19
Cikin tafiyar jan hankali ta karasa bakin kofar tsaye yake hannunsa rike da rigarsa ta ma aikatan jinya cikin nutsuwa ta sunkuya tare da furta,
"yaya Haidar sannu da zuwa".
Bai amsaba ta karɓi rigar tare da jakar hannunsa tsananin mamaki ya daskarar dashi ya yi ta maza ya kanne ya bi gefanta ya wuce ya bi siririn corridor ɗin da zai kaishi sashinsa. Ta cije leɓe tare da bin bayansa saida ya kusa minti biyar da shiga sannan ta bi bayansa yana tsaye yana amsa wayar Fadila ta ajiye kayan bakin gadonsa sannan ta juya zuwa banɗaki ta ƴhaɗa masa ruwan wanka cikin zuciyarta wautarta kawai take hangowa tare da ganin ta bada kanta amma ta daure ta cigaba ta fitowa ta samu ya cire uniform ta sadda kanta kansa,
"yaya na haɗa maka ruwan wanka".
Jim ya yi ƴyana kallonta kome ya tuna sai ya tsagayeta ya nufi banɗakin kafin ya fito ta shirya masa abincin ta fita zuwa sashinta saida ta daidaici ya gama cin abincin sannan ta dawo ta kwashe kayan ga mamakinta ya ci sossai. Ta kwashe ta mike zata fita ya tsaida ita,
"Ummi ina kayana na cikin firij?".
Dam gabanta ya faɗi kafaffunta suna neman gaggarta tsayuwa cikin rawar murya ta furta,
"wane kaya?".
"Ke! Ummi wasa nake miki zaki rainamin hankali? Ina kayana?".
Cikin dakiya ta juyo tana gatsina fuska,
"Dakata Haidar na zubar saboda banga fa idar ajiye kayan ɓarna a cikin gidana ba!".
Wani kyakkyawan mari ya zabga mata yana ficikota ta yi taga taga zata faɗi ta jingina da bango ajiye kayan hannunta ta yi dukkansu huci suke kamar zakaru ya nunata da yatsa.
"Ni zaki nunawa ɗanyar kai? Ina ruwanki da rayuwata? Rayuwarki ce bance miki bana son shishigi ba?".
Cikin tsiwa ta tareshi,
"rayuwarka tawace Haidar!".
Cak! Ya tsaya yana kare mata kallo wani abu yana zagaya kofofin jikinsa ta cigaba.
"Saboda kai ɗin JININA NE bazan juri ganinka cikin gurbataciyar rayuwa ba".
Wata shu umar dariya ya yi tare da kaiwa bakinta cafka da hannunsa ta yi tsale tana kara mara sauti suka soma zagaye ɗakin Allah ya bata sa a ta fice a guje ta yi sashinta tana numfarfashi. Tana shiga ɗakinta ta zube tana kuka mai cin rai nan da nan kanta ya hau ciwo.
Washegari bata daddara ba abinci ta sake shirya masa sannan ta wuce makaranta, duk da tana cikin damuwa amma tana kokarin ɓoye damuwarta har suka tashi daga nan ta wuce gida. Tsayin sati biyu aikin Ummi kenan kula da sashin Haidar da cimarsa sossai ya yi sabo da hakan a hankali suka soma sabawa ka idane kullum saita gaisheshi cikin girmamawa hakan yafi komai yi masa daɗi. Bangaran Ummi dauriya kawai take yi amma ko ganinsa bata muradin yi gashi ta lura kallon blue film da shan barasa ya zame masa jiki shi yasa kullum suke faɗa mudun zata je shara saita zubar dasu.
***
Bangaran su Mommy abu kam yaci tura sabida duk yadda suke wa lamarin duban sauki amma yasha kansu hakan yasa suka soma yunkurin ɗaukar mataki ta hanyar karkashin kasa.
***
Tun safe Ummi bata hutaba kasancewar Asabar ce suna hutun karshan mako Haidar na zaune kan kujera yana kallon labarai tana ɗakin girki taji an buɗe kofar falo jim kaɗan taji ya yi godiya ya koma saɗaf-saɗaf ta koma ta leka karaf idonta ya sauka kan kwalbar daya ɗaga zai kai bakinsa a sukwane ta fito daga kicin ɗin tana huci cikin shammata ta daki kwalbar hannunsa ta faɗi ji kake taratsatsa ta wargaje a tsakar ɗakin mamaki ya kamata ganin ya cire duk wata takarda dake nuna giya ce ya cukuikuyeta ya ajiye a gefe illa kawai murfin dake kan center carpet ɗinta. Cikin takaici ya kankance idanu yana dubanta sun kaɗa sunyi jajjur dasu zai yi magana kenan aka turo kofar tare da yin sallama. Gaba ɗaya suka juya a rikice jin muryar Baffa da sauri ta suri murfin da takardar ta tura karkashin kujera ta mike tana faɗaɗa fara arta.
