabin kafar Mami bata kama ba, bata falon sai yaranta. Babu wanda ya yiwa Ummi kallon banza, saidai kuma basu bada muhimmanci akanta ba don hankalinsu ya tafi ga kallon wani film na yak'i da ake haskowa a (Mbc Max). Ganin haka yasa ta kara magana.
   "Don Allah ina Anti Amarya? Mami ce ta aikoni wajenta."
   Hassana ce ta dubeta.
"Me za'a ce mata?"
  Ummi ta sanarmata, Hassana ta shiga dakin mahaifiyarsu. Ummi ta cigaba da nazarin falon, ta lura dai kusan duk girmansu daya da na Hajiya Binta, Mami ne komai nata ya fita daban mai yiwuwa kuma don itace farkon zama a gidan kafin zuwansu. Hakanan ta kasa bambance falon wanda yafi shan kaya acikinsu, don kowanne falo akwai nasa kyawun na musamman. Tunaninta ya katse bayan fitowar Hassana.
  "Tace sai zuwa anjima yanzu kanta yana sarawa ta sha magani ne."
  "To, Allah Ya bata lafiya." Daga haka ta mike ta fita.
  Mami tuni sun shiga mota, itama shiga tayi sannan ta sanarwa Mami sakon data samu wajen kowannensu bayan ta yiwa sakon Hajiya Binta kwaskwarima inda tace kawai sai zuwa anjima zata taho. Danliti yasa hancin mota ya fita daga harabar gidan.
    Sunci sa'a don kuwa ba'a kai ga daura aure ba an dai tafi. Motoci cike makil ne a kofar gidan har babu wajen fakin, dole daga nan waje Danliti ya saukesu sannan yayi gaba don neman wajen ajiye mota.
   Gidan a cike yake da yan uwa da abokan arziki na jiki sosai, Ummi banda rarraba ido yanda zata ga Amina babu abinda takeyi, saidai ko kusa bata hangota ba. Ga waje da mutane ba kadan ba ballantana tace zata nemeta. Haka ta hakura ta nemi gefe guda saman tabarma anan tsakar gidan ta zauna tana kalle-kalle. Kwalliya iri-iri, da wadanda suka burgeta da wadanda ko kusa basu burgeta ba take gani, a haka Ihsan ta zo ta wuce, har ta gaji da haduwa sai daukar ido takeyi. Ummi ta bi takalminta da kallo wanda yake da tsini sosai, jinjina kai kawai tayi tunanowa da Tasleem ta 'Yar Bariki wacce ta tsinci Ihsan kwanaki tana labartawa Adnan yanda labarin yake, har take mishi batun takalman da Tasleem ke sanyawa. Toh ita kam bata ga marabar takalmin da Ihsan ta kwatanta  da wannan dake kafarta ba. Da ace itace ai babu abinda zai hanata karyewa a kaita d'ori, sai ikon Allah.
    Ta jima sosai anan zaune, kafin ta soma jiyo gud'a sosai yana tashi daga hancin tsoffin dake a wajen.
  "An d'aura." Shins furucin da ta ji a bakunansu. Nan kuma ta ga tawagar kawayen Amarya dake a tsakar gidan sun karasa falo suna faman ihu da gud'a. Haka aka cika mak'il a falon Innar su Mami. Ganin da tayi ba zata iya lek'e ba yasa dole ta hakura ta koma da baya ta raku6e jikin bango ta zubamusu ido. A haka tawagar angwaye kuma kusan yan uwan juna gaba dayansu, don da yawansu daga Adamawa suke, yan uwansu ne sai kuma Abokai suma babu laifi.
   Bata ci wuyar hangen Ango Haidar ba, ya cakare cikin farar shadda wacce ta sha aiki mai tsada. Sai wani shek'i yakeyi. Hakanan kusan gaba daya tawagarsa fararen kaya ne jikknsu idan ka cire yayyun Ango da kaninsu Faruk, wadanda sukayi ankon shadda ruwan madara. Sunyi kyau har sun gaji da haduwa, Ummi ta karemusu kallo, tabbas 'ya'yan Hajiya Babba abin so ne ga dukkan wata diya macen da take ji da kanta ita din mai aji ce. Idanunta suka fi karkata ga Faruk wanda ta ga kamar an kara matso kyawunshi, a yau yafi koyaushe haduwa domin kuwa fuskarsa yau a sake take hakanan hakoransa a bayyane har gefen kuncinsa na dama ya lotsa. Ya sanya farin tabarau a idonsa, ta sauke ajiyar zuciya, koda ace batasan me ake kira da hadadden namiji ba, to shakka babu akan Faruk ta sani. Cikin sa'a kuwa shima idanunsa suka sauka akanta daidai lokacin da yake gyara zaman agogonsa. Haka kawai ta tsinci yanayinta ya sauya adalilin kallon da yayi mata wanda ta tabbatar haka kwayar idanunsa suke, ba wai da gayya ya yi ba. Ga mamakinta fuskarsa bata sauya  daga murmushin da yakeyi ba duk kuwa da cewar sun hada ido da shi, ta numfasa ta kauda kanta har suka shige zuwa Falo wajen iyayensu.
 
  
 
  Ta sauke ajiyar zuciya, gami da zame jiki ta durkusa a wajen. Yau Faruk ne yayi mata murmushi? Sai tace tun zuwansu bata ta6a ganinsa cikin fara'a haka ba. Mai yiwuwa saboda farincikin bikin dan uwansa ne. Jin da tayi ana ihu da shewa daga falon ne yasa ta saurin mikewa itama ta samu dama dakyar tana lek'e. Turare ta gani wata tsohuwa cikin wadanda suka zo daga Adamawa tana ta fesawa Ango da Amarya. Masu hoto suna faman yi, Faruk na daga hannun kujera zaune agefen wata mace da bata fi shekaru ashirin da bakwai ba, wacce itama cikin bak'in Adamawa take. Sai hira sukeyi suna dariya. Sunyi kama kwarai, kana gani ko ba'a fada ba kasan jini d'aya suke. Haka dai aka gama hotuna, Ango Haidar da tawagarsa suka fita. Wannan karon banda yayyun Haidar da Faruk, su kam zama sukayi ana gaisawa da hira da 'yan uwa. Tana ji anata yiwa Faruk tsiya akan shima ya dace yayi aure, abin banda dariya babu abinda yake ba shi, domin shi dai har kawowa wannan lokacin bai ga matar da ta kwanta mishi a rai ba har yakejin cewar zai iya aurenta. Duk cikin masu nuna masa kauna da so, duk cikin masu yi kishi tallar jikkunansu batare da sun buk'aci ko sisinsa ba, babu wacce ya ta6a yiwa kallon rahma. Asalima wannan d'abi'ar gaba daya haushi take ba shi wai ace mace ke tallatawa namiji kanta, yana daukar hakan a matsayin rashin aji da sanin darajar kai.
   Dakyar ya samu ya silale ya fito daga falon, Ummi ta bi bayansa da kallo sannan ta maida hankali ga tsoffin dake faman shige da fice suna rabon abinci.
  "Ummi." Ta ji muryar Amina a kanta. Wani sanyi ya mamayeta, ko babu komai zata samu abokiyar hira. Ta zaro ido tana murmushi.
  "Anti, kinga kuwa yanda kikayi kyau? Masha Allah." Ta harareta kadan
  "Lallai ma Ummin nan, wallahi ban kaiki ba, kinga yanda kikayi kyau kuwa yau?"