Sanahsmatazu.wordPress.com
"Oyoyo Baffa sannu da zuwa".
Cikin dabara ta biyo dashi sashin da kwalbar bata watsuba ta ɗauko abin kwashe shara ta kwashe ta dawo hannunta ɗauke da ruwa da kuma damammiyar fura da bata rabo da ita ta rusuna,
"Baffana ga fura".
"Da kyau Ummyterna aaa sai murna take taga Baffanta".
Cikin murna ta washe hakoranta farare tas tsayayyu masu hushirya a tsakiya gasu dogaye tsaf. Haidar yana gefe sai kallonta yake sai yaga ta yi masa kyau kamar bata ita ba. Sun jima yana yi musu nasiha mai ratsa jiki karshe ya tsare Ummi da tambaya kan ko akwai wani abu da Haidar yake mata. Ta sunkuyar da kai kasa murya a raunane ta furta,
"babu Baffa lafiya muke zaune".
Boyyayar ajiyar zuciya ya saki daga shi har Haidar ɗin wadda su kaɗai duka san manufarta mikewa ya yi yana sa musu albarka ya wuce.
Tun bayan tafiyar Baffa Haidar ya shiga dogon tunanin sossai mamaki yake yadda Ummi ta sakaya aibunsa a idon mahaifinsa. Ya tabbatar yau data bayyanawa Baffa zaman da suke da tsine masa kaɗai zai yi yaji sanyi cikin ransa saboda kullum suka haɗu nasihar kenan ya rike masa Ummi amana ya kula da ita. Duk sai yaji ya muzanta wani tausayi da wani abu daya kasa tantance ko menene a kan Ummi ya dinga zagaya zuciya da jijjiyoyin jikinsa. Mikewa ya yi ya nufi ɗakinta karo na biyu tun auransu da ita ya tura kofar ya shiga yana shiga gabansa ya yi muguwar faɗuwa.
20
Ganin Ummi ya yi ta yi zaune tana kuka, idanunta sunyi jajjur da sanyin jiki ya karasa ya zauna gefan gado. Kwata-kwata ya rasa ta inda zai tunkareta ya daure ya yi ta maza,
"Ummi ki daina kuka kinji".
Mamakin kalamansa ya tsaida kukanta cak! Haidar data sani mutum mai iza da takama yau shi ne yake lallashinta bata kara mamaki ba saida kalamansa suka ratsa kunnuwanta.
"Ummi na gode da karamcin da kikai min ubangiji yasaka miki da alkhairi".
Ai saita karasa sakwarkwacewa can wata zuciyar ta tunasar da ita,
"ke Ummi Haidar nefa kawai dankin fitar dashi ne wajan Baffa yake lallaɓaki amma bari kiga a kwana biyu".
Kallonsa ta yi tana son yi masa futsara amma ya yi mata kwarjini saita sunkuyar dakai,
"babu komai yaya Haidar amma don Allah kadaina shan giya".
Ya yi jim duk saiya tsani kansa, wai saboda bakin hali karamar yarinya kamar Ummi yake shaka,
"inshaa Allahu Ummi zan daina ki tayani addu a".
"Zan maka yaya Haidar amma kaima ka guje mata bama ita kaɗai ba duk abinda kasan zai gusar maka da tunani gƴdun zubewar mutunci. ƊDomin yana daga cikin manyan manufofin musulunci kiyayewa ɗan-Adam Hankalin shi, domin hankali bakaramar kima yake da ita ba, wannan nasan koda ban kawo ayoyi da hadisai a kan haka ba kaida kanka zaka shaida, yaya musulunci ya ba wa hankalin dan-adam hakikanin kulawa ta yadda ya tsaftace shi daga barin dukkan abinda zai gurbata masa hankali, akan wannane musulunci ya haramta dukkan abinda yake gusar da hankali kamar :, Giya, Wiwi, Koken da dukkan wani abu da za'a sarrafa ta kowacce irin hanya muddin yana taba hankali to haramunne, Ma'aikin Allah yana cewa
"Dukkan abinda ke sa maye giya ne, kuma dukkanin giya haramun ce".