  Ummi ta girgiza kai.
  "Ban kaiki ba Anti."
Amina ta dara gami da jan hannunta.
  "Taso mu zagaya baya, tun dazu ai ina can."
   Ummi ta mike suka zagaya. Babban fili ne mai shuke-shuke, nan dinma akwai mutane saidai ba kamar cikin gidan ba, kusan ma yanmata sunfi yawa anan. K'asan wata bishiya suka zauna asaman kujeru inda wasu yara biyu da Mace rike da yarinya wacce bata fi watanni uku ba suke zaune. Ummi ta hango kamannin matar sosai da Amina, hakan yasa ta gaisheta, cikin sakin fuska itama ta amsa. Amina ta dubi yaran.
   "Ahmad, ja  Kulsum ku tafi wasa Antinku ta zauna."
  Ba musu yaron ya amsa sannan ya mike suka bar wurin, daman sun k'agu su tafi wasansu amma ta hanasu da cewar sai sun ci abinci.
   Bayan sun zauna Amina ta kalli 'yar uwarta wacce daga ita sai ita a haihuwa.
  "Anti Hauwa, wannan itace Ummi da nake baki labarinta. Ummi wannan itace yayata Anti Hauwa, daga ita sai ni a wajen Innarmu. Babbar yayarmu Anti Fiddausi tana Katsina, acan take aure. Yaranta biyu, da Kulsum da kuma wannan bebin, Anisa. Ahmad shine auta wajen Innarmu."
  Bayan ta kai aya, Anti Hauwa ta sanya dariya.
  "Toh 'yar jarida, oh Amina." Ta karashe tana kama ha6a, abin sai ya bawa Ummi da Amina dariya.
   Anti Hauwa ta dubi Ummi fara'arta ta k'aru don kuwa babu abinda Amina ta 6oyemata dangane da Ummi.
  "Sannu Ummi, fatan kina lafiya?"
Ummi ta gyada kai gami da sakin kyakkyawan murmushinta.
  "Lafiya kalau Anti. Ya wajen su Inna?"
  Abin ya yiwa Anti Hauwa da Amina dadi.
  "Inna tana lafiya, taso ta zo amma matar kaninta bata ji dadi ba, ta je dubota. Watakil daga can tayo nan."
  Ta gyada kai gami da yi mata fatan samun lafiya.  Nan kuma hira sosai ta 6arke tsakaninsu. Anti Hauwa da Amina suka gangaro kan batun Saurayin Aminan, Bello wanda ya matsa akan shi zai turo magabatansa. Anti Hauwa ta bata shawara akan ta sanarwa Inna idan yaso sai a had'ashi da wani ya rakashi har can Nijar su gaisa da yan uwan mahaifinsu.
  Haka suka tsayar da shawara.
  Sun wuni tare, Anti Hauwa sai bayan la'asar ta bar gidan, Hajiya Mama harda bata kudi tayi na mota. Dakyar ta kar6a don mutunci da karamci irin na Hajiya Mama har yana so yayi yawa, mace ce da babu ruwanta. Harda kayan rabo ta had'a ta bata, ta sanya aka yiwa Inna (takeaway) na abincin biki tace ta kai mata domin ba wani nisa ne tsakanin gidansu Inna da gidan Anti Hauwa ba. Ta kar6a da godiya.
  Tafe suke gaba dayansu da Anti Hauwa da Ummi da Amina, wadanda suka yo mata rakiya don ta samu abin hawa, kasancewar babu laifi akwai 'yar tazara tsakanin gidan da babban titi. Ummi na rike da Anisa wacce ke faman kalle-kalle idanunta tarr a bud'e. Yarinyar ta shiga ranta, haka kawai ta ji tana kaunarta ko don bata ta6a ganinta rik'e da yarinya k'arama haka bane? Oho.
   A farfajiyar gidan, samari ne da d'aid'aikun yanmata suna hira, daga ganinsu kaga yan uwan juna. Suka wucesu suka fita.
   Suna tafe suna hira a haka har suka iso titi, bayan sun samarmata d'an sahu, ta shiga sukayi sallama. Ta dubi Ummi da murmushi mai bayyana hakora a saman fuskarta.
  "Toh Ummi, sai na ganki a gidana wataran ko?"
  Ummi ta amsa da toh tana maida martanin murmushin. Suka juya tare da Amina suka kama hanyar komawa. A hanyar ma hira sukeyi, Amina na yi mata korafi akan ita ko dan fita unguwa bata tambayar Mami ne? Ummi ta ta6a baki kadan.
  "To Anti wa nake da shi a garinnan?"
  "Kina da mu, wataran ki tambayeta kizo na kaiki wajen Innarmu ku gaisa."
  Murmushi Ummi tayi wanda yayi daidai da giftawar wata farar honda mai bakin gilasai ta gabansu.
  "Wannan kamar motar gidan su Alhaji." Cewar Amina kenan. Ummi da batasani ba ta bi motar da kallo kawai wacce ta koma tafiya sannu-sannu tamkar matuk'in baya so. Kafin daga bisani ya fisgi motar ya k'ara gudu.
  Ai kuwa kamar yanda Amina ta fad'a haka dinne, don suna isa kofar gidan suka iske motar a fake, na cikin motar baikai ga fitowa ba saidai kafarsa d'aya da ya fiddo waje. Ta madubin hannun kofar, Ummi ta hangeshi. Kansa a jingine jikin kujera yana amsa waya. Akayi katari suka had'a ido, gani tayi ya yafito ta da hannu. Abin ya bata tsoro, gabanta ya hau dukan tara-tara. Tayi saurin dauke idanunta don bata gaskata hakan ba.  Har zasu shige ciki ya danna hon.  Wannan ya sanyasu dakatawa.
   "Da ku ake." Cewar Maigadi. Amina ta dubi motar, saidai bata hangi ko wanene ba sakamakon duhun gilashin. Suka zagaya suka isa ta mazaunin direba, idanunsa akansu, suka durkusa a ladabce suka gaisheshi. Yaya Faruk ya dago kanshi ya dubesu da idanunsa masu tafiya da dukkan wata diya mace mai lafiya da zata kalleshi. Ya gyad'a kai kafin ya maida dubansa cikin motar, hannu yasa ya janyo leda bak'a babba ya mik'awa Ummi.
  "Ki mik'awa Hajiyata." Ta sanya hannunta dake faman rawa don gaba daya wani kwarjini yayi gareta, ta kar6i ledar wanda bisa kuskure hannayensu suka gogi juna har ta gogi tattausan gashin dake kwance a hannunsa, a gigice ta dauke hannunta had'i da kar6ar ledar tana mai amsawa da toh wanda bai fito sarari ba saidai kawai le66anta da ya nuna alamun hakan. Baice uffan ba har suka fice ya bisu da kallo, ya lura yarinyar kamar a tsorace take da shi. Ya dan ta6e baki cike da mamaki, mamakin bai wuce na ganin yara kyawawa haka ba ace wai suna aikatau ba karatu ba, tabbas ya tausayamusu. Ya kuma raina iyayensu wadanda tunaninsa yafi ba shi cewar kwadayin abin duniya ne kawai yasa suke sakin yaransu sakaka suna yawon gidajen mutane don bauta da neman kudi wanda duk yawan abinda zasu samu bazai haura dubu goma ba, aganinsa wannan cutar da rayuwarsu ce kawai. Ya lumshe ido, ya jima a haka kafin ya maida kafafunsa ciki ya rufe kofar gami da yin ribas yabar unguwar.