Bukhari da Muslim suka ruwaito, sannan koda baya sa maye sai an sha da yawa to ko kaɗan ne haramun ne kamar yadda Ma'aikin Allah yake cewa,
"Dukkan abinda meyawan shi ya ke sa maye to kadan dinshi ma haramun ne"
wannan fa shi ne hakikanin gatan da musulunci yayi mana, domin yadda giya da mukarrabanta muggan kwayoyi suke cutar da gangar jiki likitoci sun yi ittifaki akan haka da kuma yadda take sanadiyyar aukuwar cututtuka masu hatsarin gasket wasu suna kaiwa ga salwntar rayuwa, yan zu mutum ya sha wadan nan kwayoyi sun yi sana diyyar rasuwar shi haka zai zo ranar kiyama yana kamfatar waɗan nan kwayoyi kamar yadda bayanai suka gabata, ga yadda suke bata dabi'u, abin kunya kaga wani yasha ya taho yara su ns yi mishi 'ya yi marisa ya sha kafso' wani kuma ya kwararawa iyalin shi fitsari a kwance, wannan ya zama amalala, da kuma yadda take bata hankali ta kurɓata tunani, domin kowa yasan waɗan su muggan lefukan da ake tafkawa basa yiwuwa cikin cikakken hankali sai an bugu, lallai giya ta tabbata abar Allah ya yi wadaranta, wannan yasa malamai suka yi saɓani kan aukuwar sakin mai-maye idan ya saki matar shi yana cikin maye. Sabo da haka kamar yadda bayani ya gabata aka haramta dukkan wani abu da akai mai kowacce irin dabara ta yadda ya ke sa maye, ko meye kuwa, koda fura ce akai mata wata dabara ta zama tana sanya maye to ta zama haram, kamar yadda hadisin ma aiki ya yi nuni da nisantar kayan maye. Don Allah yaya Haidar ka daina sha".
Ta karashe maganar tana sharar hawaye, Haidar yayi shiru yana jimami cikin ransa sai ya mike cike da nauyin jiki ya bar mata ɗakin.
Ranar haka suka yini sukuku kowa da abin da yake ayyanawa cikin ransa. Da azahar Haidar ya fita ya bar gidan duk saita takura ganinta kamar abar zaije ya sha shi kuwa can keɓantancan waje ya samu ya killace kansa yana dogon tunani kan abin da ya faru tsakaninsa da Ummi. Bayan fitarsane ta samu bakuncin Hindatu sun jima suna hira daga bisani ta wuce gidanta. Sai bayan magarba ya shigo ta mike tana yi masa sannu da zuwa ya amsa yana ɗan murmushi kaɗan a kan fuskarsa ya wuce ɗaki ta yi tsaye jim daga bisani ta yi shahadar kuda ta bishi da abincinsa can yana zaune ta ajiye ta kalleshi,
"yaya in zuba ko sai kayi sallah?".
"Ummi nayi sallah cikin gari kinsan suna rigamu sallah kuma nanma akira ya aka yi baki ba koda yake naga alama hutu kike?".
Kunya ta kamata ta sunne kai kasa, mamaki take yadda ya gane hakan, zuba masa ta yi yaja flate ɗin gabansa yasa cokali tare da yin bisimilla ya ɗiba ya kai cokalin bakinta ɗauke kai ta yi tare da ɗaure fuska bai bi takanta ba kawai ya ci abincinsa ya yi kat. Saida ya gama cin abincin ya fuskanceta hakuri ya sake bata kan abin da ya faru ta mike ta wuce sashinta. Tun daga ranar zamansu ya sauya salo Haidar na kula da motsinta sossai da safe zai shigo yaga lafiyarta haka da dare ɓangaran Ummi kawai gani take saboda rufa masa asiri data yine amma da aka kwana biyu sai ta fuskanci ya sauya sossai wasu lokutan tana jiyo hirarsa da masu aikin gidan Haidar da ko sakar musu fuska baya yi amma shi ne hada hira. Hata ɗakinsa an samu sauyi ciki saboda tadaina karo da giya da kasussuwan batsa hakan yasa ta kara zage dantse wajan yimasa addu tare da kaiwa ubangiji kukanta kan Allah ya kara shiryar dashi.