             
   Acan kuwa Ummi kasa shiga ciki tayi haka kawai bata son shiga cikin mutanen gidan, tana jin nauyinsu. Amina ce ta kar6a ta mik'awa Hajiya Babba sannan suka koma inda suke. Sai misalin karfe bakwai kowa ya soma shirin tafiya wajen (Party) wanda Ango ya shirya na musamman da iyayensu da yanmata da samari. Abin har ya bawa  Ummi mamaki, aganinta wannan kawai rashin sanin abinda za'ayi da kudin ne, ko kuma dai kudin ne suka yawaita garesu. Tana gani Amina tayi mata sallama suka wuce sakamakon yara da zata kula dasu a gida kafin dawowar Hajiya Maman. Ummi ta dubeta.
  "Nima na tabbatar yanzu zamu wuce ko don Ramma."
  "Wace Ramma? Ramma ai ta tafi gida tun dazu tare da su Hajiyar Iklima. Baki ga su Iklima sunzo dazu ba?"
  Ummi ta zaro ido.
"Aa banma gansu ba wallahi, na tabbatar Mami ta manta ne da ta had'a tafiyata da su. Toh yanzu wa zan bi?"
Amina ta jinjina kai.
"Mamin ce zata barki ki tafi da kishiyoyinta? Wasa kike ma. Na..."
  "Ummi, kizo inji Mami." Suka tsinci muryar Fahad wanda yayi sanadin katse Amina daga maganarta. Ta dubeta.
"To saida safe, nasan kuma mu da kara haduwa ba yanzu ba." Sukayi sallama Amina ta wuce.
  Ummi tana d'ari-d'ari haka ta daure ta shiga falon, Mami na daga zaune wata tana d'aura mata d'ankwali.
Ta gaida mutanen falon sannan ta koma gefen Mami.
  "Gani Mami." Mami ta dan dubeta.
"Ramma ta riga ta tafi, nikuma da wuya idan zan dawo ta nan gaskiya don gaba d'aya zamu tafi can wajen party, ki zauna a inda zan ganki idan mu  fito."
  "Toh Mami."
  Daga haka tayi gaba, tana ji wata tana zolayar Mami wai da alama ita bata iya rayuwa saida 'yar aiki, har sauran suna dariya. Suna tsokanarta wai sai kace itace autar innartasu.
    Ummi ba haka taso ba, don alal hakika ita zuwa wajen wani party ko waje mai hayaniya baya burgeta, da ace Mami zata barta anan da ta zauna har zuwa lokacin da zasu ci su cinye su dawo su tafi. Ta dubi jikjnta bayan wucewar wasu yanmata da suka dauki ado cikin wani leshi yellow da nadin kai ja, ta yaya ma zata shiga taron jama'a da kayan nan? Ta tabbatar ita kadai zata bambanta acikinsu. Ta langa6ar da kanta, kodayake daman ita din ba kowa bace face 'yar aiki. Bata da wani daraja, babu wani wanda zai ra6eta da sunan kauna ta jini ta yan uwantaka, shiyasa take matukar kaunar Amina, ta tabbatar su Amina  suna kaunarta saidai bata da sa'ar 'yan uwa. Batasan halin da suke ciki ba a yanzu, da ace ma zatasan dangin mahaifiyarta, lallai da ta kai kanta garesu komin nisan dake tsakaninsu. Ta sauke ajiyar zuciya kafin kuma da saurinta ta share hawayen da suka zubomata.
  Ko mintuna biyar batayi ba awajen, Mami ta aiko kiranta, kaya ta dunga kwasa tana kaiwa boot din motarsu, sannan ta zauna a motar tare da Fahad da wasu iyaye matan, Mami na fitowa suka wuce wajen party.
     Tun a farfajiyar otel din Ummi tayi bala'in raina kanta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da sakin baki galala tana kallon yanda wajen ya k'ayatu, anyiwa wajen adon fulawoyi wadanda sai buso sanyi sukeyi, hakanan kuma wajen sai kamshi yakeyi. Daga can ciki kana jiyo tashin kid'a. Wadanda basu shiga ba suna tsaitsaye a farfajiyar wajen. Haka suka dunguma zuwa ciki. Sanyi ba bak'on Ummi bane don tun bata saba shan sa ba a falon Mami, har ya zamana yanzu ta saba. Wajen kowa ya dauki kwalliya. Matasa masu ji da ilimi da gayu sai kuma iyaye wadanda kallo daya zakayi musu ka tabbatar cewa kud'i sun riga sun gama jik'asu. Zugwui-zugwui take bin bayansu Mami, gaba dayanta a d'arare take, gani takeyi kamar kowa awajen ita ya zubawa ido. Idanunta suka cika da kwalla, bata saba da irin haka ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji an damki hannunta. Ta juya da sauri, Ihsan ta gani ta ci ado har ta gaji da haduwa, saidai fuskarta a murtuke. Bata ce mata uffan ba ta soma janta, gaban Ummi na faduwa haka ta bi bayanta har zuwa d'an (Corridor) na shiga dakin taron.
  "Uban wa yace ki shigo? Kalleki kiganki, typical 'yar kauye, wallahi kika yi kuskuren shigowa wajennan sai na miki wulakancin da baki ta6a zato da tsammani ba. Shegiya kawai marar galihu!" Daga haka ta ja tsaki tayi gaba ganin mutane sun nufo hanyar shigowa. Ummi kuka ya taho mata, da saurinta ta juya zata fita, ta bawa mutanen hanya suka wuce ta bi ta gefe ta fita da gudu-gudu. Kai tsaye ta wuce bayan motoci inda babu  mai ganinta ta durkushe ta soma kuka mai shiga rai. Kuka sosai takeyi, lallai ta k'ara gaskata cewar halayen DAN ADAM sun bambanta. Ta gaskata cewar ita din ba wata bace face marar galihun kamar yanda Ihsan ta jaddada mata. Kaiconta! Kaicon rayuwarta! Ace mahaifinka ya bude baki yayi furucin cewa ko bangon duniya za'a kaika, ba matsalarsa bace, baka da wani makusanci mai kaunarka, daga dangin mahaifin harma da shi kansa mahaifin. Takan rasa abinda ta yiwa mutane, wai meyasa dangin mahaifiyarta bazasu nemeta ba? Ta tabbatar koda duniya ta k'i ta, su bazasu ta6a gudunta ba, ta tabbatar zasu bambanta da sauran 'yan adam din da ta sani kuma ta rayu da su. Tana fatan su zamto irin Amina da su Anti Hauwa, tana fatan su zamto masu nunamata so da kauna ta gaskiya.
   K'arar rufe motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa a firgice. Ido hud'u sukayi, kallonta yake cike da tsantsar mamaki, yayinda ita kuwa take mishi kallo tamkar wacce ta ga wani dodo. Gaba d'aya tsoro takeji kada ya bud'emata wuta akan me takeyi anan. Ta sunkuyar da kanta tana duban motar, sai lokacin ta lura cewa motar da suka ganshi dazu a ciki ce.
  Kamar yayi mata magana, saidai ya fasa ya juya ya soma tafiya. Ta mike ta bar wajen ta soma tafiya kai tsaye ta nufi k'ofar fita daga Otel din. Kamar ance ya juyo, ya ganta.
   "Ke!"