***
Hankalin Fadila ba karamin tashi ya yi ba kwata kwata Haidar ya sauya mata waya in ba ita ta kirashi ba ya daina kiranta hakan yasa ta datawa Hajiyarta da Hajiya Sadiya hankali kan batun auranta da Haidar ga Nabila na kara zugata saboda akan idonta yake sauke Ummi a makaranta ya kuma dawo ɗaukarta. Hakan ya ɗaga musu hankali matuka Ummi kuwa babu abinda ya dameta karatunta take damuwarta ɗaya gashi harta shiga wata na shida amma ya hanata zuwa ko ina ko gidan Hindatu bata jeba duk da kusancin da suke dashi kwatsam ranar Asabar Hindatu ta kirata tana shaida mata ta yi ɓari hankalinta ya tashi sossai ta sameshi tana yi masa bayani hijabi kawai yace ta ɗauko suka nufi gidan nata. Lokacin da suka je har sun dawo asibiti daga nan fa hira ta ɓarke tsakanin Aminu dashi ashe ma asibiti ɗaya suke aiki rashin sani tun daga lokacin duk sati biyu ko uku sukan ziyarci juna.
*** Bangaran Khalifa shawarar Hindatu ya bi ya ɗaukarwa Bahijja yar aiki a hankali saiya samu saukin aiyukansa ga karatu da ya tasoshi gaba ga kuma hudimar kula da shige da fican kayan mahaifinsa daga nan Canada inda yake karatu zuwa Nigeria ga kuma cikin Bahijja daya shiga watan haihuwa. Hakan yasa bashi da lokacin kansa ko abinci a daddafe yake tsakurarsa. Kamar kodayaushe da wuri ya dawo aiki gidan shiru mai aikinsu ta gama ta tafi ya karasa falon saiya riski Bahijja tanata murkususu a rikice ya yi kanta yana faɗin,
"Bahijja lafiya?".
Cikin jigatuwar ciwo ta furta,
"Khalifa cikina zan mutu".
Ai bai jira cewarta ba ya suri Bahijja ya yi waje da ita, nan da nan suka karasa asibitin daya buɗe mata file kafin awa ɗaya Bahijja ta haifi sankaacceciyar ɗiyarta kyakkyawa kamar Khalifa nan da nan murna da farin ciki suka baibayeshi aka salamesu suka wuce gida sai murna yake yana bubbuga waya yana shaidawa dangi an samu ɗiya mace. Kai tsaye ya nufi katafaran kati ya jibgowa baby da mamanta siyayya. Bahijja ta dinga mamakin Khalifa da irin siyayya da kuma rawar kafar daya ke yi kan haihuwar Mommy baki har kunne take musu barka.
Kwana huɗu da haihuwar da yammaci yan Nigeria suka duro Canada cike da farin ciki. Tawagar tafiyar daga Hindatu sai kannan Bahijja guda biyu Ikilmaht da Wasila. Tayi murna da zuwansu sossai ana gobe suna duk suna zaune a falo Khalifa ya shigo yana fara a kan fuskarsa Hindatu ta dubeshi,
"nifa yaya banjin sunan babynmu ba".
Dariya ta kwace masa ya shafa sumarsa,
"ke Hinduwa ki rabani ga kalatacan mijinki can ya biyo ki har nan".
Dariya ta saki tana faɗin,
"ka cika zolaya dama ai akwai abin da zaizo yi".
Dariya suka yi ya saci kalon Bahijja da take kokarin yanka kankana babyn na cinyar Wasila ya ce cikin dakiyar zuciya,
"sunanta Aishatul Humaira amma Ummyter za a dinga kiranta".
Hindatu ta daka wani wawwan tsale ta mike,
"kai gaskiya yaya kayi rawar gani....".
Saita katse azarɓaɓin da take yi sakammakon karar da Bahijja ta saki duk suka bita da idanu cikin mamaki ashe kaɗuwar data yi yasa wukar hannunta ta yanketa cikin masifa ta shaki wuyansa tana wujjijjigashi tamkar wani karamin yaro........
21
"Khalifa nizaka wulakanta ka tozarta a idon duniya? Ka rasa sunan da zaka sama ɗiyarka saina tsohuwar budurwarka? Wallahi baka isa ba sai ka sake mata suna!".