Ya fad'a a sannu yanda yasan zata ji don ba wani nisa tayi ba. Ta juya gabanta na fad'uwa. Sai lokacin ta lura da shigarsa, ya had'u karshen haduwa, a yanzun yana sanye da shadda ruwan kasa mai duhu wacce aka yiwa dinkin da ya zauna daidai a jikinsa. Takalmi da hular da ya dora ma su kansu abin a kalla a k'ara kalla ne. A haka har ta karasa wajensa ta durkusa. Ya bata umarnin ta mik'e. Bayan ta mike ya kare mata kallo sannan ya jefota da tambaya.
  "Ina zaki?"
  Ta soma rawar murya.
  "Gi..da." Ya yamutse fuska.
  "Ke kika kawo kanki?"
  Ta girgiza kai.
  "To shiga ciki."
  Tunanowa da maganar Ihsan yasa ta soma zubar hawaye ta dubeshi da jajayen idanunta wadanda kuka ya maidasu hakan, sai lokacin shima ya lura da su.
   "Kayi hakuri Yalla6ai, bazan iya shiga ba."
  Shiru ya biyo baya ayayinda ya kafeta da ido yana kallon fuskarta. Haka kawai sai ya ja guntun tsaki.
  "Akan wane dalili?"
"Ih..ih.san tace kada na shiga zata wulakantani."
   Ya ji wani abu a ransa, sai kuma ya cije le66ansa na kasa.
  "Ko menene ku kuke jawowa rayuwarku, da ace kun hakura da yanayin rayuwa, kun godewa kad'an din da kuke samu a gidajenku, da babu abinda zaisa kuzo ana wulakantaku ana baku tamkar wasu karnuka."
  Batasan sadda ta cigaba da 6ul6ulo da ruwan hawaye ba. Ta so tayi shiru ta barwa zuciyarta amsa, saidsi ta tsinci kanta da kasa aikata hakan.
   "Ka gafarceni Yalla6ai, saidai akwai lokutan da ba'ason ran mutum yajr aikata abinda ya aikata ba. Akwai tilastawar rayuwa, wani ba shi da yanda zaiyi ne, sai yaga da yaje ya aikata abin turr gwara ya gwammace ya rufawa iyayensa da kansa asiri ta hanyar nema ta halal. Wani kuwa, rashin gata da rashin samun kulawar yan uwa ke sanyashi tsintar kai a halin da yake ciki. Kowane bawa da yanda Allah Ya tsaro rayuwarsa, ba mu muka za6awa kanmu wannan rayuwar ba. Akwai KADDARA."
  Daga haka ta juya da sauri-sauri ta bar wajen gami da nufar get, batayi wata-wata ba ta fice daga wajen batare da tasan inda ta nufa ba, burinta kawai tabar wajen ko ranta zaiyi sanyi....!
 

Dan Adam 6

A kwana a tashi ba wuya a wajen Ubangiji, har ga shi ana sauran kwanaki hud'u bikin Haidar da Intisar. Wannan ya janyo Ihsan komawa gidan Hajiya Mama don taya 'yar uwarta shirye-shirye. Alokacin tuni su Hajiya Babba sun iso Kano don anan za'a yi sha'anin bikin kasancewar mijinta, Gen. Ahmad Danzaki, uba ga su Usman, shima dan asalin Kano ne.
    Mami ta yiwa Ramma da Ummi kyautar atamfa turmi d'aya na anko. Ramma ta had'a ta kai musu dinki wanda ya zauna d'as a jikinsu. Ana washegari za'a soma biki, suka ziyarci Hajiya Mama wacce ke fama da shirye-shirye. Amina ta ji dadi kwarai na ganin Ummi. Anan gidan Mami ta barta tare da Fahad suka fita zuwa babban shagon siyar da kayayyakin kicin, hakanan su Ihsan suma sun fita wajen gyaran Amarya.
  Ummi ta dubi hannun Amina da suka sha kunshi.
  "Anti na kasa dauke ido daga kunshin nan naki wallahi, yayimin kyau sosai."
   Amina fuska a sake ta amsa mata sadda take gyara zaman tsintsiyar hannunta wanda take shirin yin shara.
   "Idan kina so muje na rakaki sai na dawo, wallahi yarinyar ta iya kunshi, baki ganta ba kuma ba wata babba ba."
  Ummi ta zaro ido, ga koshi ga kwanan yunwa.
  "A'a, banason fad'an Mami, idan suka dawo basu tarar da ni ba ai nasan ba zata kyaleni ba."
  Amina ta dara kadan. "Kedai akwai matsoraciya, ni na fadamaki har babban gida sai sun shiga tunda Gwaggo ta zo (surukar Mami kuma yar uwar mahaifinta). Na tabbatar su da mu gansu a gidan nan sai Magriba. Bari nayi shara na rakaki, keda kike fara tas ma ai sai ya fi yi miki kyau a kaina."
   Ummi tayi tsuru da ido bata kara cewa komai ba, tana kallo Amina ta kammala share tsakar falon, ta wanko hannunta sannan ta yafa gyale.
  "Muje."
  Ummi ta girgiza kai.
  "Ai baki isa ba, tunda har kina so wallahi sai kinyi, saidai wani ikon Allahn ya hana. Idan kudin kike ji, kada wannan ya dameki, zan biya."
  Dakyar ta shawo kanta ta amince suka tafi. Babu nisa sosai, saida Amina ta ga an soma yi sannan ta taho bayan ta rok'i alfarmar mai kunshin akan ta sanya a raka ta gida. Ba wani mai yawa akayi mata ba, saidai duk kushen mai kushe bazai kalli hannu da kafafun Ummi ba ya ce baiyi kyau ba. Bak'in lalle ne, hakan yasa babu jimawa sosai ya bushe adalilin iskar dake kad'awa. Ta wanke a gurguje, alokacin anyi sallar la'asar, gaba daya fargabanta bai wuce na kada ya zamana su Mami sun dawo ba. Saidai cikin ikon Allah daga su Mamin har su Intisar babu wanda ya dawo. Amina ta rude ganin yanda Ummi tayi kyau.
   "Kai amman lallen nan yayi miki kyau sosai masha Allah, sauranki kitso."
  Ummi ta murmusa.
"Anti nikam banason kitso wallahi bansan dalili ba."
  Amina ta harareta kad'an.
"Eh mana, don kinga kina da gashin ne ai, amma idan kana da kyau saika k'ara da wanka. Gashinan yanzu kunshi yasa kin fito a Mace."
  Sukayi dariya. Koda Ummi ta idar da sallah, tare suka shiga kicin tana kallon yanda Amina ke had'a girke-girke. Abin sai ya bata sha'awa matuka, don duk iyakar girkinta a gidan Mami, bai wuce dahuwar kwai da indomi ba. Amina ta bata shawara akan ta k'ara zage damtse wajen lura da yanda su Mami da Ramma ke girke-girke. Anan suka shantake wajen hira, har Amina na labarta mata batun wani saurayinta wanda shi kadai take saurara, har a yanzu haka ya soma matsawa da batun turo magabatansa.
   "Allah Sarki, toh Anti ki ba shi dama mana."
  Amina ta murmusa.
  "Ba anan matsalar take ba, dangin mahaifina ne abun ji, kina ganin yanda suka wancakalar da lamuranmu, ina gudun kada azo a samu matsala ne."
  Ummi ta gyada kai.
  "In sha Allah babu abinda zai faru, ki gwada ba shi dama."
  "Ai ko na k'i ko na so babu yanda na iya, tunda dai ina kaunarsa haka kuma Innarmu ta ba shi wannan damar har ta sanar da ni muddin ya kara tuntu6arta da maganar zata kwatanta mishi gidan su Mahaifina, kinga kuwa ai bani da ta cewa sai addu'a."
  "Gaskiya kam, Allah Ya yi miki za6i."
"Amin, bari mugani, idan banyi lattin gama dahuwa ba, zan kaiki ki gaida Inna."
  Wani sanyi ya mamaye kirjinta.
"Toh Anti."
   Ba haka suka so ba, don lokaci k'urarre suka kammala, alokacin kuma Mami suka dawo, duk da haka ba su bar gidan nan ba sai bayan Isha'i, wannan yasa Amina yi mata alkawarin duk randa suka k'ara zuwa zata yi kai ta.  Koda Mami ta ganta da kunshi babu abinda tace, illa iyaka ta tambayi yanda ta samu kudin, ta shaidamata Amina ce ta biyamata, daga wannan bata k'ara uffan ba.
   Washegari ya kama ranar  Kamu wanda za'a gabatar a wani tsadadden dakin taro wanda ake ji da shi sosai a birnin Kano, wajen da sai wane da wance. Tun misalin karfe uku na rana, dakin Mami kaf suka shirya, a ranar ma Ummi ta kara fashin makaranta wanda ko kadan ba haka ta so ba, saidai tasan Mami ba barinta zatayi ita d'aya. Daya cikin kayan da aka dinkamata tun farkon zuwanta ta sanya don kuwa Ramma ta sanar da ita cewa sai ranar yini za'a sanya anko.
   Tsari da kwalliyar wajen ya burgeta kwarai, banda wak'a babu abinda kakeji yana tashi a filin taron, waka marar sauti sosai, acikin nutsuwa akeyinta. Har shagala tayi wajen kallon gogaggun yan boko mata wadanda suka ci ado har suka gaji, sai faman fara'a suke kowacce na harkar gabanta. Tana nan zaune tana rarraba idanu, ta ji an dafa kafadarta. Amina ta gani, suka washewa juna hakora, haka kawai itama Ummi ta tsinci kanta da tsantsar farinciki kai kace bikin wani nata akeyi. Amina ta ci kwalliya kamar ba ita ba duk ta chanja.
   "Kedai Ummi kina da ban haushi, bansan meyasa bakyason gyara fuskarki ba wallahi, kalli dai yanda yanmata suke cakarewa, amma ke inaga ko hoda bakya shafawa, kodai baki da ita ne?"
  Ummi tayi dariya har hakoranta suka bayyana a fili.
  "Anti nida ban iya kwalliyar ba?"
  "Ai ba lallai sai kinyi mai zafi ba, ko hoda kadai kika shafa kika saka jan baki mai kala a le66anki ya wadatar, ji yanda kika hadu, wallahi da ace kina kwalliya na tabbata sai kin fi haka."
  Ummi ta rausaya ido tana dariya.
"Ko?" Suka dara gaba d'aya.

   Babu jimawa sosai Amarya ta iso filin da Angonta. Baki bud'e Ummi ta dubi Amina, alokacin wuri ya hargitse, k'arar kid'a ya yawaita da ihun mutane da masu daukar hoto. Ta so ta tambayi Amina daman namijin na zuwa kamu? Saidai babu damar hakan sakamakon hayaniyar da tayi yawa awajen, sunyi kyau matuk'a. Gaba dayansu fararen kaya suka sanya, Haidar cikin farar shadda, yayinda itama Intisar ta had'e cikin shadda dinkin doguwar rigar da ta sha aiki. Su Ihsan da sauran kawayen Intisar suna take musu baya, hakanan shima ango, abokansa na Abuja da na nan Kano kalilan cikinsu sun samu halara, yayinda wasu suka barwa gobe daurin aure. Ba anko sukayi ba, saidai shadda brown kowannensu ya saka, na wani yafi na wani turuwa.
   Sunyi kyau kwarai, sai kirari ake yiwa Ango da Amaryarsa har suka isa mazauninsu. Duk raba idanun Ummi bata ga yayyun Haidar ba da kuma Faruk. Har akayi nisa da sha'anin, mata ne kawai da daidaikun matasan wajen wadanda dukkansu yan uwansu ne na Adamawa sai kuma yan uwan mahaifin Haidar Danzaki da ma'aikata.
   Sun jima sosai a wajen, an ci an sha, har saida aka kusan tashi sannan ta hangi mota ta faka daga can gefen na amarya da ango. Su biyar ne suka fito daga motar, Yaya Ridwan ne sai wasu wadanda suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad'arsa. Har aka tashi daga wajen babu Faruk da Babban Yaya.
     Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta chanja sutura ta kwanta.
                      ☆☆☆

Dan Adam 5

Wannan karon a kan kujera ta sameta tana amsa waya. Zama tayi har ta kammala sannan tayi magana.
"Gani Hajiya." Ta dubeta a nutse sannan ta soma magana.
  "Yauwa Ummi, dafatan dai Amina ta nunamaki dukkan ayyukan da takeyi? Toh inaso ki zamo mai rike amana, muddin kika ci amanata, bazan kyaleki ba. Yanda zan rik'i amanarki da gaskiya a matsayinki na Amanar a hannuna, haka kema nakeso ki rike, ki kula da dukkan ayyukan da zaki dunga yi."  Ta k'ara karanto mata ayyukan harma da na gyaran sashenta ciki da falonta na biyu, banda wannan da suke ciki don duk cikin aikin Ramma ne. Ta k'ara jaddamata cewar batason k'azanta, hakanan ta kiyaye tsaftar suturunta, duk sadda zatayi wanki, ta tambayi omo zata samu. A dai maganganun Hajiya, Ummi ta fahimci cewa dagaske batason k'azanta kuma tana da kyankyami.
   Ta rausaya kai.
"In sha Allahu Hajiya zan zama mai kula da dukkan abinda kukace, nagode Allah Ya k'ara girma da arziki."
Har a ranta ta ji dad'in maganganun Ummi.
  "Shikenan kina iya tafiya."
                       ☆☆☆
   Tun daga wannan ranar, Ummi ta kama aikinta sosai, Amina na taimakonta. Har ya kasance wani sa'in kafin Amina ta tashi, ta rigata tashi. Tana jin dad'in zama da Amina saboda shawarwarin da take bata, har karatu tana koyamata. Duk da cewar Amina na cin wuya don Ummi ko bak'i bata iya ba. Duk sai ta bata tausayi, haka take lalla6awa ta biyamata, amma ta tabbatar muddin tana wajen Hajiya Madina, bazata ta6a bari ta zauna mata da jahilci ba, duk wadanda suka ta6a zama sukayi aiki awajenta, ba wacce bata sanya a islamiyya ba, boko ne dai ba lallai ka samu ba.
     Saida Ummi tayi sati da zuwa, sannan Amina ta soma shirin tafiya don Hajiya Mama sun dawo. Gaba daya ta ji babu dadi, tana zaune gefe tana duban yanda take ninke kayanta tana sanyawa ciki jaka. Amina ta ankara da duban da takeyi mata, itama sai taji batason rabuwa da ita.
  "Haba Ummi, menene abin damuwa har haka alhalin muna gari d'aya? Karki damu, na tabbata zamu dunga ganin juna. Kedai ki cigaba da hakuri da zama da su tsakaninki da Allah."
   Ummi ta gyad'a kai.