Dauketa ya yi da giggitacan marin daya sa numfashinta tafiyar wucin gadi ta sheka barzahu ta dawo. Duk fallon suka zuba masa ido ganin yadda yake huci tamkar wanda ya yi gudun shekara ya nunata da yatsa,
"Bahijja ni zaki nunawa iko kan abin da yake JININA NE? Lallai yau na kara tabbatarwa baki da wayau".
"A'a fa yaya wannan tauye hakkine, da baka yi shawara da ita ba ka yanke hukunci haka ake rayuwar auren wannan ai cin zarafine?".
Cewar Wasila tana taunar cingum, mamaki ya cikashi kawai sai ya juya ya bar ɗakin da sauri Hindatu ta bi bayansa a ɗaki ta sameshi ya yi tagumi ta kira sunansa.
"Yaya ka yi hakuri nasani an ɓata maka amma kaima da kai meyasa baka tuntuɓeta ba? Ita ma ai tana da hakki ɗiyarta ce fa ya kake tunanin zata ji musamman data san matsayin wadda kasa sunan dominta?".
"Hindatu idan ba lallashina kika zo yi ba tarewa yar uwarki kika zo yi to fita kibani waje. Diya dai tawa ce kuma nike da hakkin raɗa mata suna don haka Aisha naga damar sa mata kuma wallahi babu sauyi".
Wayarsa ce ta yi kara ganin sunan Mama yasa shi risina ya amsa kiran cikin girmamawa amma bata amsa ba ta haushi da faɗa.
"Abubakar ina hankalinka yake? Dukan matarka ka yi anya kuwa kaine menene yake damunka?".
"Mama ki fahimce ni Bahijja duk ta wuce tunaninki, ni wallahi ma tunda saura shekara ɗaya in dawo to tare zan haɗosu da su Hindatu su dawo gida. Mama nagaji da Bahijja kwata-kwata bata dace da rayuwata ba".
Ya karashe kamar zai yi kuka, jikin Maman ya yi sanyi sossai ta numfasa,
"lafiya kuwa me take maka?".
"Mama basai mun yi tone-tone ba amma ki dinga yimin addu a don Allah ya bani mace daidai da tsarina".
Duk sai ta yi sanyi maimaikon faɗa ta koma lallashi Khalifa dai ya kafe kan bame sauyawa ɗiyarsa suna da haka suka yi sallama. Lokacin da Hindatu ta fito har lokacin kuka Bahijja take ta dubeta,
"Bahijja ki daina kuka don ƙAllah suna dai shi aka samata haka Allah ya hukunta saiki dangana".
"Dillacan munafuka rufamun baki, ai bakinku ɗaya kin san kuwa yadda nake jin KIYYAYAR Ummi a raina?".
"Ba KIYYAYA bece Bahijja SON ZUCIYA ne kawai irin naki an taɓa kishi da matar dake auran wani daban ba mijinki ba wannan ai shirimene?".
"Kimin shiru Hindatu kar kisamun ciwan kai, wallahi bazan shayar da wannan yarinyar nono ba mudun bai sake mata suna ba".
Fuu! Suka bar ɗakin suka barta rungume da yarinya tana tsanyara kuka haka suka yini yarinyar tana kuka kamar wadda ake mintsini bunu bunu Khalifa ya shigo yayin da Bahijja ta ɓame kofa ta kulle ita da kannanta.
***
Misalin karfe huɗu na yammacin ranar Lahdi Fadila ta shirya cikin shigar atamfa wadda tela yaci mutuncinta ɗinkin ya zauna das a jikinta ta ɗauki na suga. Kai tsaye office ɗin Haidar ta nufa tana tafe tana tunani ira iran waɗanan ranakun kafin ta nemi Haidar ya nemeta amma yau ita take nemansa yana guduwa ta share kwala daidai lokacin da ta yi parking a harabar kayatacan asibitinsu ta sauka ta kukkule motar ta kutsa kai cikin office ɗin.
Zaune ta sameshi shida Ahmad ta karasa rana murmushi babu yabo ba fallasa Haidar ya tareta sun ɗan yi jim na mintuna goma ya mike yana duban agogon hannunta ya nufi hanyar fita. Wani abu ya tokare makoshinta murya a shake ta furta,
"ina kuma zaka bayan kasan wajanka nazo?".
Bai juyo ba bai kuma tsaya ba ya furta,
"Ummi zan ɗauko a makaranta me zan miki?".
Ya faɗa tare da juyowa ya tsareta da ido duk saita muzanta ta sassauta murya.
"An ya Haidar ka kyautamun kuwa? In taso kafa ya kafa tun daga gida domin kai amma ka wofintar dani? Kwata-kwata ka sauyamun kota batun auranmu baka yi".
Jikinsa ya yi sanyi shi kansa yasan bai kyauta ma Fadila ba amma a yanayin daya ke dubanta bazai iya auranta ba saidai yana shakkar furta mata sabida koda yana yiwa Fadila duban lallataciya shi ne silla shiya fara buɗe mata ido da rayuwar clube kuma shi shaidane shiya fara saninta kansa ya ƴyi nauyi kawai saiya fice ya bar office ɗin. Fadila sunkuya wa ta yi ta fashe da kuka mai cin rai tausayinta ya tsinka zuciyar Ahmad ya dinga yi mata duban wauta,
"Baby ki hakura da Haidar kawai kizo miyi rayuwarmu zai fiye miki".
"Bazai yiwu ba boss bazan iya rayuwa babu Haidar ba tabbas nayi kuskuren sarayar da yancina gareshi amma wallahi bazai ci bulus ba duk da ba iya kansa na tsaya da rayuwata ba amma shi ne sillar komai dan haka yadda na ɗanɗani takaici sai shima ya ɗanɗana wallahi mu zuba".
Fuuu! Ta bar ɗakin Ahmad ya ɗaga kafaɗa ya wuce abinsa. Haidar kuwa kai tsaye makaranta ya wuce ɗaukar Ummi lokacin daya karaso tana tsaye tare da Sabah ɗiyar Hajiya Sarrinah sallama ta yi mata ta shiga motar suka cilla kan titi.
Kamar kurame haka suka dinga tafiya har suka karaso gidan yana yin parking ya yi saurin maida sucuirity ɗin motar ya rufe. Ummi ta yi tsamo-tsamo cikin motar ya dalla mata harara,
"waike baki iya yi wa mutum godiya ba aikinki kawai ki share ɗaki ki gyara gado kazama kawai ko gadonma baki iya hawa ba".
Cikin gungunin da baisan abin da take faɗa ba ta ce,
"ainafi wani wallahi".
Bata yi aune ba ya cafke bakin ya dinga murzashi da hannunsa a zaba ta isheta tasa hannu biyu ta na kici kicin kwacewa ta kasa shi kuwa laushin hannunta ya shagaltar dashi ya rasa a duniyar daya ke bai aune ba ta kwace rikon da ya yi ma bakinta ta zabga masa cizo ta buɗe motar ta yi waje da gudu zuwa cikin gida. Ya jima yana jinjina kokari irin nata wani fanin ma dariya take bashi kaɗa kai ya yi ya shige gida abinsa.
***
Washegari tun safe Khalifa ya tashi Hindatu saboda kwana suka yi basu yi bacci ba sai asuba saboda kukan da Ummyter take yi. Kai tsaye asibiti suka nufi sabida yadda yarinyar ta yi mugun galabaita. Zuwansu asibiti ba daɗewa aka sawa babyn drip saboda taji jiki daga nan suka wuce office ɗin likitan nan ya dinga masifa kan me aka barta da yunwa?. Cikin nutsuwa Khalifa ya yi masa bayanin Mamanta ce bata da lafiya, don haka suka kawota don abata madarar yara saboda gudun ciwo ya kamata. Likitan ƴya ƴyi mata duban tsaf sannan ya ce,
"yallaɓai ka yi hakuri bazamu baka madara haka nan ba saimun tabbatar da abinda ka faɗa dan haka inmun sallameku zuwa anjima sai kuzo da Maman babyn mu dubata".
"Yanzu likita babu taimakon da zakai mana?".
"Babu yallaɓai domin zuwanta zaisa mugane menene ainihin matsalar in za a bata maganine a bata in kuma babu damar hakan sai mu muduba wanne mataki zamu ɗauka abin da kuka sa fahimta shi ne.
Nonon uwa na da amfani ga jariri kwarai da gaske kuma yana dauke da ruwa da abinci da sinadarai da dama waɗanda jariri yake bukata a watanni shida na farkon rayuwarsa. Akwai bambanci a lafiyar jaririn da aka ba nonon uwa da wanda aka ba shi nonon saniya (ko na akuya). Koda an ga jaririn da aka ba madarar shanu ya yi kato, sinadaran da ya sha a madarar (milk) ba ɗaya suke da na nonon uwa ba.