"Toh Anti." Sai yamma suka tafi har Hajiya da su Adnan, gidan ya rage Ummi kad'ai da Ramma. Bayan ta kammala ayyukanta ta fito farfajiyar gidan tayi zamanta. Bata kai mintuna biyar a zaune, budurwar da bazata ta6a mance fuskarta ba wacce suka samu sa6ani da Adnan a farkon ganinta da su, ta fito daga sashensu tare da k'awayenta har su biyu suna dariya.
   Hararar da ta sakarmata ne yasa ta dauke kanta babu shiri ta saddar a k'asa, ta gabanta sukazo wucewa, ai kuwa ta sanya takalminta mai tsini ta take yatsun k'afarta har saida tayi k'ara. Ta juyo ta rankwasheta.
"Munafuka, sharri zakiyimin kina gidan ubana kina cin arziki? Shegiya kawai."
  K'awayen dariya kawai sukayi, d'aya tana fad'in "Kai Iklima baki da kirki."
Iklima ta ta6e baki.
  "Na kaiku?"
Suka fice Ummi ta mike da sauri tabar wajen, saida ta tsaya a lungun ta share kwallah sannan ta k'arasa ciki. Ta zauna a kicin tana kallon yanda Ramma ke faman had'a miya, tana dan jan Ummin da hira har ta share batun Iklima ta saki jikinta.
                      ☆☆☆
 
      Bayan tafiyar Amina, Ummi dole ta sabarwa kanta hira da Ramma, don Ramma mace ce mai abin dariya. Ayyuka ko kusa basu bata wuya sosai don a ganinta ta saba da fin haka acan gidansu. Sau da yawa takan tuna Mahaifinta, tana tunanin ko wane hali yake ciki yanzu, saidai daga zuciyarta ta tunano mata irin tsana da tsangwanar da take sha a wajen shi kansa, sai ta ji tunanin ya kau.
   A d'an zaman da sukayi da Hajiya Madina ta fahimci Ummi lallai bata da wani ilimi da addini, ta lura ko sallolinta akwai gyara ciki, wannan dalilin ne yasa ta sanya Ramma kaita makarantar da yaranta(ita Rammar) ke zuwa, karfe biyu suke zuwa su taso k'arfe biyar na yamma. Babu ruwanta da shiga sashen kowace matar gidan don sosai ta dauki gargadin  Hajiya Madina, hakanan tana rike da nasihar Antinta. 
   Alokacin Hajiya Lubna amaryar gidan sun dawo daga Maiduguri, ta lura yaranta suna da kirki basu da hali irin na yaran Hajiya Binta. Saidai uwarsu ce sai a hankali, mace ce mai shan k'amshi, saika gaisheta sai ta ga dama take amsawa.
  Maigidan ma bai rufe sati biyu ba ya dawo. Ranar da ya kasance Hajiya Madina ce da aiki, sun ci aiki sosai, har da Hajiya Madinar. Ummi banda wanke wannan mik'o wancan babu abinda takeyi. Abinci kusan kala uku ta ga anyi ciki harda suyar kaza bayan an tafasa an tura shinkafa da kayan hadi a k'asanta an toshe bakin da dankali babba guda d'aya. Sai lemun zo6o da taga sun had'a sai kamshin abarba yakeyi. Aka kammala aka zuzzuba, suka ajiye a saman tebur. Ummi da Ramma suka tattara kicin din, can bayan magriba, lokacin Ramma ta tafi, sai ga Hajiya Madina ta fito daga dakinta ta ci ado cikin wani (yellow lace) wanda ya sha adon duwatsu, tayi kyai sai k'amshi kawai ke tashi a jikinta.
  Ummi na  rak'u6e a can gefen kofar kicin tana kallon wani fim na yak'i da su Adnan suka nutsu suna kallo.
  "Wow! Wallahi Mom kinyi kyau."
Cewar Ihsan tana mikewa tsaye, daga ita sai riga iyaka gwuiwa da riga tshirt kanta hula ce ta sanya. Ta isa ga Mamin tana mai sanya hannu ta k'ara gyara mata zaman d'aurin. Murmushi kawai Hajiya Madina tayi.
  "Naji, taho ki kaimin kayannan sashen Abbanku."
  Ihsan tayi dariya.
Tare suke fice ta dauki wasu Ihsan ta dauki sauran. Ummi ta bi Hajiya Madina da kallo cike da sha'awa don kwalliyar ta burgeta. Idan kana da kudi babu abinda ba zakayi ba.
     Har ta gaji da kallon, ta koma daki ta hau duba karatunta, a karshe da ta gaji, kwanciya tayi abinta wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita don bata ta6a aikatuwa irin na yau ba saboda girkin dawowar Alhaji da ta taimaka da shi.
        Bayan kwanaki biyu da dawowar Alhajin, ranar juma'a bayan ta je ta gaida Hajiya. Hajiya ta dubeta a nutse. Doguwar bakar abaya ce jikinta na wajen Amina.
  "Wai ke baki da kaya ne sai wadannan guda ukun? Yau idan kin saka doguwar riga bak'a, gobe sai jan atamfa kodadde, jibi ma haka? Bakizo da kaya bane ba?"
   Ummi ta sunkuyar da kai gaba daya jikinta yayi sanyi, cikin rawar murya tace.
"Eh su kadai ne masu d'an dama-dama Hajiya."
   Hajiya tayi shiru da mamaki, kafin tace. "Daukomin duka kayanki nagani."
  Ta mik'e da sauri ta cika umarninta, Hajiya ta sanyata ta zazzagesu. Kayan duk ba wani na kirki kam da gaskiyar Ummin.
  "Kwashesu ki maida ledar, kada su koma wannan d'akin. Fita kimin kiran Ramma."
  Ta amsa da toh, ta mayarda kayan jaka sannan ta fita ta kira Ramma. Tana ji Hajiya tace idan ta kammala tayi magana zata bata kudade gobe ta shiga kasuwa ta siyo mata kananun atamfofi guda hud'u sai dogayen riguna yan kanti su kuma guda uku sai wanduna da vest guda shida-shida. Ramma ta amsa da toh, zata mike Hajiya ta dakatar da ita.
  "Tafi da wannan ledar a zubar don Allah." Ramma na dariya ta dauka tayi gaba tana fadin toh.
    A washegarin kuwa Ramma bata zo da wuri ba sai wajen sha d'aya na safe. Sai gata da kayan da Hajiya ta umarceta. Hajiya ta duba sannan ta bata atamfofin ta kai dinki, tayi kiran Ummi ta mik'a mata ledar kayan ta kara jaddada mata cewa ta kula da tsaftar jiki da dakin da take kwana. Ummi ta amsa tayi godiya ranta fari k'al ta zubawa Hajiya ruwan addua wanda hakan ba k'aramin faranta Hajiya Madina yakeyi ba. Saida ta shiga ta zazzage kayan tana duba, ai kuwa dai abinda Hajiya ta karanto shi d'in aka sissiyo harma da k'arin man shafawa da turare (Lovilla) na roba. Har wani tsalle tayi na murna, ko babu komai a makaranta yan ajinsu zasu dinga jin tana k'amshi kamar yanda ta ga yan babban aji a makarantar suna yi idan sunzo giftasu ko kuma monitoci.
                    ☆☆☆
   A wani yammacin Alhamis, Ummi na zaune a tsakar gida tana taya Ramma goge ku6ewa, Hajiya ta fita zuwa asibiti, k'aramar 'yarta wacce ta aurar a karshe tana nak'uda, wato Aisha.  Ihsan da Adnan suka sanyo kai, Adnan na daga gaba a guje yayinda Ihsan ke binshi a baya itama a guje tana rok'on ya ara mata wayarsa. Dariya yakeyi ya juya gareta.