Yawanci akan samu sinadaran da suke karanci a madarar shanu, a samu wasu kuma sun yi yawa. A na uwa kuwa komai na nan daidai da bukatar jariri. Ruwan madarar (milk) uwa da abin da ke ciki canzawa yake idan jariri na girma. Kalar madara a kwnanakin jariri na farko ba fara bace, za a gan ta ɗorawa-ɗorawa (yellow in color,) wanda ba madara kawai ba ne a ciki, sinadaran sa wa jariri kwayoyin garkuwar jiki don hana kamuwa da cututtukan (infections) jariri. Bayan wadannan kwanaki sai ruwan ya canza kala (olor), ya kara komawa fari, ya kara suga (sugar) da sinadarai masu gina jiki, haka har yaro ya kai wata shida (six months), kafin ya sake canza ɗanɗano, ya kara yawan suga har ila yau da sinadarai daidai bukatar jariri. Haka dai har a yaye jariri. Sai an tabbatar (make sure) uwa ba ta da isasshen ruwan madara ne ake hakura a kara da madarar shanu (cow milk).
Ko kuma idan uwar tagwaye (twins) ta haifa, wanda a wannan yanayi zai wuya nonon uwa zalla ya ishe su. Ba a hada ruwa da ruwan nono (don't compare breasth milk with water) tunda shi nonon yana ɗauke da iyakacin ruwan da jariri yake so. Manufar hana jariri ruwa a watannin farko (1st months of life) ba wai mugunta ba ce irin ta likitoci makar yadda wasu suke faɗa, a'a ana jiye wa jariri shan kwayoyin cuta ( to avoid infections) da ke cikin ruwan ne. Da yaro ya fara girma, kwayoyin garkuwar jikinsa sun yi karfi a wata biyar ko shida, to za a iya fara ba shi ruwa tsabtatacce (clean water), wato wanda aka tace aka tafasa. Ko ruwan roba ne ko na leda, an dai fi son a tafasa (boiled cooled water). Kayan ba da ruwan ma makar bulunboti, ana so duk bayan kwana biyu a tafasa. A waɗannan watanni ne kuma akan iya fara ba yaro dan abinci mai ruwa-ruwa, yawanci irin abincin gwangwani wadanda aka sa wa sinadarai na kara kuzari (a healthy supplement) da lafiya, wanda ba zai iya samu a nonon uwa ba.
An yi amanna yaron da aka yi wa irin wannan gatan da wuya ya samu matsalar gudawa (diarrhoea,pylorospasm and cough & catarrh)ko ta ciwon ciki ko mura da tari, wadanda cuttutuka ne da jarirai suka fi samu ta hanyar shan ruwa da kayan ba da ruwan irinsu cokali da kofuna (spoon & cup). Ko ya samu ciwon ma nan da nan zai fafi, domin kwayoyin cutar 'yan kadan zai samu ba kamar wanda aka ba ruwa madarar tsabta ba. Ban da karin lafiys, shan nonon uwa na da muhimmanci wajen kara soyayya (mothers love) uwa da jariri. An yi amanna cewa jariri na son uwarsa fiye da kowace mace a duniya saboda shayar da shi (breasthfeeds) da take yi. Ba a taba ganin jariri ya guji mahaifiyarsa, duk saboda albarkan da ke cikin shayarwa".
Jiki a sanyaye suka baro office ɗin Khalifa yaci layyar cin mutuncin Bahijja awarsu biyu suka bar asibitin zuwa gida.
Bahijja.....
Tun tafiyar Hindatu da Khalifa hankalinta ya tashi sossai, musamman yadda taga sun fita da yarinyar kamar mataciyya kannanta nata yi mata hira amma ta tafi kan tunanin wuyar data ci wajan haihuwar Ummyter karshe saita sa kuka duk suka saki baki suna dubanta ta dinga zazzaga musu masifa kamar taci babu ana haka taji tsayuwa motar su Khalifa ta kwasa ta yi wajen window tana lekensu babyn kwance a kafaɗar Hindatu tasa hannunta a baki tana tsotsa abu biyu ya tsirgamata lokaci guda tsoro da tausayi a haka suka ɓacewa ganinta suka shigo falon gidan ta sake kwasa tabi hanyar dazata sadasu da juna.
20
ReplyDelete