   "Ai baki isa ba, sai na rigaki jin kukan bebin."
  Su dai kallonsu kawai sukeyi. Ramma tayi dariya.
  "Oh, wai kada dai kucemin har Aisha ta haihu?"
   Adnan na dariya alokacin da yake danno lambar Maminsa, ya bata amsa.
  "Ta haifi d'anta namiji yanzu Mami ke gayamin."
  Ai sai Ramma ta kara washe baki.
"Kai Alhamdulillah."
  Ummi dai na kallonsu, ita har mamakin Ihsan takeyi, fara'arta ga yan uwanta ne kawai amma ba dai ga ita ba. Batasan meyasa  take d'asawa da Ramma ba, sune dai bata ta tasu.
  Adnan bayan ya yiwa yar uwarsa murna, ya bawa Ihsan don ta dameshi da rok'o. Nan fa ta cika musu kunne da ihun murna, ya warce wayarsa.
  "Kingani ko? Ai ke wata shashasha ce wallahi, a komai bakya yin na hankali shiyasa ma nak'i baki."
  Tayi mishi gwalo bayan ta saita kafarta zuwa hanyar falo.
  "Oho dai ka bani." A guje tayi ciki, ya bita. Ummi da Ramma abin sai ya basu dariya. Ta fahimci Aisha dai d'iyar Hajiya wacce Amina ta gayamata itace ake nufin ta haihu.
   Ranar suna tayi mamaki da Hajiya tayi mata iznin ta shirya har ita zasu tafi. Ai kuwa tayi murna ba kad'an ba don tunda tazo bata ketare layinnan ba bare har ta hau mota zuwa wani wajen, murnarta ta dad'u, burinta bai ta ga Antinta ba, don ba karamin ganin girman Amina takeyi ba.
    Ta sanya d'aya cikin atamfar da aka dinka mata, kasancewar ba dauri ta iya ba, kawai sai ta kulleshi a baya kamar yanda takeyiwa kayan islamiyyarsu. Ta sanya hijabin islamiyyarsu wanda ya kasance fari tas. Silifas dinta na roba wanda Amima ta barta ta zura ta fito. Ba jimawa suma iyalan gidan suka fito banda Ihsan wacce tun haihuwar da kwana hud'u ta tattara ta koma can.
  "A'a, kaga iyalan Mami." Cewar Adnan cikin tsokana yana duban Ummi. Ita dai murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta, Mami kanta shigar Ummi ya burgeta sai ya fito da kyan fuskarta. Tana rike da hannun Fahad suka shiga mota.
   Suna tafe a mota, idanunta na kan hanya tana ta kallon manyan titunan garin Kano masu cike da motoci iri daban-daban. Wani motar idan ta gani saidai ta bud'e baki tana kallo. Har suka iso gidan sunan bata ji ta gaji da kalle-kalle ba.
  Acan suka tarar da dukkan yayyun Ihsan duk da lokacin rana ce don ba'a soma cika sosai ba.
  Haka ta zauna jugum a gefe tana kallon yanda suke hira da dariya abinsu babu abinda ya damesu, sai daukar hoto sukeyi da bebi. Ba jimawa sai ga Hajiya Mama da su Amina, batasan Hajiya Mamar ba, amma ganin da tayiwa Amina tare da ita yasa ta fahimci itace. Ai kuwa ta washe baki ganin Antinta. Amina itama riko hannunta tayi fuskarta a sake.
  "Wai kanwata ce ta koma haka? Lallai Ummi Hajiya ta gyaramin ke." Ummi dai dariya tayi ta gaisheta. Amina ta amsa sannan tace bari ta shiga ta gaida mutanen ciki ta dawo gareta don lokacin Ummi ta gaji ta fito 'yar barandar kofar falon.
  Nan fa sukayita hira, Ummi ta sanarmata an sanyata makaranta, Amina na murmushi mai bayyana hak'ora ta dubeta.
  "Ban gayamaki cewa Hajiya bata zama da marar ilimi ba? Kedai ki dage sosai, zakiyi ilimi fiye da zatonki in har Allah Ya so. Kada ki gaji da bada himma."
   Ummi ranta fari k'al hakoranta a waje sun k'i rufuwa ta gyada kai.
  "Toh Anti."

Suna ta hira har Amina na sanar mata batun taron family da su Hajiya sukeyi duk bayan wata uku.
  "Gaba d'aya wanda ke nesa suna zuwa."
  Ummi ta jefomata tambaya.
"Yaushe zasuyi kuma Anti?"
Amina har lokacin da murmushi saman fuskarta ta amsa.
  "Asabar mai zuwa, nan zuwa jibi."
Ummi ta dan ta6e baki kadan.
"Toh ai ba inda zasu zo da mu ko?"
"Eh mana."
  Haka sukayita hirarsu, Amina na sanarmata cewa mamanta tace ta gaisheta. Har aka kammala aka watse batasan sunan yaro ba, sai a mota ta ji Hajiya Mama na waya tana fad'a, sunan yaron Tahir. Suma kishiyoyin Hajiya Madina sun leko saidai ko awa basu cika ba sukayi sallama suka tafi, babu wacce ta zo da yaro cikinsu sai wani shan k'amshi sukeyi.
                      ☆☆☆ 

A gajiye likis Ummi take, suna zuwa sallolin dake kanta kawai tayi ta kwanta. Bata kara sanin abinda ke faruwa ba a duniyar sai bayan farkawarta da Asuba. Bayan ta idar da sallah ta zauna anan addu'o'i har garin Allah Ya waye, kasancewar babu makarantar boko ballantana ta tashi had'e-had'en karin yaran yasa ta komawa tayi kwanciyarta, baccin da tayi har ya fiye mata na farko dadi, ta jima tana bacci kafin kuma ta soma jin ana bubbuga kafarta ana kiran sunanta. Farkawa tayi a firgice tana salati, ganin Fahad yasa ta sauke ajiyar zuciya. Kira ne daga Maminsa akan ta soya mishi kwai ta had'a da biredi da shayi. Dole ta mike ba don baccin ya isheta ba ta fad'a bandaki ta wanko bakinta da fuska sannan ta bi bayansa.
  Saida ta kammala komai sannan ta fad'a d'akinsu, ganin Ihsan bata farka ba yasa ta fitowa batare da tayi abinda ya kaita ba(wato gyaran daki). Tana gudun ta shiga bandakin don wankewa Ihsan ta yi mata rashin mutunci tace ta hanata bacci.
   Misalin karfe biyun rana, kowannensu yayi shirin Islamiyya, kai tsaye yaran wajen mahaifinsu suka nufa sanin da sukayi cewar yana garin suka kwashi gaisuwa ya sallamesu da abin kashewa bayan makaranta sannan suka d'uru cikin mota, suka tafi. Sai lokacin ne Ummi ta samu sararin yin nata shirin na makaranta tana ta zabga uban sauri adalilin lattin da ta so yi, haka ta fito cikin shiri ta yiwa Mami sallama. Mami ta amsa gami da yi mata fatan alheri, har ranta ta ji dadi don abu ne da sam Mamin bata saba ba, alamun Mami gaba daya a yau sun nuna tana cike da nishadi wanda babu damar tambayar dalilinsa. Ta sanya kai ta fice daga gidan.
  A makaranta nan dinma ta ji dadi sosai don kuwa ta kai haddarta saidai ta sha gyara duk da baikai yawan yanda a baya Malamin nasu ke cin gyaranta ba, ta lura yana yi mata uzuri ganin ko bak'i bata iya had'awa ba, wannan dalilin yasa ya ware mata lokacinta daban yake koyar da ita wasula da bak'ak'e.
   Koda suka tashi, cike da nishadi ta dawo haka kawai a yau batasan farincikin ko menene takeyi ba, ta godewa Allah yafi sau biyar a zuciyarta. A farfajiyar gidan ta iske motar Danliti, hakan ya bata tabbacin cewar Ihsan sun dawo. Hajiya Binta ta gani tare da wata wacce ba yau ta soma ganinta ba ga dukkan alamu kuma kawarta ce. Ta gaishesu a ladabce, suka amsa ciki-ciki suna karemata kallo. Bata kai ga karasawa ba ta ji suna maganarta, inda matar ke cewa.
"Ina mamakin Hajiya Madina, ko a ina ta kwaso wannan mai ruwan buzayen? Wannan ko Alhajinku ya gani mai yiwuwa yayi ta hud'u da ita."
  Ta karashe tana dariyar zolaya. Hajiya Binta ta ja tsaki.
"Ai kuwa da anyi girman kwabo, ballantana kuma sanin kanki ne Alhaji banda waccan shegiyar babu mai fad'amasa ya ji acikinmu, abin na kona raina."
  "Ai ku kukayi sake, ki bada hadin kai kika yanda komai zai chanja mana."

 
  Iyakar abinda Ummi ta tsinkaya kenan cikin zantukansu kafin kuma ta ta6e baki kawai, a kasan ranta kuwa tana tsoron ranar da Mami zata gaji ta korata daga gidan, watakil shikenan kuma dukkan gatan da ta soma samu na ilimi ya rushe. Saidai kuma tayi mamakin yanda Hajiya Binta take kula kawaye irin haka, da ace sun saba kwarai, da babu abinda zai hanata yin shishshigi wajen bata shawarar watsi da zantukan wannan mata. Da sallama ta nufi shiga falon, saidai kuma tayi turus ganin takalman maza har sawu hud'u da kuma na mata a bakin kofar, haka kawai ta ji gabanta ya fad'i, koda ta shiga bata ga kowa ba a wannan falon, ta numfasa ta karasa ciki, har ta chanja sutura tana cike da tunanin wadanda suka zo, sai kuma ta tunano da su Yaya Haidar, watakila su d'inne suka zo. Ta shirya cikin atamfa riga da zani da dankwali bayan tayi wanka sannan ta d'auro alwala ganin Magriba na dab da yi, fitowa tayi falo, tana son zuwa sanarwa Mami cewa ta dawo saidai kuma batason iske bak'in gaba d'aya nauyinsu take ji.
  A kicin ta had'u da Ramma, ta gaisheta. Ramma ta amsa tana fad'in.
  "Yanzu kuwa Hajiyar ke tambayarki, ta ji shiru nace kin dawo kina ciki. Kije tana nemanki."
  Gaba daya ta ji tsoro ya kamata har yanayin fuskarta ya nunawa Ramma.
  "To ai naga tana tare da bak'i yanzu."
Ramma ta kama baki. "Su waye bak'in? Ai 'yan gida ne, Hajiya Babba ce fa da yaranta."
  Ta gyada kai sannan ta juya ta nufi hanyar falon Mami gabanta na dukan tara-tara, ita da ba don ance Mami ke nemanta ba da babu inda zata. Har ta kai kofar shiga sai kuma ta juya da sauri don ji tayi ba zata iya ba. Muryoyin da ta jiyo daga bayanta na matasan yasa dole ta juyo. Gaba daya mazan ne suka fito da alamu dai masallaci suka nufa sakamakon kiraye-kirayen sallar da aka soma. Kallo d'aya tayi musu ta durkusa da sauri ta gaishesu. Suka amsa sannan ta basu wuri don su wuce. D'ago idon da zata yi sukayi ido hud'u da Faruk wanda dagaske kallonta yakeyi, ta gwammace ace bai kalleta din ba domin kuwa kallo ne ba na arziki ba face kallon raini, fuskarsa babu wata alamar fara'a; ta sadda kanta da sauri.
  "Ai kuwa Mami na ta cigiyarki da alama kin mata wani gagarumin laifi Ummi." Cewar Adnan ya karashe da dariyar zolaya.
  "Um." Shine abinda ta furta kawai da murmushi dauke saman fuskarta. Bayan sun wuceta ta bi bayansu da kallo. Wannan karon, Yaya Usman ne kadai ya sanya manyan kaya, gaba daya su ukun k'ananun kaya ne jikinsu. Hajiya Babba Allah Ya bata arziki na zaratan maza wadanda dukkansu basuyi kama da ragwaye ba a komai da ya shafi gwagwarmayar rayuwa da sauransu. Saidai da ace za'a bata za6in wanda yafi kyau da burgewa a fuska acikinsu, toh fa babu abinda zai hanata nuna Yaya Haidar bisa hujjarta na ganin duk ya fisu fara'a. Koda kuwa tasan da yawa cikin wasu matasan yanmata irinta, zasu iya bugun kirji su za6i Yaya Faruk, ita kam banda ita. Tsakani da Allah ta ji haushin kallon da ya bita da shi tamkar wanda ya ci karo da kashi, ta numfasa don tuni sun jima da kauracewa ganinta ta juya, gabanta ya fad'i ganin Ihsan tsaye ta harde hannuwa a kirji ta zubamata na mujiya fuskarta dauke da wani mugun murmushi. Ummi ta kauda kai ta bi ta gefenta zata wuce saidai maganganun da ya soma fitowa daga bakin Ihsan ya tsayar da ita cak!
   "Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki."
   Daga wannan ta sanya kai ta fita tana kwalawa Ramma kira. Iyakar radadi da bacin rai, Ummi ta ji shi a ranta, batasan sadda idanunta suka ciko da kwalla ba, wannan cin zarafi har ina? Kai tsaye an yankemata mummunan hukuncin da ko a mafarki bata yi zaton koda mak'iyinta zai shaideta da aikatawa ba, toh daman ina ita ina ire-iren wadannan mazan? Yaudarar kai ne, koda ta auna cewa Ihsan batasan irin zargin da ya kamata tayi mata  ba, yasa ta yin murmushi mai ciwo, da alama Ihsan bata gama sanin bambancin matsayinta da su ba, tabbas ta cucesu tunda har ta had'asu da ita, watakil da zasu ji da sai sun had'a da kai mata bugu don haushin abinda tayi musu. Ta share batun gami da goge fuskarta sannan ta juya ta koma don ta tabbatar a yanzun Mami ta shiga sallah. Dakinta ta koma itama ta tayar da nata sallar, saida ta idar ta kaiwa Allah kukanta akan Ya ji6anci lamuranta. Bata da kowa sai Shi, Shi ne gatanta. Yayi rahma ga Mahaifiyarta. Haka tayita kwararo addu'o'i har tana fidda ruwan hawaye kafin kuma ta shafa. Bata kai ga mikewa daga wurin ba ta ji Fahad na kwala mata kira adaidai sadda ya murd'a kofar dakin nata.
  "Ummi! Kizo inji Mami."
  Ta mike batare da ta cire hijabin ba ta bi bayansa.